1 BIT 2
Rayayyen Dutse da Kabila Tsattsarka
1 t Saboda haka, sai ku yar da kowace irin ƙeta, da ha'inci, da munafunci, da hassada, da kuma kowane irin kushe. 2 t Kamar jariri sabon haihuwa, ku yi marmarin shan madara marar gami mai ruhu, domin ku girma da shi, har ya kai ku ga samun ceto,
3 t in dai kun ɗanɗana alherin Ubangiji.
4 t Ku zo a gare shi, rayayyen dutsen nan, hakika abin ƙi ne a gun mutane, amma zaɓaɓɓe, ɗaukakakke a gun Allah. 5 t Ku kuma, kamar rayayyun duwatsu, bari a gina gida mai ruhu da ku, domin ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, da nufin ku miƙa hadayu na ruhu, abin karɓa ga Allah, ta wurin Yesu Almasihu,
6 t Domin a tabbace yake a Nassi cewa,
“Ga shi, na sa mafificin dutsen a gini a Sihiyona, zaɓaɓɓe, ɗaukakakke,
Duk mai gaskatawa da shi kuwa, ba zai kunyata ba.”
7 t A gare ku, ku da kuka ba da gaskiya kuwa, shi ɗaukakakke ne. Amma ga waɗanda suka ƙi gaskatawa, to,
“Dutsen da magina suka ƙi,
Shi ne ya zama mafificin dutsen gini,”
8 t Da kuma,
“Dutsen sa tuntuɓe,
Da fā na sa faɗuwa.”
Sun yi tuntuɓe ne da maganar, don sun ƙi biyayya da ita. Haka kuwa aka ƙaddaro musu.
9 t Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.
10 t Dā ba jama'a ɗaya kuke ba, amma a yanzu, ku jama'ar Allah ce. Dā ba ku sadu da jinƙansa ba, amma a yanzu kun sadu da shi.Ku yi Zaman Bayin Allah
11 t Ya ƙaunatattuna, ina roƙonku don ku baƙi ne, bare kuma, ku guje wa mugayen sha'awace-sha'awace na halin mutuntaka waɗanda suke yaƙi da zuciyarku.
12 t Ku yi halin yabo a cikin al'ummai, don duk sa'ad da suke kushenku, cewa ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah a ran da alheri ya sauko musu.
13 t Ku yi biyayya ga kowace hukumar mutane saboda Ubangiji, ko ga sarki, domin shi ne shugaba, 14 t ko kuwa ga mahukunta, domin su ne ya a'aika su hori mugaye, su kuma yabi masu kirki. 15 t Domin nufin Allah ne ku toshe jahilcin marasa azanci ta yin aiki nagari. 16 t Ku yi zaman 'yanci, sai dai kada ku fake a bayan 'yancin nan naku, ku yi mugunta. Amma ku yi zaman bayin Allah.
17 t Ku girmama kowa, ku ƙaunaci 'yan'uwa, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.Koyi da Wahalar Almasihu
18 t Ku barori, ku bi iyayen gidanku da matuƙar ladabi, ba sai na kirki da masu sanyin hali kaɗai ba, har ma da miskilai. 19 t Ai, abin karɓa ne, in saboda mutum yana sane da nufin Allah, ya jure wa wuyar da yake sha, ba da alhakinsa ba.
20 t To, ina abin taƙama don kun yi haƙuri in kun sha dūka a kan laifin da kuka yi? Amma, in kun yi aiki nagari kuka sha wuya a kansa, kuka kuma haƙura, to shi ne abin karɓa ga Allah.
21 t Domin a kan haka ne musamman aka kira ku. Gama Almasihu ma ya sha wuya dominku, ya bar muku gurbi ku bi hanyarsa. 22 t Bai taɓa yin laifi ba faufau, ba a kuwa taɓa jin yaudara a bakinsa ba. 23 t Da aka zage shi bai rama ba, da ya sha wuya kuma bai yi kashedi ba, sai dai ya dogara ga mai shari'ar adalci. 24 t Shi kansa ya ɗauke zunubanmu a jikinsa a kan gungume, domin mu yi zamanmu matattu ga zunubi, rayayyu kuma ga adalci. Da raunukansa ne aka warkar da ku. 25 t A dā kun ɓăce kamar tumaki, amma a yanzu kun dawo ga Makiyayi, wato mai kula da rayukanku.
1 Peter 2
1 Putting away therefore all wickedness, and all guile, and hypocrisies, and envies, and all evil speakings,2 as newborn babes, long for the spiritual milk which is without guile, that ye may grow thereby unto salvation;3 if ye have tasted that the Lord is gracious:4 unto whom coming, a living stone, rejected indeed of men, but with God elect, precious,5 ye also, as living stones, are built up a spiritual house, to be a holy priesthood, to offer up spiritual sacrifices, acceptable to God through Jesus Christ.6 Because it is contained in scripture, Behold, I lay in Zion a chief corner stone, elect, precious: And he that believeth on him shall not be put to shame.
7 For you therefore that believe is the preciousness: but for such as disbelieve, The stone which the builders rejected, The same was made the head of the corner;
8 and, A stone of stumbling, and a rock of offence; for they stumble at the word, being disobedient: whereunto also they were appointed.9 But ye are a elect race, a royal priesthood, a holy nation, a people for God’s own possession, that ye may show forth the excellencies of him who called you out of darkness into his marvellous light:10 who in time past were no people, but now are the people of God: who had not obtained mercy, but now have obtained mercy.11 Beloved, I beseech you as sojourners and pilgrims, to abstain from fleshly lust, which war against the soul;12 having your behavior seemly among the Gentiles; that, wherein they speak against you as evil-doers, they may by your good works, which they behold, glorify God in the day of visitation.13 Be subject to every ordinance of man for the Lord’s sake: whether to the king, as supreme;14 or unto governors, as sent by him for vengeance on evil-doers and for praise to them that do well.15 For so is the will of God, that by well-doing ye should put to silence the ignorance of foolish men:16 as free, and not using your freedom for a cloak of wickedness, but as bondservants of God.17 Honor all men. Love the brotherhood. Fear God. Honor the king.18 Servants, be in subjection to your masters with all fear; not only to the good and gentle, but also to the froward.19 For this is acceptable, if for conscience toward God a man endureth griefs, suffering wrongfully.20 For what glory is it, if, when ye sin, and are buffeted for it, ye shall take it patiently? but if, when ye do well, and suffer for it, ye shall take it patiently, this is acceptable with God.21 For hereunto were ye called: because Christ also suffered for you, leaving you an example, that ye should follow his steps:22 who did no sin, neither was guile found in his mouth:23 who, when he was reviled, reviled not again; when he suffered threatened not; but committed himself to him that judgeth righteously:24 who his own self bare our sins in his body upon the tree, that we, having died unto sins, might live unto righteousness; by whose stripes ye were healed.25 For ye were going astray like sheep; but are now returned unto the Shepherd and Bishop of your souls.