previous next

1 KOR 1

Gaisuwa

1  t Daga Bulus, manzo kirayayye na Almasihu Yesu da yardar Allah, da kuma ɗan'uwanmu Sastanisu,

2 t zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Koranti, wato, su waɗanda aka keɓe a cikin Almasihu Yesu, tsarkaka kirayayyu, tare da dukan waɗanda a ko'ina suke addu'a, da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijinsu da namu duka.

3  t Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Godiya saboda Bayebaye na Ruhu


4  t Kullum nakan gode wa Allah dominku, saboda alherin Allah da aka yi muku baiwa ta hanyar Almasihu Yesu, 5 t har ta kowace hanya aka wadata ku a cikinsa, a wajen yin magana duka da ilimi duka– 6 t domin kuwa an tabbatar da shaida a kan Almasihu a cikinku. 7 t Har ma ku ba kāsassu ba ne a wajen samun kowace baiwar Allah, kuna zuba ido ga bayyanar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 8 t wanda zai tabbatar da ku har ya zuwa ƙarshe, ku kasance marasa abin zargi a ranar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

9 t Allah mai alkawari ne, shi ne kuma ya kira ku ga tarayya da Ɗansa Yesu Almasihu Ubangijinmu.

Tsattsaguwa a Ikkilisiya


10 Na roƙe ku 'yan'uwa, saboda sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, cewa dukanku bakinku yă zama ɗaya, kada wata tsaguwa ta shiga a tsakaninku, sai dai ku haɗa kai, kuna da nufi ɗaya, ra'ayinku ɗaya. 11 Don kuwa, ya 'yan'uwana, mutanen gidan Kuluwi sun ba ni labari, cewa akwai jayayya a tsakaninku. 12 t Abin da nake nufi, shi ne kowannenku yana faɗar abu dabam, “Ni na Bulus ne,” wani kuwa, “Ni na Afolos ne,” wani kuwa, “Ni na Kefas ne,” ko kuwa, “ni na Almasihu ne.” 13 t Ashe, Almasihu a rarrabe yake? Ko Bulus ne aka gicciye dominku? Ko kuwa an yi muku baftisma ne da sunan Bulus? 14 t Na gode Allah da ban yi wa waninku baftisma ba, banda Kirisbus da Gayus, 15 kada wani ya ce da sunana ne aka yi muku baftisma.

16 t Ai, kuwa lalle na yi wa jama'ar gidan Istifanas ma. Amma banda waɗannan ban san ko na yi wa wani baftisma ba.

17  t Ai, ba don in yi baftisma Almasihu ya aiko ni ba, sai dai in sanar da bishara, ba kuwa da gwanintar iya magana ba, domin kada a wofinta ƙarfin gicciyen Almasihu.

Almasihu Ikon Allah Ne, da Hikimarsa


18  t Maganar gicciye, maganar wauta ce ga waɗanda suke hallaka, amma ƙarfin Allah ce a gare mu, mu da ake ceto.

19 t Domin a rubuce yake cewa,
“Zan rushe hikimar mai hikima,
Zan kuma shafe haziƙancin haziƙi.”
20  t To, ina masu hikima suke? Ina kuma masana? Ina masu muhawwarar zamanin nan? Ashe, Allah bai fallashi hikimar duniyar nan a kan wauta ce ba? 21 Da yake bisa ga hikimar Allah, duniya ba ta san Allah ta wurin hikimarta ba, sai Allah ya ji daɗin ceton masu ba da gaskiya, ta wurin wautar shelar bishara. 22 t Yahudawa kam, mu'ujiza suke nema su gani, Helenawa kuwa hikima suka nema su samu, 23 t mu kuwa muna wa'azin Almasihu gicciyeyye, abin sa yin tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga al'ummai, 24 t amma ga waɗanda suke kirayayyu, ko Yahudawa ko al'ummai duka biyu, Almasihu ikon Allah ne, da hikimar Allah.

