previous next

1 KOR 5

Hukunci a kan Fasikanci

1  t Ana ta cewa akwai fasikanci a tsakaninku, irin wanda ba a yi ko a cikin al'ummai, har wani yana zama da matar ubansa.

2 t A! Har kuwa alfarma kuke yi! Ashe, ba gwamma ku yi baƙin ciki ba, har a fitar da wanda ya yi wannan mugun aiki daga cikin jama'arku?
3  t Ko da yake a jiki ba na nan, ai, ruhuna yana nan, kamar ma ina nan ne, har ma na riga na yanke wa mutumin da ya yi abin nan hukunci da sunan Ubangijinmu Yesu. 4 t Sa'ad da kuka hallara, ruhuna kuma yana nan, da kuma ikon Ubangijinmu Yesu,

5 t sai ku miƙa irin wannan mutum ga Shaiɗan, don yă hallaka jikinsa, ruhunsa kuma ya tsira a ranar Ubangiji Yesu.
6  t Fāriyarku ba shi da kyau. Ashe, ba ku sani ba, ɗan yisti kaɗan yake game dukkan curin gurasa? 7 t Ku fitar da tsohon yistin nan, don ku zama sabon curi, domin hakika an raba ku da yistin, da yake an riga an yanka Ɗan Ragonmu na Idin Ƙetarewa, wato, Almasihu.

8 t Saboda haka, sai mu riƙa yin idinmu, ba da gurasa mai tsohon yisti ba, ba kuwa gauraye da yisti na ƙeta da na mugunta ba, sai dai da gurasa marar yisti ta sahihanci da ta gaskiya.
9  t Na rubuta muku a cikin wasiƙata, cewa kada ku yi cuɗanya da fasikai. 10 t Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita, da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai yă zama dole ku fita daga duniya. 11 t Sai dai na rubuta muku ne, don kada ku yi cuɗanya da duk wanda ake kira ɗan'uwa, mai bi, in yana fasikanci, ko makwaɗaici, ko matsafi, ko mai zage-zage, ko mashayi, ko mazambaci, kada ku ko ci abinci da irin waɗannan. 12 t Ina ruwana da hukunta waɗanda ba namu ba? Ba waɗanda suke a cikin Ikkilisiya za ku hukunta ba? 13 t Allah ne yake hukunta waɗanda ba namu ba. Ku kori mugun nan daga cikinku.

1 Corinthians 5

1 It is actually reported that there is fornication among you, and such fornication as is not even among the Gentiles, that one of you hath his father’s wife.2 And ye are puffed up, and did not rather mourn, that he that had done this deed might be taken away from among you.3 For I verily, being absent in body but present in spirit, have already as though I were present judged him that hath so wrought this thing,4 in the name of our Lord Jesus, ye being gathered together, and my spirit, with the power of our Lord Jesus,5 to deliver such a one unto Satan for the destruction of the flesh, that the spirit may be saved in the day of the Lord Jesus.6 Your glorying is not good. Know ye not that a little leaven leaveneth the whole lump?7 Purge out the old leaven, that ye may be a new lump, even as ye are unleavened. For our passover also hath been sacrificed, even Christ:8 wherefore let us keep the feast, not with old leaven, neither with the leaven of malice and wickedness, but with the unleavened bread of sincerity and truth.9 I wrote unto you in my epistle to have no company with fornicators;10 not at all meaning with the fornicators of this world, or with the covetous and extortioners, or with idolaters; for then must ye needs go out of the world:11 but as it is, I wrote unto you not to keep company, if any man that is named a brother be a fornicator, or covetous, or an idolater, or a reviler, or a drunkard, or an extortioner; with such a one no, not to eat.12 For what have I to do with judging them that are without? Do not ye judge them that are within?13 But them that are without God judgeth. Put away the wicked man from among yourselves.