previous next

1 KOR 14

Harsuna da Annabci

1  t Ku nace wa ƙauna, ku kuma himmantu ga neman bayebaye na ruhu, tun ba ma na yin annabci ba. 2 t Duk wanda yake magana da wani harshe, ba da mutane yake magana ba, da Allah yake yi, ba kuwa wanda yake fahimtarsa, domin asirtattun al'amura yake ambato ta wurin Ruhu. 3 t Wanda kuwa yake yin annabci, mutane yake yi wa magana domin yă inganta su, ya ƙarfafa su, yă ta'azantar da su. 4 t Duk wanda yake magana da wani harshe, kansa yake ingantawa. Mai yin annabci kuwa, ikkilisiya yake ingantawa.

5 t To, ina so dukanku ku yi magana da waɗansu harsuna dabam, amma na fi so ku yi annabci. Wanda yake yin annabci, ya fi mai magana da waɗansu harsuna, sai ko in wani ya yi masa fassara, domin a inganta ikkilisiya.
6  t To, 'yan'uwa, in na zo muku ina magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayani, ko ilimi, ko annabci, ko koyar da Maganar Allah ba? 7 In abubuwan nan marasa rai, kamar su sarewa da molo, muryarsu ba ta fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa? 8 t In ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi? 9 Haka ma yake a gare ku. In kun yi magana da wani harshe, wanda ba a fahimta ba, yaya wani zai san abin da ake faɗa? Kun yi magana a banza ke nan! 10 Hakika akwai harsuna iri iri a duniya, ba kuwa wanda ba shi da ma'ana. 11 In kuwa ba na jin harshen, sai in zama bare ga mai maganar, mai maganar kuma ya zama bare a gare ni.

12 Haka ma yake a gare ku. Tun da yake kun ɗokanta da samun bayebaye na Ruhu, sai ku himmantu ku ba da ƙarfinku ga inganta ikkilisiya.
13 Saboda haka duk mai magana da wani harshe, sai yă yi addu'a a yi masa baiwar fassara. 14 In na yi addu'a da wani harshe, ruhuna ne yake addu'a, amma tunanina bai amfana kowa ba. 15 t To, ƙaƙa ke nan? Zan yi addu'a da ruhuna, zan kuma yi a game da tunanina. Zan yi waƙar yabon Allah da ruhuna, zan yi a game da tunanina. 16 t In ba haka ba, in ka gode wa Allah da ruhu kawai, ta yaya wanda yake jahili zai ce, “Amin,” a kan godiyar da kake yi, in bai san abin da kake faɗa ba? 17 Ko da yake ka gode wa Allah sosai, ai, ɗan'uwanka bai ƙaru da kome ba. 18 Na gode Allah ina magana da waɗansu harsuna fiye da ku duka.

19 Duk da haka dai a taron ikkilisiya na gwammace in faɗi kalmomi biyar a game da tunanina, domin in karantar da waɗansu, da in faɗi kalmomi dubu goma da wani harshe.
20  t Ya ku 'yan'uwa, kada ku yi hankali irin na yara, sai dai a wajen mugunta, ku yi halin jarirai, amma a wajen hankali ku yi dattako. 21 t A rubuce yake a cikin littattafai masu tsarki cewa, “Zan yi magana da jama'an nan ta wurin mutane masu baƙin harsuna, da kuma ta harshen baƙi, duk da haka kuwa ba za su saurare ni ba, in ji Ubangiji.” 22 t Wato, ashe, harsuna a kan alamu suke, ba ga masu ba da gaskiya ba, sai dai ga marasa ba da gaskiya. Annabci kuwa domin masu ba da gaskiya ne, ba don marasa ba da gaskiya ba. 23 t Saboda haka, in dukan ikkilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da wani harshe dabam, waɗansu jahilai kuma ko marasa ba da gaskiya suka shigo, ashe, ba sai su ce kun ruɗe ba? 24 In kuwa kowa yana yin annabci, wani kuma marar ba da gaskiya ko jahili ya shigo, sai maganar kowa ta ratsa shi, ya kamu a ransa ta maganar kowa,

25 t asiran zuciyarsa kuma su tonu. Ta haka sai ya fāɗi ya yi wa Allah sujada, yana cewa lalle Allah na cikinku.

A Yi Kome yadda Ya Dace, a Shirye


26  t To, ƙaƙa abin yake ne, 'yan'uwa? Duk sa'ad da kuka taru, wani yakan yi waƙar yabon Allah, wani kuma koyar da Maganar Allah, wani bayani, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Sai dai a yi kome don ingantawa. 27 In kuwa waɗansu za su yi magana da wani harshe, kada su fi mutum biyu, matuƙa uku, su ma kuwa bi da bi, wani kuma yă yi fassara. 28 In kuwa ba mai fassara, sai kowannensu yă yi shiru a cikin taron Ikkilisiya, yă yi wa Allah magana a zuci. 29 t Masu yin annabci kuma, sai dai biyu ko uku su yi magana, saura kuwa su auna maganar. 30 In kuwa an yi wa wani wanda yake zaune wani bayani, sai na farkon nan mai magana yă yi shiru. 31 Dukanku kuna iya yin annabci da ɗaya ɗaya, har kowa yă koya, yă koma sami ƙarfafawa. 32 t Annabawa suna sarrafa ruhohinsu na annabci,

33 t domin Allah ba Allahn ruɗu ba ne, na salama ne.
Haka yake kuwa a duk ikilisyoyin tsarkaka.
34 t Sai mata su yi shiru a cikin taron ikkilisiya, don ba a ba su izinin yin magana ba, sai dai su bi, kamar dai yadda Attaura ma ta ce. 35 In akwai wani abin da suke so su sani, to, sai su tambayi mazansu a gida, don abin kunya ne mace ta yi magana a cikin taron ikkilisiya.

