1 KOR 10
Kashedi a kan Bautar Gumaka
1 t To, ina so ku sani, 'yan'uwa, dukan kakanninmu an kāre su ne a ƙarƙashin gajimare, dukansu kuma sun ratsa ta cikin bahar. 2 Dukansu kuwa an yi musu baftisma ga bin Musa a cikin gajimaren, da kuma bahar ɗin. 3 Duka kuwa sun ci abincin nan na ruhu, 4 t duk kuma sun sha ruwan nan na ruhu. Domin sun sha ruwa daga Dutsen nan na ruhu, wanda ya yi tafiya tare da su. Dutsen nan kuwa Almasihu ne.
5 t Duk da haka Allah bai yi murna da yawancinsu ba, har aka karkashe su a jeji.
6 To, ai, waɗannan abubuwa gargaɗi ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi. 7 t Kada fa ku zama matsafa kamar yadda waɗansunsu suke. A rubuce yake cewa, “Jama'a sun zauna garin ci da sha, suka kuma tashi suka yi ta rawa.” 8 t Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har mutum dubu ashirin da uku suka zuba a rana ɗaya tak. 9 t Kada kuma mu gwada Ubangiji yadda waɗansu suka yi, har macizai suka hallaka su. 10 t Kada kuma mu yi gunaguni yadda waɗansu suka yi, har mai hallakarwa ya hallaka su. 11 t To, duk wannan ya same su ne a kan misali, an kuma rubuta shi ne don a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana. 12 t Don haka duk wanda yake tsammani ya kahu, ya mai da hankali kada ya fāɗi.
13 t Ba wani gwajin da ya taɓa samunku, wanda ba a saba yi wa ɗan adam ba. Allah mai alkawari ne, ba zai kuwa yarda a gwada ku fin ƙarfinku ba, amma a game da gwajin sai ya ba da mafita, yadda za ku iya jure shi.
14 Saboda haka, ya ƙaunatattuna, ku guji bautar gumaka. 15 Ina magana da ku a kan ku mahankalta ne fa, ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa. 16 t Ƙoƙon nan na yin godiya, wanda muke gode wa Allah saboda shi, ashe, ba tarayya ne ga jinin Almasihu ba? Gurasar nan da muke gutsuttsurawa kuma, ashe, ba tarayya ce ga jikin Almasihu ba? 17 t Da yake gurasar nan ɗaya ce, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama mu duk gurasa ɗaya muke ci. 18 t Ku dubi ɗabi'ar Isra'ila. Ashe, waɗanda suke ci daga hadayu, ba tarayya suke yi da bagadin hadaya ba? 19 t Me nake nufi ke nan? Abin da aka yanka wa gumakan ne ainihin wani abu, ko kuwa gunkin ne ainihin wani abu? 20 t A'a! Na nuna ne kawai cewa abin da al'ummai suke yankawa, ga aljannu suke yanka wa, ba Allah ba. Ba na fa so ku zama abokan tarayya da aljannu. 21 t Ba dama ku sha a ƙoƙon Ubangiji, ku kuma sha a na aljannu. Ba dama ku ci abinci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a na aljannu.
22 t Ashe, har mā tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?Yi Kome saboda Ɗaukakar Allah
23 t “Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne masu amfani ba. “Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne suke ingantawa ba. 24 t Kada kowa ya nemi ya kyautata wa kansa, sai dai ya kyautata wa ɗan'uwansa. 25 t Ku ci kowane irin abu da ake sayarwa a mahauta, ba tare da tambaya ba saboda lamiri. 26 t Don an rubuta, “Duniya ta Ubangiji ce, da duk abin da yake cikinta.” 27 t In wani a cikin marasa ba da gaskiya ya kira ku cin abinci, kuka kuwa yarda ku tafi, sai ku ci duk irin da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya ba saboda lamiri. 28 t In kuwa wani ya ce muku, “An yanka wannan saboda gunki ne fa,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan mai gaya muku, da kuma saboda lamiri, 29 t nasa lamiri fa na ce, ba naka ba. Don me fa lamirin wani zai soki 'yancina?
30 t In na yi godiya ga Allah a kan abincina, saboda me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?
31 t To, duk abin da kuke yi, ko ci, ko sha, ku yi kome saboda ɗaukakar Allah. 32 t Kada ku zama abin tuntuɓe ga Yahudawa ko al'ummai ko ikkilisiyar Allah, 33 t kamar dai yadda nake ƙoƙarin kyautata wa dukan mutane a cikin duk abin da nake yi, ba nema wa kaina amfani nake yi ba, sai dai in amfani mutane da yawa, don su sami ceto.
1 Corinthians 10
1 For I would not, brethren, have you ignorant, that our fathers were all under the cloud, and all passed through the sea;2 and were all baptized unto Moses in the cloud and in the sea;3 and did all eat the same spiritual food;4 and did all drink the same spiritual drink: for they drank of a spiritual rock that followed them: and the rock was Christ.5 Howbeit with most of them God was not well pleased: for they were overthrown in the wilderness.6 Now these things were our examples, to the intent we should not lust after evil things, as they also lusted.7 Neither be ye idolaters, as were some of them; as it is written, The people sat down to eat and drink, and rose up to play.8 Neither let us commit fornication, as some of them committed, and fell in one day three and twenty thousand.9 Neither let us make trial of the Lord, as some of them made trial, and perished by the serpents.10 Neither murmur ye, as some of them murmured, and perished by the destroyer.11 Now these things happened unto them by way of example; and they were written for our admonition, upon whom the ends of the ages are come.12 Wherefore let him that thinketh he standeth take heed lest he fall.13 There hath no temptation taken you but such as man can bear: but God is faithful, who will not suffer you to be tempted above that ye are able; but will with the temptation make also the way of escape, that ye may be able to endure it.14 Wherefore, my beloved, flee from idolatry.15 I speak as to wise men; judge ye what I say.16 The cup of blessing which we bless, is it not a communion of the blood of Christ? The bread which we break, is it not a communion of the body of Christ?17 seeing that we, who are many, are one bread, one body: for we are all partake of the one bread.18 Behold Israel after the flesh: have not they that eat the sacrifices communion with the altar?19 What say I then? that a thing sacrificed to idols is anything, or that an idol is anything?20 But I say, that the things which the Gentiles sacrifice, they sacrifice to demons, and not to God: and I would not that ye should have communion with demons.21 Ye cannot drink the cup of the Lord, and the cup of demons: ye cannot partake of the table of the Lord, and of the table of demons.22 Or do we provoke the Lord to jealousy? are we stronger than he?23 All things are lawful; but not all things are expedient. All things are lawful; but not all things edify.24 Let no man seek his own, but each his neighbor’s good.25 Whatsoever is sold in the shambles, eat, asking no question for conscience’ sake,26 for the earth is the Lord’s, and the fulness thereof.27 If one of them that believe not biddeth you to a feast, and ye are disposed to go; whatsoever is set before you, eat, asking no question for conscience’ sake.28 But if any man say unto you, This hath been offered in sacrifice, eat not, for his sake that showed it, and for conscience sake:29 conscience, I say, not thine own, but the other’s; for why is my liberty judged by another conscience?30 If I partake with thankfulness, why am I evil spoken of for that for which I give thanks?31 Whether therefore ye eat, or drink, or whatsoever ye do, do all to the glory of God.32 Give no occasions of stumbling, either to Jews, or to Greeks, or to the church of God:33 even as I also please all men in all things, not seeking mine own profit, but the profit of the many, that they may be saved.