1 KOR 15
Tashin Almasihu daga Matattu
1 t A yanzu kuma, 'yan'uwa, zan tuna muku da bisharar da na sanar da ku, wadda kuka karɓa, wadda kuke bi,
2 t wadda kuma ake cetonku da ita, muddin kun riƙe maganar da na sanar da ku da kyau, in ba sama sama ne kuka gaskata ba.
3 t Jawabi mafi muhimmanci da na sanar da ku, shi ne wanda na karɓo, cewa, Almasihu ya mutu domin zunubanmu, kamar yadda Littattafai suka faɗa, 4 t cewa an binne shi, an ta da shi a rana ta uku, kamar yadda Littattafai suka faɗa, 5 t ya kuma bayyana ga Kefas, sa'an nan ga sha biyun. 6 Sa'an nan ya bayyana ga 'yan'uwa fiye da ɗari biyar a lokaci guda, yawancinsu kuwa suna nan har zuwa yanzu, amma waɗansu sun yi barci. 7 t Sa'an nan ya bayyana ga Yakubu, sa'an nan ga dukan manzanni. 8 t Daga ƙarshen duka ya bayyana a gare ni, ni ma da nake kasasshe, marar cancanta. 9 t Don ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban ma isa a ce da ni manzo ba, saboda na tsananta wa Ikkilisiyar Allah. 10 t Amma saboda alherin Allah na zama yadda nake, alherin da ya yi mini kuwa ba a banza yake ba. Har ma na fi kowannensu aiki, ba kuwa ni ba, alherin Allah ne da yake zuciyata.
11 To, ko ni ne dai, ko kuma su ne, haka muke wa'azi, ta haka kuma kuka gaskata.Tashin Matattu
12 t To, da yake ana wa'azin Almasihu a kan an tashe shi daga matattu, ƙaƙa waɗansunku suke cewa, babu tashin matattu? 13 In dai babu tashin matattu, ashe, ba a ta da Almasihu ba ke nan. 14 t In kuwa ba a ta da Almasihu ba, to, ashe, wa'azinmu a banza ne, bangaskiyarku kuma banza ce. 15 t Sai ma ya zamana mun yi wa Allah shaidar zur ke nan, domin mun shaida Allah, cewa ya ta da Almasihu, wanda kuwa bai tasar ba, in da gaskiya ne ba a ta da matattu. 16 Don kuwa in ba a ta da matattu, ashe, Almasihu ma ba a ta da shi ba ke nan. 17 t In kuwa ba a ta da Almasihu ba, ashe, bangaskiyarku banza ce, har yanzu kuma kuna tare da zunubanku. 18 Ashe, waɗanda suka yi barci a kan su na Almasihu, sun hallaka ke nan.
19 t Da begenmu ga Almasihu domin wannan rai ne kaɗai, ai, da mun fi kowa zama abin tausayi.
20 t Amma ga hakika an ta da Almasihu daga matattu, shi ne ma nunan fari na waɗanda suka yi barci. 21 t Tun da yake mutuwa ta wurin mutum ta faru, haka kuma tashin matattu ta wurin Mutum yake. 22 t Kamar yadda duk ake mutuwa saboda Adamu, haka duk za a rayar da su saboda Almasihu. 23 t Amma kowanne bi da bi, Almasihu ne nunan fari, sa'an nan a ranar komowarsa, waɗanda suke na Almasihu. 24 t Sa'an nan sai ƙarshen, sa'ad da zai mayar wa Allah Uba mulki, bayan ya shafe dukkan sarauta da mulki da iko. 25 t Domin kuwa lalle ne ya yi mulki, har ya take dukkan maƙiyansa. 26 t Magabciyar ƙarshe da za a shafe, ita ce mutuwa. 27 t “Gama Allah ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa.” Amma da aka ce, “An sarayar da kome karƙashin ikonsa” a fili yake shi wannan da ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa ɗin, a keɓe yake.
28 t Sa'ad da kuma aka sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa ɗin, sa'an nan ne Ɗan da kansa shi ma zai sarayar da kansa ga wannan da ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa, domin Allah yă tabbata shi ne kome da kome.
29 In ba haka ba, mene ne nufin waɗanda ake yi wa baftisma saboda matattu? In ba a ta da matattu sam, don me ake yi wa waɗansu baftisma saboda su? 30 t Don me kuma nake a cikin hatsari a kowane lokaci? 31 t Na hakikance 'yan'uwa, saboda taƙama da ku da nake yi a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu, a kowace rana sai na sallama raina ga mutuwa! 32 t Idan bisa ga ra'ayin mutum ne, na yi kokawa da namomin jeji a Afisa, mece ce ribata in dai har ba a ta da matattu? “Ba sai mu yi ta ci da sha ba, da yake gobe za mu mutu?” 33 Kada fa a yaudare ku! “Zama da mugaye yakan ɓata halayen kirki.”
