1 KOR 12
Bayebaye na Ruhu
1 t A yanzu kuma 'yan'uwa, a game da baye-baye na ruhu, ba na so ku rasa sani. 2 t Kun sani fa a sa'ad da kuke bin al'ummai, an juyar da ku ga bin gumakan nan marasa baki yadda aka ga dama.
3 t Don haka nake sanar da ku, cewa ba mai magana ta wurin ikon Ruhun Allah sa'an nan ya ce, “Yesu la'ananne ne!” Haka kuma ba mai iya cewa, “Yesu Ubangiji ne,” sai ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
4 t To, akwai baiwa iri iri, amma Ruhu ɗaya ne. 5 Akwai fanni iri iri na ibada, amma Ubangiji ɗaya ne. 6 t Akwai kuma aiki iri iri, amma Allah ɗaya yake iza kowa ga yin kowannensu. 7 t An yi wa kowanne baiwa da wani buɗi na Ruhu, don kyautata wa duka. 8 t Wani an yi masa baiwa da koyar da hikima ta wurin Ruhu, wani kuma da koyar da sani ta wurin wannan Ruhu. 9 t Wani kuwa an yi masa baiwa da bangaskiya ta wurin Ruhun nan, wani kuma baiwar warkarwa ta wurin Ruhun nan, 10 t wani kuma yin mu'ujizai, wani kuma annabci, wani kuma baiwar rarrabe ruhu da aljani, wani kuma iya harshe iri iri, wani kuma fassara harsuna.
11 t Dukan waɗannan Ruhu ɗaya ne da yake iza su, yake kuma rarraba wa ko wannensu yadda ya nufa.Dukkanmu Gaɓoɓin Jiki Guda Ne
12 t Wato, kamar yadda jiki yake guda, yake kuma da gaɓoɓi da yawa su gaɓoɓin kuwa ko da yake suna da yawa, jiki guda ne, to, haka ga Almasihu.
13 t Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda, mu zama jiki guda, Yahudawa ko al'ummai, bayi ko 'ya'ya, dukanmu kuwa an shayar da mu Ruhu guda.
14 Jiki ba gaba ɗaya ba ne, gaɓoɓi ne da yawa. 15 Da ƙafa za ta ce, “Da yake ni ba hannu ba ce, ai, ni ba gaɓar jiki ba ce,” faɗar haka ba za ta raba ta da zama gaɓar jikin ba. 16 Da kuma kunne zai ce, “Da yake ni ba ido ba ne, ai, ni ba gaɓar jiki ba ne,” faɗar haka ba za ta raba shi da zama gaɓar jikin ba. 17 Da dukan jiki ido ne, da me za a ji? Da dukan jiki kunne ne, da me za a sansana? 18 t Amma ga shi, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowaccensu yadda ya nufa. 19 Da dukan jikin gaɓa ɗaya ne, da ina sauran jikin? 20 t Amma ga shi, akwai gaɓoɓi da yawa, jiki kuwa ɗaya. 21 Ba dama ido yă ce wa hannu, “Ba ruwana da kai,” ko kuwa kai yă ce wa ƙafafu, “Ba ruwana da ku.” 22 Ba haka yake ba, sai ma gaɓoɓin da ake gani kamar raunana, su ne wajibi, 23 gaɓoɓin jiki kuma da ake gani kamar sun kasa sauran daraja, mukan fi ba su martaba. Ta haka gaɓoɓinmu marasa kyan gani, akan ƙara kyautata ganinsu. 24 Gaɓoɓinmu masu kyan gani kuwa ba sai an yi musu kome ba. Amma Allah ya harhaɗa jiki, yana ba da mafificiyar martaba ga ƙasƙantacciyar gaɓa, 25 kada rashin haɗa kai ya kasance ga jiki, sai dai gaɓoɓin su kula da juna, kula iri ɗaya.
26 Ta haka, in wata gaɓa ta ji ciwo, duk sai su ji ciwo tare, in kuwa an yabi wata, duk sai su yi farin ciki tare.
27 t To, ku jikin Almasihu ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne. 28 t A cikin ikkilisiya, Allah ya sa waɗansu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa'an nan sai masu yin mu'ujizai, sai masu baiwar warkarwa, da mataimaka, da masu tafiyar da Ikkilisiya, da kuma masu magana da harsuna iri iri. 29 Shin, duka manzanni ne? Ko duka annabawa ne? Ko duk masu koyarwa ne? Su duka masu yin mu'ujizai ne? 30 t Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne suke magana da waɗansu harsuna? Ko kuwa duka ne suke fassara?
31 t Sai dai ku himmantu ga neman mafafitan bayebaye.
Har ma zan nuna muku wata hanya mafificiya nesa.
1 Corinthians 12
1 Now concerning spiritual gifts, brethren, I would not have you ignorant.2 Ye know that when ye were Gentiles ye were led away unto those dumb idols, howsoever ye might led.3 Wherefore I make known unto you, that no man speaking in the Spirit of God saith, Jesus is anathema; and no man can say, Jesus is Lord, but in the Holy Spirit.4 Now there are diversities of gifts, but the same Spirit.5 And there are diversities of ministrations, and the same Lord.6 And there are diversities of workings, but the same God, who worketh all things in all.7 But to each one is given the manifestation of the Spirit to profit withal.8 For to one is given through the Spirit the word of wisdom; and to another the word of knowledge, according to the same Spirit:9 to another faith, in the same Spirit; and to another gifts of healings, in the one Spirit;10 and to another workings of miracles; and to another prophecy; and to another discernings of spirits; to another divers kinds of tongues; and to another the interpretation of tongues:11 but all these worketh the one and the same Spirit, dividing to each one severally even as he will.12 For as the body is one, and hath many members, and all the members of the body, being many, are one body; so also is Christ.13 For in one Spirit were we all baptized into one body, whether Jews or Greeks, whether bond or free; and were all made to drink of one Spirit.14 For the body is not one member, but many.15 If the foot shall say, Because I am not the hand, I am not of the body; it is not therefore not of the body.16 And if the ear shall say, Because I am not the eye, I am not of the body; it is not therefore not of the body.17 If the whole body were an eye, where were the hearing? If the whole were hearing, where were the smelling?18 But now hath God set the members each one of them in the body, even as it pleased him.19 And if they were all one member, where were the body?20 But now they are many members, but one body.21 And the eye cannot say to the hand, I have no need of thee: or again the head to the feet, I have no need of you.22 Nay, much rather, those members of the body which seem to be more feeble are necessary:23 and those parts of the body, which we think to be less honorable, upon these we bestow more abundant honor; and our uncomely parts have more abundant comeliness;24 whereas our comely parts have no need: but God tempered the body together, giving more abundant honor to that part which lacked;25 that there should be no schism in the body; but that the members should have the same care one for another.26 And whether one member suffereth, all the members suffer with it; or one member is honored, all the members rejoice with it.27 Now ye are the body of Christ, and severally members thereof.28 And God hath set some in the church, first apostles, secondly prophets, thirdly teachers, then miracles, then gifts of healings, helps, governments, divers kinds of tongues.29 Are all apostles? are all prophets? are all teachers? are all workers of miracles?30 have all gifts of healings? do all speak with tongues? do all interpret?31 But desire earnestly the greater gifts. And moreover a most excellent way show I unto you.