36 A kanku ne maganar Allah ta fara, ko kuwa a gare ku kaɗai ta isa?
37  t In wani yana zato shi annabi ne, ko kuwa mai wata baiwa ta ruhu, to, sai yă fahimta, abin nan da nake rubuto muku umarni ne na Ubangiji. 38 In kuwa wani ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi. 39 t Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku himmantu ga samun baiwar yin annabci, kada kuma ku hana yin magana da waɗansu harsuna. 40 t Sai dai a yi kome ta hanyar da ta dace, a shirye kuma.

1 Corinthians 14

1 Follow after love; yet desire earnestly spiritual gifts, but rather that ye may prophesy.2 For he that speaketh in a tongue speaketh not unto men, but unto God; for no man understandeth; but in the spirit he speaketh mysteries.3 But he that prophesieth speaketh unto men edification, and exhortation, and consolation.4 He that speaketh in a tongue edifieth himself; but he that prophesieth edifieth the church.5 Now I would have you all speak with tongues, but rather that ye should prophesy: and greater is he that prophesieth than he that speaketh with tongues, except he interpret, that the church may receive edifying.6 But now, brethren, if I come unto you speaking with tongues, what shall I profit you, unless I speak to you either by way of revelation, or of knowledge, or of prophesying, or of teaching?7 Even things without life, giving a voice, whether pipe or harp, if they give not a distinction in the sounds, how shall it be known what is piped or harped?8 For if the trumpet give an uncertain voice, who shall prepare himself for war?9 So also ye, unless ye utter by the tongue speech easy to be understood, how shall it be known what is spoken? for ye will be speaking into the air.10 There are, it may be, so many kinds of voices in the world, and no kind is without signification.11 If then I know not the meaning of the voice, I shall be to him that speaketh a barbarian, and he that speaketh will be a barbarian unto me.12 So also ye, since ye are zealous of spiritual gifts, seek that ye may abound unto the edifying of the church.13 Wherefore let him that speaketh in a tongue pray that he may interpret.14 For if I pray in a tongue, my spirit prayeth, but my understanding is unfruitful.15 What is it then? I will pray with the spirit, and I will pray with the understanding also: I will sing with the spirit, and I will sing with the understanding also.16 Else if thou bless with the spirit, how shall he that filleth the place of the unlearned say the Amen at thy giving of thanks, seeing he knoweth not what thou sayest?17 For thou verily givest thanks well, but the other is not edified.18 I thank God, I speak with tongues more than you all:19 howbeit in the church I had rather speak five words with my understanding, that I might instruct others also, than ten thousand words in a tongue.20 Brethren, be not children in mind: yet in malice be ye babes, but in mind be men.21 In the law it is written, By men of strange tongues and by the lips of strangers will I speak unto this people; and not even thus will they hear me, saith the Lord.22 Wherefore tongues are for a sign, not to them that believe, but to the unbelieving: but prophesying is for a sign, not to the unbelieving, but to them that believe.23 If therefore the whole church be assembled together and all speak with tongues, and there come in men unlearned or unbelieving, will they not say that ye are mad?24 But if all prophesy, and there come in one unbelieving or unlearned, he is reproved by all, he is judged by all;25 the secrets of his heart are made manifest; and so he will fall down on his face and worship God, declaring that God is among you indeed.26 What is it then, brethren? When ye come together, each one hath a psalm, hath a teaching, hath a revelation, hath a tongue, hath an interpretation. Let all things be done unto edifying.27 If any man speaketh in a tongue, let it be by two, or at the most three, and that in turn; and let one interpret:28 but if there be no interpreter, let him keep silence in the church; and let him speak to himself, and to God.29 And let the prophets speak by two or three, and let the others discern.30 But if a revelation be made to another sitting by, let the first keep silence.31 For ye all can prophesy one by one, that all may learn, and all may be exhorted;32 and the spirits of the prophets are subject to the prophets;33 for God is not a God of confusion, but of peace. As in all the churches of the saints,34 let the women keep silence in the churches: for it is not permitted unto them to speak; but let them be in subjection, as also saith the law.35 And if they would learn anything, let them ask their own husbands at home: for it is shameful for a woman to speak in the church.36 What? was it from you that the word of God went forth? or came it unto you alone?37 If any man thinketh himself to be a prophet, or spiritual, let him take knowledge of the things which I write unto you, that they are the commandment of the Lord.38 But if any man is ignorant, let him be ignorant.39 Wherefore, my brethren, desire earnestly to prophesy, and forbid not to speak with tongues.40 But let all things be done decently and in order.