previous next

1 KOR 8

Abincin da aka Miƙa wa Gumaka

1  t To, yanzu a game da abubuwan da aka yanka wa gumaka, mun sani dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kumbura mutum, ƙauna kuwa takan inganta shi. 2 t Duk mai gani ya san wani abu, ai, har a yanzu, bai san yadda ya kamata ya sani ba.

3 t In kuwa wani na ƙaunar Allah, to, Allah ya san shi.
4  t A game da cin abin da aka yanka wa gumaka kuwa, mun sani, duk duniyar nan gunki yana a matsayin abin da babu ne, da kuma, babu wani Allah sai ɗaya. 5 t Ko da yake, akwai waɗanda ake kira alloli a sama ko a ƙasa, don kuwa akwai “alloli” da “iyayengiji” da yawa,

6 t duk da haka dai, a gare mu kam, Allah ɗaya ne, wato Uba, wanda dukkan abubuwa suke daga gare shi, wanda mu kuma zamansa muke yi, Ubangiji kuma ɗaya ta gare shi muka kasance.
7  t Amma dai ba kowa ne yake da wannan sani ba. Amma waɗansu ta wurin sabawarsu da al'amuran gunki har yanzu, sukan ci naman da suka ɗauka kamar an yanka wa gunki ne. Saboda haka lamirinsu, da yake rarrauna ne, ya ƙazantu. 8 t Abinci ba zai ƙare mu a game da Allah ba. In mun ci, ba mu ƙaru ba, in kuma ba mu ci ba, ba mu ragu ba. 9 t Sai dai ku lura, kada 'yancin nan naku ya zama abin sa tuntuɓe ga waɗanda ba su tsai da zuciyarsu ba. 10 Amma in wani mutum, wanda yake da rarraunan lamiri, ya gan ka, kai da kake da sani, kana ci a ɗakin gunki, ashe, wannan ba zai ƙarfafa lamirinsa har ya ci abincin da aka miƙa wa gunki ba? 11 t Wato, ta sanin nan naka, sai a rushe rarraunan nan, ɗan'uwa ne kuwa wanda Almasihu ya mutu dominsa! 12 t Ta haka ne kuke yi wa Almasihu laifi, wato ta wurin yi wa 'yan'uwanku laifi, kuna rushe rarraunan lamirinsu. 13 t Saboda haka in dai cin nama ya sa ɗan'uwana tuntuɓe, har abada ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa ɗan'uwana tuntuɓe.

1 Corinthians 8

1 Now concerning things sacrificed to idols: We know that we all have knowledge. Knowledge puffeth up, but love edifieth.2 If any man thinketh that he knoweth anything, he knoweth not yet as he ought to know;3 but if any man loveth God, the same is known by him.4 Concerning therefore the eating of things sacrificed to idols, we know that no idol is anything in the world, and that there is no God but one.5 For though there be that are called gods, whether in heaven or on earth; as there are gods many, and lords many;6 yet to us there is one God, the Father, of whom are all things, and we unto him; and one Lord, Jesus Christ, through whom are all things, and we through him.7 Howbeit there is not in all men that knowledge: but some, being used until now to the idol, eat as of a thing sacrificed to an idol; and their conscience being weak is defiled.8 But food will not commend us to God: neither, if we eat not, are we the worse; nor, if we eat, are we the better.9 But take heed lest by any means this liberty of yours become a stumblingblock to the weak.10 For if a man see thee who hast knowledge sitting at meat in an idol’s temple, will not his conscience, if he is weak, be emboldened to eat things sacrificed to idols?11 For through thy knowledge he that is weak perisheth, the brother for whose sake Christ died.12 And thus, sinning against the brethren, and wounding their conscience when it is weak, ye sin against Christ.13 Wherefore, if meat causeth my brother to stumble, I will eat no flesh for evermore, that I cause not my brother to stumble.