1 KOR 6
Kada a Kai Ƙara Gaban Marasa Bi
1 t In waninku yana da wata ƙara a game da ɗan'uwansa, ashe, zai yi ƙurun kai maganar a gaban marasa adalci, ba a gaban tsarkaka ba? 2 t Ashe, ba ku sani ba, tsarkaka ne za su yi wa duniya shari'a? In kuwa ku ne za ku yi wa duniya shari'a, ashe, ba za ku iya shari'ar ƙananan al'amura ba? 3 Ba ku sani ba, za mu yi wa mala'iku shari'a, balle al'amuran da suka shafi zaman duniyar nan? 4 In kuwa kuna da irin waɗannan ƙararraki, don me kuma kuke kai su gaban waɗanda su ba kome ba ne, a game da Ikkilisiya? 5 t Na faɗi wannan ne don ku kunyata. Ashe, wato, ba ko mutum ɗaya mai hikima a cikinku, da zai iya sasanta tsakanin 'yan'uwa?
6 t Amma ɗan'uwa yakan kai ƙarar ɗan'uwa, gaban marasa ba da gaskiya kuma?
7 t Ku yi ƙarar juna ma, ai, hasara ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura a zambace ku?
8 t Amma, ga shi, ku da kanku kuna cuta, kuna zamba, har ma 'yan'uwanku kuke yi wa!
9 t Ashe, ba ku sani ba, marasa adalci ba za su sami gādo a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo, 10 ko ɓarayi, ko makwaɗaita, ko mashaya, ko masu zage-zage, ko mazambata, da za su sami gādo a cikin Mulkin Allah.
11 t Waɗansunku ma dā haka suke, amma an wanke ku, an tsarkake ku, an kuma kuɓutar da ku, da sunan Ubangiji Yesu Almasihu, da kuma Ruhun Allahnmu.Ku Ɗaukaka Allah da Jikinku
12 t “Dukan abubuwa halal ne a gare ni,” amma ba dukan abubuwa ne masu amfani ba. “Abu duka halal na a gare ni,” amma ba zan zama bawan kome ba. 13 t “Abinci don ciki aka yi shi, ciki kuma don abinci”–Allah kuma zai hallaka duka biyu, wannan da wancan. Jiki kam, ba don fasikanci yake ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki.
14 t Allah ya ta da Ubangiji daga matattu, haka mu ma zai ta da mu da ikonsa.
15 t Ashe, ba ku sani ba jikinku gaɓoɓin Almasihu ne? Ashe kuma, sai in ɗauki gaɓoɓin Almasihu in mai da su gaɓoɓin karuwa? Faufau! 16 t Ashe, ba ku sani ba, duk wanda ya tara da karuwa, sun zama jiki ɗaya ke nan? Domin a rubuce yake cewa, “Su biyun za su zama jiki ɗaya.” 17 t Duk wanda kuwa yake haɗe da Ubangiji, sun zama ɗaya a ruhu ke nan. 18 t Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubin da mutum yake yi bai shafi jikinsa ba, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne. 19 t Ashe, ba ku sani ba, jikinku Haikali ne na Ruhu Mai Tsarki wanda yake a zuciyarku, wanda kuka kuma samu a gun Allah? Ai, ku ba mallakar kanku ba ne. 20 t Sayenku aka yi da tamani. To, sai ku ɗaukaka Allah da jikinku.
1 Corinthians 6
1 Dare any of you, having a matter against his neighbor, go to law before the unrighteous, and not before the saints?2 Or know ye not that the saints shall judge the world? and if the world is judged by you, are ye unworthy to judge the smallest matters?3 Know ye not that we shall judge angels? how much more, things that pertain to this life?4 If then ye have to judge things pertaining to this life, do ye set them to judge who are of no account in the church?5 I say this to move you to shame. What, cannot there be found among you one wise man who shall be able to decide between his brethren,6 but brother goeth to law with brother, and that before unbelievers?7 Nay, already it is altogether a defect in you, that ye have lawsuits one with another. Why not rather take wrong? why not rather be defrauded?8 Nay, but ye yourselves do wrong, and defraud, and that your brethren.9 Or know ye not that the unrighteous shall not inherit the kingdom of God? Be not deceived: neither fornicators, nor idolaters, nor adulterers, nor effeminate, nor abusers of themselves with men,10 nor thieves, nor covetous, nor drunkards, nor revilers, nor extortioners, shall inherit the kingdom of God.11 And such were some of you: but ye were washed, but ye were sanctified, but ye were justified in the name of the Lord Jesus Christ, and in the Spirit of our God.12 All things are lawful for me; but not all things are expedient. All things are lawful for me; but I will not be brought under the power of any.13 Meats for the belly, and the belly for meats: but God shall bring to nought both it and them. But the body is not for fornication, but for the Lord; and the Lord for the body:14 and God both raised the Lord, and will raise up as through his power.15 Know ye not that your bodies are members of Christ? shall I then take away the members of Christ, and make them members of a harlot? God forbid.16 Or know ye not that he that is joined to a harlot is one body? for, The twain, saith he, shall become one flesh.17 But he that is joined unto the Lord is one spirit.18 Flee fornication. Every sin that a man doeth is without the body; but he that committeth fornication sinneth against his own body.19 Or know ye not that your body is a temple of the Holy Spirit which is in you, which ye have from God? and ye are not your own;20 for ye were bought with a price: glorify God therefore in your body.