1 KOR 4
Aikin Manzanni
1 t Ta haka ya kamata a san mu da zama ma'aikatan Almasihu, masu riƙon amanar asirtattun al'amuran Allah. 2 Har wa yau dai, abin da ake bukata ga mai riƙon amana, a same shi amintacce. 3 A gare ni kam, sassauƙan abu ne a ce ku ne za ku gwada ni, ko kuwa a gwada ni a gaban kowace mahukunta ta mutane. Ni ma ba na gwada kaina. 4 t Ban sani ina da wani laifi ba, amma ba don wannan na kuɓuta ba, ai, Ubangiji shi ne mai gwada ni.
5 t Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.
6 t To, 'yan'uwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina, da kuma Afolos saboda ku, don ku yi koyi da mu, cewa, kada ku zarce abin da yake a rubuce, kada kuma waninku ya yi fahariya da wani a kan wani.
7 t Wa ya fifita ka da sauran? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? Da yake karɓa ka yi, don me kake fahariya, kamar ba karɓa ka yi ba?
8 t Mhm, wato, har kun riga kun yi hamdala! Har kun wadata! Har ma kun yi sarauta ba tare da mu ba ma! Da ma a ce kun yi mulki mana, har mu ma mu yi tare da ku! 9 t Don a ganina, Allah ya bayyana mu, mu manzanni, koma bayan duka ne, kamar waɗanda mutuwa yake jewa a kansu, don mun zama abin nuni ga duniya, da mala'iku duk da mutane. 10 t An ɗauke mu marasa azanci saboda Almasihu, wato, ku kuwa masu azanci cikin Almasihu! Wato, mu raunana ne, ku kuwa ƙarfafa! Ku kam, ana ganinku da martaba, mu kuwa a wulakance! 11 t Har a yanzu haka, yunwa muke ji, da ƙishirwa, muna huntanci, ana bugunmu, kuma yawo muke yi haka, ba mu da gida. 12 t Guminmu muke ci. In an zage mu, mukan sa albarka. In an tsananta mana, mukan daure.
13 t In an ci mutuncinmu, mukan ba da haƙuri. Mun zama, har a yanzu ma, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.
14 t Ba don in kunyata ku na rubuta wannan ba, sai dai don in gargaɗe ku a kan cewa, ku 'ya'yana ne, ƙaunatattu. 15 t Ko da kuna da malamai masu ɗumbun yawa, amma ba ku da ubanni da yawa, don ni ne ubanku a cikin Almasihu ta wurin bishara. 16 t Don haka, ina roƙon ku, ku yi koyi da ni. 17 t Saboda haka, na aika muku da Timoti, wanda yake shi ne ɗana ƙaunatacce, amintacce kuma a cikin Ubangiji, zai kuwa tuna muku da ka'idodina na bin Almasihu, kamar yadda nake koyarwa a ko'ina, a kowace ikkilisiya. 18 Waɗansu har suna ɗaga kai, kamar ba zan zo wurinku ba. 19 t Amma kuwa zan zo gare ku ba da daɗewa ba, in Ubangiji ya yarda, zan kuma bincika, in ga ƙarfin mutane masu ɗaga kan nan, ba maganganunsu ba. 20 Domin Mulkin Allah ba ga maganar baka yake ba, sai dai ga ƙarfi. 21 t To, me kuka zaɓa, in zo muku da sanda, ko kuwa da fuskar ƙauna da lumana?
1 Corinthians 4
1 Let a man so account of us, as of ministers of Christ, and stewards of the mysteries of God.2 Here, moreover, it is required in stewards, that a man be found faithful.3 But with me it is a very small thing that I should be judged of you, or of man’s judgment: yea, I judge not mine own self.4 For I know nothing against myself; yet am I not hereby justified: but he that judgeth me is the Lord.5 Wherefore judge nothing before the time, until the Lord come, who will both bring to light the hidden things of darkness, and make manifest the counsels of the hearts; and then shall each man have his praise from God.6 Now these things, brethren, I have in a figure transferred to myself and Apollos for your sakes; that in us ye might learn not to go beyond the things which are written; that no one of you be puffed up for the one against the other.7 For who maketh thee to differ? and what hast thou that thou didst not receive? but if thou didst receive it, why dost thou glory as if thou hadst not received it?8 Already are ye filled, already ye are become rich, ye have come to reign without us: yea and I would that ye did reign, that we also might reign with you.9 For, I think, God hath set forth us the apostles last of all, as men doomed to death: for we are made a spectacle unto the world, both to angels and men.10 We are fools for Christ’s sake, but ye are wise in Christ; we are weak, but ye are strong; ye have glory, but we have dishonor.11 Even unto this present hour we both hunger, and thirst, and are naked, and are buffeted, and have no certain dwelling-place;12 and we toil, working with our own hands: being reviled, we bless; being persecuted, we endure;13 being defamed, we entreat: we are made as the filth of the world, the offscouring of all things, even until now.14 I write not these things to shame you, but to admonish you as my beloved children.15 For though ye have ten thousand tutors in Christ, yet have ye not many fathers; for in Christ Jesus I begat you through the gospel.16 I beseech you therefore, be ye imitators of me.17 For this cause have I sent unto you Timothy, who is my beloved and faithful child in the Lord, who shall put you in remembrance of my ways which are in Christ, even as I teach everywhere in every church.18 Now some are puffed up, as though I were not coming to you.19 But I will come to you shortly, if the Lord will; and I will know, not the word of them that are puffed up, but the power.20 For the kingdom of God is not in word, but in power.21 What will ye? shall I come unto you with a rod, or in love and a spirit of gentleness?