34 Ku farka daga magagi, ku kama aikin adalci, ku daina yin zunubi. Waɗansu kam, ba su da sanin Allah. Na faɗi wannan ne don ku kunyata.Tashin Jiki
35 t Watakila wani zai yi tambaya, “Ta yaya ake ta da matattu? Da wace irin kama kuma suke fitowa?” 36 t Kai, marar azanci! Abin da ka shuka, ai, ba zai tsiro ba sai ya mutu. 37 Abin da ka shuka kuma, ba shi ne ainihin abin da zai kasance ba, ƙwaya ce ƙawai, ko ta alkama ce, ko kuma, wata iri dabam. 38 t Amma Allah yakan ba ta kama, yadda ya nufa, kowace ƙwaya da irin tata kama. 39 Don ba dukan tsoka ce iri ɗaya ba, mutane da irin tasu, dabbobi ma da irin tasu, tsuntsaye da irin tasu, kifaye kuma da irin tasu. 40 Akwai halitta irin ta Sama, akwai kuma irin ta ƙasa. Amma ɗaukakar irin ta Sama dabam, ɗaukakar irin ta ƙasa kuma dabam.
41 Ɗaukakar rana dabam, ta wata dabam, ta taurari kuma dabam. Wani tauraro kuwa yakan bambanta da wani a wajen ɗaukaka.
42 t Haka kuma yake ga tashin matattu. Akan shuka su da halin ruɓa, akan kuma ta da su da halin rashin ruɓa. 43 t Akan shuka da wulakanci, akan tasa da ɗaukaka, akan shuka da rashin ƙarfi, akan tasa da ƙarfi. 44 t Akan shuka da jikin mutuntaka, akan tasa da jiki na ruhu. Da yake akwai jiki na mutuntaka, lalle kuma akwai jiki na ruhu. 45 t Haka kuma yake a rubuce, “Mutumin farko, Adamu, ya zama rayayyen taliki,” Adamun ƙarshe kuwa Ruhu ne mai rayarwa. 46 Amma ba shi na Ruhun nan ne ya fara bayyana ba, na mutuntaka ne, daga baya kuma sai na Ruhu. 47 t Mutumin farko daga ƙasa yake, na turɓaya ne. Na biyun kuwa daga Sama yake. 48 t Kamar yadda shi na turɓayar nan yake, haka kuma waɗanda suke na turɓaya suke. Kamar yadda shi na Saman nan yake, haka kuma waɗanda suke na Sama suke. 49 t Kamar yadda muka ɗauki siffar na turɓayar nan, haka kuma za mu ɗauki siffar na Saman nan.
50 t Ina dai gaya muku wannan 'yan'uwa, ba shi yiwuwa jiki mai tsoka da jini ya sami gādo a Mulkin Allah, haka kuma mai ruɓa ba ya gādon marar ruɓa.
51 t Ga shi, zan sanar da ku wani asiri! Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, amma dukanmu za a sauya kamanninmu, 52 t farat ɗaya da ƙyiftawar ido, da jin busar ƙaho na ƙarshe, domin za a busa ƙaho, za a kuma ta da matattu da halin rashin ruɓa, za a kuma sauya kamanninmu. 53 t Domin lalle ne, marar ruɓa ya maye mai ruɓar nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwar nan.
54 t Sa'ad da kuma marar ruɓa ya maye mai ruɓar nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwar nan, a sa'an nan ne fa maganar nan da take a rubuce za a cika ta, cewa,
“An shafe mutuwa da aka ci nasararta.”
55 t “Ke mutuwa, ina nasararki?
Ke mutuwa, ina ƙarinki?”
56 t Ai, zunubi shi ne ƙarin mutuwa, Shari'a kuwa ita ce sanadin ƙarfin zunubi.
57 t Godiya tā tabbata ga Allah wanda yake ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu.
58 t Don haka, ya 'yan'uwana, ƙaunatattu, ku tsaya a kafe, kullum kuna himmantuwa ga aikin Ubangiji, domin kuwa kun san famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.
