previous next

1 KOR 2

Shelar Almasihu Gicciyeyye

1  t Sa'ad da na zo wurinku, 'yan'uwa, ban zo ina sanar da ku asiran Allah ta wurin iya magana ko gwada hikima ba. 2 t Don na ƙudura a raina, sa'ad da nake zaune da ku, ba zan so sanin kome ba, sai dai Yesu Almasihu, shi ma kuwa gicciyeyye. 3 t Ina kuma tare da ku ne da rauni, da tsoro, da rawar jiki ƙwarai. 4 t Jawabina da wa'azina, ba su danganta ga maganar rarrashi ko ta wayo ba, sai dai ga rinjaye na ikon Ruhu,

5 t kada bangaskiyarku ta dogara ga hikimar mutane, sai ga ƙarfin Allah.

Bayani daga Ruhun Allah


6  t Duk da haka dai muna sanar da hikima ga waɗanda suka kammala, sai dai ba hikimar wannan zamani ba, ba kuwa ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda suke shuɗewa ba. 7 Amma muna maganar asirtacciyar hikima ta Allah, wadda dā ɓoyayyiya ce, wato, hikimar da Allah ya ƙaddara tun gaban farkon zamanai, domin ɗaukakarmu. 8 t A cikin masu mulkin zamanin nan, ba wanda ya gane hikimar nan, don da sun gane ta, da ba su gicciye Ubangiji Maɗaukaki ba.

9 t Amma kuwa yadda yake a rubuce ke nan cewa,
“Abubuwan da ido bai taɓa gani ba,
Kunne bai taɓa ji ba,
Zuciyar mutum kuma ba ta ko riya ba,
Waɗanda Allah ya tanadar wa masu ƙaunarsa,”
10  t mu ne Allah ya bayyana wa, ta wurin Ruhu, domin Ruhu shi yake fayyace kome, har ma zurfafan al'amuran Allah. 11 t Wane ne a cikin mutane ya san tunanin wani mutum, in ba ruhun shi mutumin ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah. 12 t Mu kuwa ba ruhun duniya muka samu ba, sai dai Ruhu wanda yake daga wurin Allah, domin mu fahimci abubuwan da Allah ya yi mana baiwa hannu sake.

13 t Su ne kuwa muke sanarwa ta maganar da ba hikimar ɗan adam ce ta koyar ba, sai dai wadda Ruhu ya koyar, muna bayyana al'amura masu ruhu ga waɗanda suke na ruhu.
14  t Mutumin da ba shi da Ruhu yakan ƙi yin na'am da al'amuran Ruhun Allah, don wauta ne a gare shi, ba kuwa zai iya fahimtarsu ba, domin ta wurin ruhu ne ake rarrabewa da su. 15 Mutumin da yake na ruhu kuwa yakan rarrabe da kome, shi kansa kuma ba mai jarraba shi. 16 t “Wa ya taɓa sanin tunanin Ubangiji, har da zai koya masa?” Mu kuwa tunaninmu na Almasihu ne.

1 Corinthians 2

1 And I, brethren, when I came unto you, came not with excellency of speech or of wisdom, proclaiming to you the testimony of God.2 For I determined not to know anything among you, save Jesus Christ, and him crucified.3 And I was with you in weakness, and in fear, and in much trembling.4 And my speech and my preaching were not in persuasive words of wisdom, but in demonstration of the Spirit and of power:5 that your faith should not stand in the wisdom of men, but in the power of God.6 We speak wisdom, however, among them that are fullgrown: yet a wisdom not of this world, nor of the rulers of this world, who are coming to nought:7 but we speak God’s wisdom in a mystery, even the wisdom that hath been hidden, which God foreordained before the worlds unto our glory:8 which none of the rulers of this world hath known: for had they known it, they would not have crucified the Lord of glory:9 but as it is written, Things which eye saw not, and ear heard not, And which entered not into the heart of man, Whatsoever things God prepared for them that love him.

10 But unto us God revealed them through the Spirit: for the Spirit searcheth all things, yea, the deep things of God.11 For who among men knoweth the things of a man, save the spirit of the man, which is in him? even so the things of God none knoweth, save the Spirit of God.12 But we received, not the spirit of the world, but the spirit which is from God; that we might know the things that were freely given to us of God.13 Which things also we speak, not in words which man’s wisdom teacheth, but which the Spirit teacheth; combining spiritual things with spiritual words.14 Now the natural man receiveth not the things of the Spirit of God: for they are foolishness unto him; and he cannot know them, because they are spiritually judged.15 But he that is spiritual judgeth all things, and he himself is judged of no man.16 For who hath known the mind of the Lord, that he should instruct him? But we have the mind of Christ.