1 YAH 5
Bangaskiya ta Yi Nasara da Duniya
1 t Kowa da yake gaskata Yesu shi ne Almasihu, haifaffen Allah ne. Kowa yake ƙaunar mahaifi kuwa, yana ƙaunar ɗa kuma. 2 Ta haka muku sani muna ƙaunar 'ya'yan Allah, wato, in muna ƙaunar Allah, muna kuma bin umarninsa. 3 t Domin ƙaunar Allah ita ce mu bi umarninsa, umarninsa kuwa ba matsananta ba ne. 4 t Domin duk wanda yake haifaffen Allah yana nasara da duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta sa muka yi nasara da duniya.
5 Wane ne yake nasara da duniya, in ba wanda ya gaskata Yesu Ɗan Allah ba ne?Shaida a kan Ɗansa
6 t Shi ne wanda ya bayyana ta wurin ruwa da jini, Yesu Almasihu, ba fa ta wurin ruwa kaɗai ba, amma ta wurin ruwa da jini. 7 t Ruhu kuma shi ne mai ba da shaida, domin Ruhun shi ne gaskiya. 8 Akwai shaidu uku, wato Ruhun, da ruwa, da kuma jini, waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce. 9 t Tun da yake muna yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa. 10 t Kowa ya gaskata da Ɗan Allah, shaidar tana nan gare shi. Wanda bai gaskata Allah ba, ya ƙaryata shi ke nan, domin bai gaskata shaidar da Allah ya yi Ɗansa ba. 11 t Wannan kuma ita ce shaidar, cewa Allah yā ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa.
12 t Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai. Wanda ba shi da Ɗan Allah kuwa, ba shi da rai.Tabbatar Samun Rai Madawwami
13 t Na rubuto muku wannan ne, ku da kuka gaskata da sunan Ɗan Allah, domin ku tabbata kuna da rai madawwami. 14 t Wannan ita ce amincewarmu a gabansa, wato, in mun roƙi kome bisa ga nufinsa, sai ya saurare mu. 15 t In kuwa muka san kome muka roƙa yana sauraronmu, mun tabbata mun sami abin da muka roƙa a gare shi ke nan. 16 t Kowa ya ga ɗan'uwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai ya yi masa addu'a. Saboda mai addu'ar nan kuwa, Allah zai ba da rai ga waɗanda suka yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yake na mutuwa. Ban ce a yi addu'a domin wannan ba.
17 t Duk rashin adalci zunubi ne. Akwai kuma zunubin da ba na mutuwa ba.
18 t Mun sani kowane haifaffen Allah ba ya yin zunubi, kasancewarsa haifaffen Allah ita takan kare shi. Mugun nan kuwa ba ta taɓa shi.
19 t Mun sani mu na Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun.
20 t Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami. 21 t Ya ku 'ya'yana ƙanana, ku yi nesa da gumaka.
1 John 5
1 Whosoever believeth that Jesus is the Christ is begotten of God: and whosoever loveth him that begat loveth him also that is begotten of him.2 Hereby we know that we love the children of God, when we love God and do his commandments.3 For this is the love of God, that we keep his commandments: and his commandments are not grievous.4 For whatsoever is begotten of God overcometh the world: and this is the victory that hath overcome the world, even our faith.5 And who is he that overcometh the world, but he that believeth that Jesus is the Son of God?6 This is he that came by water and blood, even Jesus Christ; not with the water only, but with the water and with the blood.7 And it is the Spirit that beareth witness, because the Spirit is the truth.8 For there are three who bear witness, the Spirit, and the water, and the blood: and the three agree in one.9 If we receive the witness of men, the witness of God is greater: for the witness of God is this, that he hath borne witness concerning his Son.10 He that believeth on the Son of God hath the witness in him: he that believeth not God hath made him a liar; because he hath not believed in the witness that God hath borne concerning his Son.11 And the witness is this, that God gave unto us eternal life, and this life is in his Son.12 He that hath the Son hath the life; he that hath not the Son of God hath not the life.13 These things have I written unto you, that ye may know that ye have eternal life, even unto you that believe on the name of the Son of God.14 And this is the boldness which we have toward him, that, if we ask anything according to his will, he heareth us:15 and if we know that he heareth us whatsoever we ask, we know that we have the petitions which we have asked of him.16 If any man see his brother sinning a sin not unto death, he shall ask, and God will give him life for them that sin not unto death. There is a sin unto death: not concerning this do I say that he should make request.17 All unrighteousness is sin: and there is a sin not unto death.18 We know that whosoever is begotten of God sinneth not; but he that was begotten of God keepeth himself, and the evil one toucheth him not.19 We know that we are of God, and the whole world lieth in the evil one.20 And we know that the Son of God is come, and hath given us an understanding, that we know him that is true, and we are in him that is true, even in his Son Jesus Christ. This is the true God, and eternal life.21 My little children, guard yourselves from idols.