1 Corinthians 15
1 Now I make known unto you brethren, the gospel which I preached unto you, which also ye received, wherein also ye stand,2 by which also ye are saved, if ye hold fast the word which I preached unto you, except ye believed in vain.3 For I delivered unto you first of all that which also I received: that Christ died for our sins according to the scriptures;4 and that he was buried; and that he hath been raised on the third day according to the scriptures;5 and that he appeared to Cephas; then to the twelve;6 then he appeared to above five hundred brethren at once, of whom the greater part remain until now, but some are fallen asleep;7 then he appeared to James; then to all the apostles;8 and last of all, as to the child untimely born, he appeared to me also.9 For I am the least of the apostles, that am not meet to be called an apostle, because I persecuted the church of God.10 But by the grace of God I am what I am: and his grace which was bestowed upon me was not found vain; but I labored more abundantly than they all: yet not I, but the grace of God which was with me.11 Whether then it be I or they, so we preach, and so ye believed.12 Now if Christ is preached that he hath been raised from the dead, how say some among you that there is no resurrection of the dead?13 But if there is no resurrection of the dead, neither hath Christ been raised:14 and if Christ hath not been raised, then is our preaching vain, your faith also is vain.15 Yea, we are found false witnesses of God; because we witnessed of God that he raised up Christ: whom he raised not up, if so be that the dead are not raised.16 For if the dead are not raised, neither hath Christ been raised:17 and if Christ hath not been raised, your faith is vain; ye are yet in your sins.18 Then they also that are fallen asleep in Christ have perished.19 If we have only hoped in Christ in this life, we are of all men most pitiable.20 But now hath Christ been raised from the dead, the firstfruits of them that are asleep.21 For since by man came death, by man came also the resurrection of the dead.22 For as in Adam all die, so also in Christ shall all be made alive.23 But each in his own order: Christ the firstfruits; then they that are Christ’s, at his coming.24 Then cometh the end, when he shall deliver up the kingdom to God, even the Father; when he shall have abolished all rule and all authority and power.25 For he must reign, till he hath put all his enemies under his feet.26 The last enemy that shall be abolished is death.27 For, He put all things in subjection under his feet. But when he saith, All things are put in subjection, it is evident that he is excepted who did subject all things unto him.28 And when all things have been subjected unto him, then shall the Son also himself be subjected to him that did subject all things unto him, that God may be all in all.29 Else what shall they do that are baptized for the dead? If the dead are not raised at all, why then are they baptized for them?30 Why do we also stand in jeopardy every hour?31 I protest by that glorifying in you, brethren, which I have in Christ Jesus our Lord, I die daily.32 If after the manner of men I fought with beasts at Ephesus, what doth it profit me? If the dead are not raised, let us eat and drink, for to-morrow we die.33 Be not deceived: Evil companionships corrupt good morals.34 Awake to soberness righteously, and sin not; for some have no knowledge of God: I speak this to move you to shame.35 But some one will say, How are the dead raised? and with what manner of body do they come?36 Thou foolish one, that which thou thyself sowest is not quickened except it die:37 and that which thou sowest, thou sowest not the body that shall be, but a bare grain, it may chance of wheat, or of some other kind;38 but God giveth it a body even as it pleased him, and to each seed a body of its own.39 All flesh is not the same flesh: but there is one flesh of men, and another flesh of beasts, and another flesh of birds, and another of fishes.40 There are also celestial bodies, and bodies terrestrial: but the glory of the celestial is one, and the glory of the terrestrial is another.41 There is one glory of the sun, and another glory of the moon, and another glory of the stars; for one star differeth from another star in glory.42 So also is the resurrection of the dead. It is sown in corruption; it is raised in incorruption:43 it is sown in dishonor; it is raised in glory: it is sown in weakness; it is raised in power:44 it is sown a natural body; it is raised a spiritual body. If there is a natural body, there is also a spiritual body.45 So also it is written, The first man Adam became a living soul. The last Adam became a life-giving spirit.46 Howbeit that is not first which is spiritual, but that which is natural; then that which is spiritual.47 The first man is of the earth, earthy: the second man is of heaven.48 As is the earthy, such are they also that are earthy: and as is the heavenly, such are they also that are heavenly.49 And as we have borne the image of the earthy, we shall also bear the image of the heavenly.50 Now this I say, brethren, that flesh and blood cannot inherit the kingdom of God; neither doth corruption inherit incorruption.51 Behold, I tell you a mystery: We all shall not sleep, but we shall all be changed,52 in a moment, in the twinkling of an eye, at the last trump: for the trumpet shall sound, and the dead shall be raised incorruptible, and we shall be changed.53 For this corruptible must put on incorruption, and this mortal must put on immortality.54 But when this corruptible shall have put on incorruption, and this mortal shall have put on immortality, then shall come to pass the saying that is written, Death is swallowed up in victory.55 O death, where is thy victory? O death, where is thy sting?56 The sting of death is sin; and the power of sin is the law:57 but thanks be to God, who giveth us the victory through our Lord Jesus Christ.58 Wherefore, my beloved brethren, be ye stedfast, unmoveable, always abounding in the work of the Lord, forasmuch as ye know that your labor is not vain in the Lord.