1 BIT 1
Gaisuwa
1 t Daga Bitrus, manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zaɓaɓɓun Allah da suke bare, a warwatse a Fantas, da Galatiya, da Kafadokiya, da Asiya, da kuma Bitiniya,
2 t su da suke zaɓaɓɓu bisa ga rigyasanin Allah Uba, waɗanda Ruhu kuma ya tsarkake, domin su yi wa Yesu Almasihu biyayya, su kuma tsarkaka da jininsa. Alheri da salama su yawaita a gare ku.Rayayyiyar Bege
3 t Godiya ta tabbata a gare shi, shi wanda yake Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurin tsananin jinƙansa ya sāke haifuwarmu, domin mu yi rayayyen bege, ta wurin albarkacin tashin Yesu Almasihu daga matattu, 4 t mu kuma sami gādo marar lalacewa, marar ɓāci, marar ƙarewa kuma, wanda aka keɓe muku a Sama, 5 t wato, ku da ikon Allah yake kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani. 6 t A kan wannan ne kuke da matuƙar farin ciki, ko da yake da ɗan lokaci kwa yi baƙin ciki ta dalilin gwaje-gwaje iri iri. 7 t Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne (wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan jarraba ta da wuta), domin bangaskiyar nan taku tă jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Almasihu. 8 t Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa. Ko da yake ba kwa ganinsa a yanzu, duk da haka kuna gaskatawa da shi, kuna farin ciki matuƙa, wanda ya fi gaban ambato,
9 t kuna samun ceton rayukanku, ta wurin sakamakon bangaskiyarku.
10 t Annabawan da suka yi annabci a kan alherin da zai zama naku, sun tsananta bin diddigi a kan wannan ceto, 11 t suna bincike ko wane ne, ko kuma wane lokaci ne, Ruhun Almasihu da yake a zuciyarsu yake ishara, sa'ad da ya yi faɗi a kan wuyar da Almasihu zai sha, da kuma ɗaukakar da take biye.
12 t An dai bayyana musu, cewa ba kansu suke bauta wa ba, ku suke bauta wa, a game da abubuwan da masu yi muku bishara, ta ikon Ruhu Mai Tsarki, wanda aka aiko daga sama suka samar da ku a yanzu. Su ne kuwa abubuwan da mala'iku suke ɗokin gani.Kira a Yi Zaman Tsarki
13 Don haka, sai ku yi ɗamara, ku natsu, ku sa zuciyarku sosai a kan alherin da zai zo muku a bayyanan Yesu Almasihu. 14 t Ku yi zaman 'ya'ya masu biyayya. Kada ku biye wa muguwar sha'awarku ta dā, ta lokacin jahilcinku. 15 t Amma da yake wanda ya kira ku mai tsarki ne, ku ma kanku sai ku zama tsarkaka a cikin dukan al'amuranku.
16 t Domin a rubuce yake cewa, “Sai ku zama tsarkaka domin ni mai tsarki ne.”
17 t Da yake kuna kiransa Uba a wajen addu'a, shi da yake yi wa kowa shari'a gwargwadon aikinsa, ba zaɓe, sai ku ƙarasa lokacin baƙuncinku, kuna tsoronsa. 18 t Domin kun sani an fanshe ku ne daga al'adunku na banza da wofi da kuka gāda, ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa da zinariya ba, 19 t sai dai da jinin nan mai daraja na Almasihu, kamar na ɗan rago marar naƙasa, marar tabo. 20 t An rigyasaninsa a kan haka, tun ba a halicci duniya ba, amma saboda ku ne aka bayyana shi a zamanin ƙarshe.
21 t To gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya ta da shi daga matattu, ya kuma ɗaukaka shi, domin bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.
22 t Da yake kun tsarkake ranku kuna yi wa gaskiya biyayya har kuna nuna sahihiyar ƙauna ga 'yan'uwa, sai ku himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya. 23 t Gama sāke haifuwarku aka yi, ba ta iri mai lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, wato, ta Maganar Allah rayayyiya dawwamammiya.
24 Domin
“Duk ɗan adam kamar ciyawa yake,
Duk darajarsa kamar furen ciyawa take,
Ciyawar takan bushe, furen yakan kaɗe,
25 t Maganar Ubangiji kuwa dawwamammiya ce,”
Ita ce maganar bishara da aka yi muku.
1 Peter 1
1 Peter, an apostle of Jesus Christ, to the elect who are sojourners of the Dispersion in Pontus, Galatia, Cappadocia, Asia, and Bithynia,2 according to the foreknowledge of God the Father, in sanctification of the Spirit, unto obedience and sprinkling of the blood of Jesus Christ: Grace to you and peace be multiplied.3 Blessed be the God and Father of our Lord Jesus Christ, who according to his great mercy begat us again unto a living hope by the resurrection of Jesus Christ from the dead,4 unto an inheritance incorruptible, and undefiled, and that fadeth not away, reserved in heaven for you,5 who by the power of God are guarded through faith unto a salvation ready to be revealed in the last time.6 Wherein ye greatly rejoice, though now for a little while, if need be, ye have been put to grief in manifold trials,7 that the proof of your faith, being more precious than gold that perisheth though it is proved by fire, may be found unto praise and glory and honor at the revelation of Jesus Christ:8 whom not having seen ye love; on whom, though now ye see him not, yet believing, ye rejoice greatly with joy unspeakable and full of glory:9 receiving the end of your faith, even the salvation of your souls.10 Concerning which salvation the prophets sought and searched diligently, who prophesied of the grace that should come unto you:11 searching what time or what manner of time the Spirit of Christ which was in them did point unto, when it testified beforehand the sufferings of Christ, and the glories that should follow them.12 To whom it was revealed, that not unto themselves, but unto you, did they minister these things, which now have been announced unto you through them that preached the gospel unto you by the Holy Spirit sent forth from heaven; which things angel desire to look into.13 Wherefore girding up the loins of your mind, be sober and set your hope perfectly on the grace that is to be brought unto you at the revelation of Jesus Christ;14 as children of obedience, not fashioning yourselves according to your former lusts in the time of your ignorance:15 but like as he who called you is holy, be ye yourselves also holy in all manner of living;16 because it is written, Ye shall be holy; for I am holy.17 And if ye call on him as Father, who without respect of persons judgeth according to each man’s work, pass the time of your sojourning in fear:18 knowing that ye were redeemed, not with corruptible things, with silver or gold, from your vain manner of life handed down from your fathers;19 but with precious blood, as of a lamb without spot, even the blood of Christ:20 who was foreknown indeed before the foundation of the world, but was manifested at the end of times for your sake,21 who through him are believers in God, that raised him from the dead, and gave him glory; so that your faith and hope might be in God.22 Seeing ye have purified your souls in your obedience to the truth unto unfeigned love of the brethren, love one another from the heart fervently:23 having been begotten again, not of corruptible seed, but of incorruptible, through the word of God, which liveth and abideth.24 For, All flesh is as grass, And all the glory thereof as the flower of grass. The grass withereth, and the flower falleth:25 But the word of the Lord abideth for ever. And this is the word of good tidings which was preached unto you.