1 YAH 3
'Ya'yan Allah
1 t Ku dubi irin ƙaunar da Uba ya nuna mana, har yake ce da mu 'ya'yan Allah, haka kuwa muke. Abin da ya sa duniya ba ta san mu ba, don ba ta san shi ba ne. 2 t Ya ku ƙaunatattuna, a yanzu mu 'ya'yan Allah ne, yadda za mu zama nan gaba kuwa, ba a bayyana ba tukuna, amma mun sani sa'ad da ya bayyana, za mu zama kamarsa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.
3 t Duk mai ƙwallafa sa zuciya gare shi haka, yana tsarkake kansa ke nan, kamar yadda shi yake Mai Tsarki.
4 t Duk mai aikata zunubi ya yi tawaye ke nan. Zunubi tawaye ne. 5 t Kun dai sani an bayyana shi domin yă ɗauke zunubai ne, a gare shi kuma ba zunubi. 6 t Kowa da yake a zaune a cikinsa, ba ya aikata zunubi. Kowa da yake aikata zunubi, bai taɓa ganinsa ba, bai ma san shi ba. 7 t Ya ku 'ya'yana ƙanana, kada fa kowa ya ɓad da ku. Shi wanda yake aikata adalci, mai adalci ne, kamar yadda Almasihu mai adalci ne. 8 t Duk mai aikata zunubi, na Iblis ne, don tun farko Iblis mai aikata zunubi ne. Dalilin bayyanar Ɗan Allah shi ne domin yă rushe aikin Iblis. 9 t Duk wanda yake haifaffen Allah, ba yakan aikata zunubi ba, domin irinsa yana a cikinsa a zaune, ba yakan aikata zunubi ba, da yake shi haifaffen Allah ne.
10 t Ta haka sai a ga waɗanda suke 'ya'yan Allah, da kuma waɗanda suke 'ya'yan Iblis, wato duk wanda ba ya aikata adalci, ba na Allah ba ne, haka kuma wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa.Ku Ƙaunaci Juna
11 t Wannan shi ne jawabin da kuka ji tun farko, cewa dai mu ƙaunaci juna, 12 t kada mu zama kamar Kayinu, wanda yake na Mugun, har ma ya kashe ɗan'uwansa. To, don me ya kashe shi? Don ayyukansa mugaye ne, na ɗan'uwansa kuwa na kirki ne. 13 t Kada ku yi mamaki, 'yan'uwa, idan duniya take ƙinku. 14 t Mu kam, mun sani mun riga mun tsere wa mutuwa, mun kai ga rai saboda muna ƙaunar 'yan'uwa. Wanda ba shi da ƙauna, zaman mutuwa yake yi. 15 t Kowa da yake ƙin dan'uwansa, mai kisankai ne. Ƙun kuwa sani ba mai kisankan da yake da rai madawwami a zauna tare da shi. 16 t Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, ta wurin ba da ransa da ya yi saboda mu. Mu kuma ya kamata mu ba da ranmu saboda 'yan'uwa. 17 t Duk kuwa wanda yake da abin hannunsa, yake kuma ganin ɗan'uwansa da rashi, sa'an nan ya rufe ido gare shi, ƙaƙa ƙaunar Allah yake zaune a cikinsa?
18 t Ya ku 'ya'yana ƙanana, kada mu nuna ƙauna da fatar baki kawai, sai dai da aikatawa da kuma gaskiya.Amincewa Gaban Allah
19 Ta haka za mu tabbata mu na gaskiya ne, har kuma mu amince wa kanmu gaban Allah, 20 duk sa'ad da zuciyarmu ta ba mu laifi, saboda Allah ya fi ta, ya kuma san kome. 21 t Ya ku ƙaunatattuna, in zuciyarmu ba ta ba mu laifi ba, sai mu je gaban Allah amincewa. 22 t Mukan kuma sami duk abin da muka roƙa a gare shi, domin muna bin umarninsa, muna kuma yin abin da yake so. 23 t Umarninsa kuwa shi ne mu gaskata da sunan Ɗansa Yesu Almasihu, mu kuma ƙaunaci juna, kamar yadda ya umarce mu. 24 t Duk mai bin umarnin Allah kuwa a dawwame yake cikinsa, Allah kuma a cikinsa. Ta haka muka tabbata ya dawwama a cikinmu, saboda Ruhun da ya ba mu.
1 John 3
1 Behold what manner of love the Father hath bestowed upon us, that we should be called children of God; and such we are. For this cause the world knoweth us not, because it knew him not.2 Beloved, now are we children of God, and it is not yet made manifest what we shall be. We know that, if he shall be manifested, we shall be like him; for we shall see him even as he is.3 And every one that hath this hope set on him purifieth himself, even as he is pure.4 Every one that doeth sin doeth also lawlessness; and sin is lawlessness.5 And ye know that he was manifested to take away sins; and in him is no sin.6 Whosoever abideth in him sinneth not: whosoever sinneth hath not seen him, neither knoweth him.7 My little children, let no man lead you astray: he that doeth righteousness is righteous, even as he is righteous:8 he that doeth sin is of the devil; for the devil sinneth from the beginning. To this end was the Son of God manifested, that he might destroy the works of the devil.9 Whosoever is begotten of God doeth no sin, because his seed abideth in him: and he cannot sin, because he is begotten of God.10 In this the children of God are manifest, and the children of the devil: whosoever doeth not righteousness is not of God, neither he that loveth not his brother.11 For this is the message which ye heard from the beginning, that we should love one another:12 not as Cain was of the evil one, and slew his brother. And wherefore slew he him? Because his works were evil, and his brother’s righteous.13 Marvel not, brethren, if the world hateth you.14 We know that we have passed out of death into life, because we love the brethren. He that loveth not abideth in death.15 Whosoever hateth his brother is a murderer: and ye know that no murderer hath eternal life abiding in him.16 Hereby know we love, because he laid down his life for us: and we ought to lay down our lives for the brethren.17 But whoso hath the world’s goods, and beholdeth his brother in need, and shutteth up his compassion from him, how doth the love of God abide in him?18 My Little children, let us not love in word, neither with the tongue; but in deed and truth.19 Hereby shall we know that we are of the truth, and shall assure our heart before him:20 because if our heart condemn us, God is greater than our heart, and knoweth all things.21 Beloved, if our heart condemn us not, we have boldness toward God;22 and whatsoever we ask we receive of him, because we keep his commandments and do the things that are pleasing in his sight.23 And this is his commandment, that we should believe in the name of his Son Jesus Christ, and love one another, even as he gave us commandment.24 And he that keepeth his commandments abideth in him, and he in him. And hereby we know that he abideth in us, by the Spirit which he gave us.