1 KOR 3
Abokan Aiki na Allah
1 t Amma ni, 'yan'uwa, ban iya yi muku jawabi ba, kamar yadda nake yi wa mutanen da suke na ruhu, sai dai kamar yadda nake yi wa masu halin mutuntaka, kamar jarirai a cikin bin Almasihu. 2 t Nono ne na shayar da ku, ba abinci mai tauri na ba ku ba, don ba ku isa ci ba a lokacin, ko a yanzu ma ba ku isa ba, 3 t don har a yanzu ku masu halin mutuntaka ne. Muddin akwai kishi da jayayya a tsakaninku, ashe, ku ba masu halin mutuntaka ba ne, kuna kuma aikata halin mutuntaka?
4 t Don in wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afolos ne,” ashe, ba aikata halin mutuntaka kuke yi ba?
5 To, wane ne Afolos? wane ne Bulus kuma? Ashe, ba bayi ne kawai ba, waɗanda kuka ba da gaskiya ta wurinsu, ko wannensu kuwa gwargwadon abin da Ubangiji ya ba shi? 6 t Ni na yi shuka, Afolos ya yi banruwa, amma Allah ne ya girmar. 7 Don haka da mai shukar, da mai banruwan, ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai, shi da ya girmar. 8 t Da mai shukar, da mai banruwan, duk daidai suke, sai dai ko wanne zai sami tasa ladar gwargwadon wahalarsa,
9 t gama mu abokan aiki ne na Allah, ku kuwa gona ce ta Allah, ginin Allah kuma.
10 t Kamar gwanin magini, haka na sa harsashin gini, gwargwadon baiwar alherin da Allah ya yi mini, wani kuma yana ɗora gini a kai. Sai dai kowane mutum, yă lura da irin ginin da yake ɗorawa a kai. 11 t Harsashin kam, ba wanda yake iya sa wani dabam da wanda aka riga aka sa, wato, Yesu Almasihu. 12 To, kowa ya yi ɗori da zinariya a kan harsashin nan, ko da azurfa, ko da duwatsun alfarma, ko da itace, ko da shuci, ko da kara, 13 t ai, aikin kowane mutum zai bayyana, domin ranar nan za ta tona shi, gama za a bayyana ta da wuta, wutar kuwa za ta gwada aikin kowa a san irinsa. 14 In aikin da kowane mutum ya ɗora a kan harsashin nan ya tsira, to, zai sami sakamako.
15 t In kuwa aikin wani ya ƙone, to, sai yă yi hasara, ko da yake shi da kansa zai tsira, amma kamar ya bi ta wuta ne.
16 t Ashe, ba ku sani ku Haikalin Allah ne ba, Ruhun Allah kuma yana zaune a zuciyarku?
17 In wani ya ɓāta Haikalin Allah, Allah zai ɓāta shi. Gama Haikalin Allah tsattsarka ne, ku kanku Haikalinsa ne.
18 t Kada kowa yă ruɗi kansa. In waninku ya zaci shi mai hikima ne, yadda duniya ta ɗauki hikima, sai yă mai da kansa marar hikima, domin ya sami zama mai hikima. 19 t Gama hikimar duniyar nan wauta ce a gun Allah, domin a rubuce yake, “Yakan kama masu hikima da makircinsu.” 20 t Har wa yau, “Ubangiji ya san tunanin masu hikima banza ne.” 21 t Saboda haka kada kowa yă yi fariya da 'yan adam. Don kuwa kome naku ne, 22 t ko Bulus, ko Afolos, ko Kefas, ko duniya, ko rai, ko mutuwa, ko abubuwan yanzu, ko da na gaba, ai, duk naku ne. 23 t Ku kuwa na Almasihu ne, Almasihu kuma na Allah ne.
1 Corinthians 3
1 And I, brethren, could not speak unto you as unto spiritual, but as unto carnal, as unto babes in Christ.2 I fed you with milk, not with meat; for ye were not yet able to bear it: nay, not even now are ye able;3 for ye are yet carnal: for whereas there is among you jealousy and strife, are ye not carnal, and do ye not walk after the manner of men?4 For when one saith, I am of Paul; and another, I am of Apollos; are ye not men?5 What then is Apollos? and what is Paul? Ministers through whom ye believed; and each as the Lord gave to him.6 I planted, Apollos watered; but God gave the increase.7 So then neither is he that planteth anything, neither he that watereth; but God that giveth the increase.8 Now he that planteth and he that watereth are one: but each shall receive his own reward according to his own labor.9 For we are God’s fellow-workers: ye are God’s husbandry, God’s building.10 According to the grace of God which was given unto me, as a wise masterbuilder I laid a foundation; and another buildeth thereon. But let each man take heed how he buildeth thereon.11 For other foundation can no man lay than that which is laid, which is Jesus Christ.12 But if any man buildeth on the foundation gold, silver, costly stones, wood, hay, stubble;13 each man’s work shall be made manifest: for the day shall declare it, because it is revealed in fire; and the fire itself shall prove each man’s work of what sort it is.14 If any man’s work shall abide which he built thereon, he shall receive a reward.15 If any man’s work shall be burned, he shall suffer loss: but he himself shall be saved; yet so as through fire.16 Know ye not that ye are a temple of God, and that the Spirit of God dwelleth in you?17 If any man destroyeth the temple of God, him shall God destroy; for the temple of God is holy, and such are ye.18 Let no man deceive himself. If any man thinketh that he is wise among you in this world, let him become a fool, that he may become wise.19 For the wisdom of this world is foolishness with God. For it is written, He that taketh the wise in their craftiness:20 and again, The Lord knoweth the reasonings of the wise that they are vain.21 Wherefore let no one glory in men. For all things are yours;22 whether Paul, or Apollos, or Cephas, or the world, or life, or death, or things present, or things to come; all are yours;23 and ye are Christ’s; and Christ is God’s.