25 t Domin abin da aka zata wauta ce ta Allah, ya fi hikimar ɗan adam, abin da kuma aka zata rauni ne na Allah, ya fi duk ƙarfin ɗan adam.
26 Ku dubi kiranku da aka yi, ya ku 'yan'uwa, a cikinku, ai, ba a kira masu hikima irin ta duniya da yawa ba, masu iko kuma ba su da yawa, haka ma masu asali ma ba yawa. 27 t Amma Allah ya zaɓi abin da yake wauta a duniya, domin ya kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abin da yake rarrauna a duniya, domin ya kunyata ƙaƙƙarfa. 28 t Allah ya zaɓi abin da yake ƙasƙantacce, wulakantacce a duniya, har ma abubuwan da ba su, domin yă shafe abubuwan da suke akwai. 29 t Wannan kuwa duk don kada wani ɗan adam yă yi fariya a gaban Allah ne. 30 t Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa. 31 t Saboda haka, “Duk mai yin alfarma, yă yi da Ubangiji” (abin da yake a rubuce ke nan).

1 Corinthians 1

1 Paul, called to be an apostle of Jesus Christ through the will of God, and Sosthenes our brother,2 unto the church of God which is at Corinth, even them that are sanctified in Christ Jesus, called to be saints, with all that call upon the name of our Lord Jesus Christ in every place, their Lord and ours:3 Grace to you and peace from God our Father and the Lord Jesus Christ.4 I thank my God always concerning you, for the grace of God which was given you in Christ Jesus;5 that in everything ye were enriched in him, in all utterance and all knowledge;6 even as the testimony of Christ was confirmed in you:7 so that ye come behind in no gift; waiting for the revelation of our Lord Jesus Christ;8 who shall also confirm you unto the end, that ye be unreproveable in the day of our Lord Jesus Christ.9 God is faithful, through whom ye were called into the fellowship of his Son Jesus Christ our Lord.10 Now I beseech you, brethren, through the name of our Lord Jesus Christ, that ye all speak the same thing and that there be no divisions among you; but that ye be perfected together in the same mind and in the same judgment.11 For it hath been signified unto me concerning you, my brethren, by them that are of the household of Chloe, that there are contentions among you.12 Now this I mean, that each one of you saith, I am of Paul; and I of Apollos: and I of Cephas; and I of Christ.13 Is Christ divided? was Paul crucified for you? or were ye baptized into the name of Paul?14 I thank God that I baptized none of you, save Crispus and Gaius;15 lest any man should say that ye were baptized into my name.16 And I baptized also the household of Stephanas: besides, I know not whether I baptized any other.17 For Christ sent me not to baptize, but to preach the gospel: not in wisdom of words, lest the cross of Christ should be made void.18 For the word of the cross is to them that perish foolishness; but unto us who are saved it is the power of God.19 For it is written, I will destroy the wisdom of the wise, And the discernment of the discerning will I bring to nought.

20 Where is the wise? where is the scribe? where is the disputer of this world? hath not God made foolish the wisdom of the world?21 For seeing that in the wisdom of God the world through its wisdom knew not God, it was God’s good pleasure through the foolishness of the preaching to save them that believe.22 Seeing that Jews ask for signs, and Greeks seek after wisdom:23 but we preach Christ crucified, unto Jews a stumblingblock, and unto Gentiles foolishness;24 but unto them that are called, both Jews and Greeks, Christ the power of God, and the wisdom of God.25 Because the foolishness of God is wiser than men; and the weakness of God is stronger than men.26 For behold your calling, brethren, that not many wise after the flesh, not many mighty, not many noble, are called:27 but God chose the foolish things of the world, that he might put to shame them that are wise; and God chose the weak things of the world, that he might put to shame the things that are strong;28 and the base things of the world, and the things that are despised, did God choose, yea and the things that are not, that he might bring to nought the things that are:29 that no flesh should glory before God.30 But of him are ye in Christ Jesus, who was made unto us wisdom from God, and righteousness and sanctification, and redemption:31 that, according as it is written, He that glorieth, let him glory in the Lord.