previous next

1 BIT 3

Hakkin Aure

1  t Haka kuma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, don ko waɗansunsu ba su bi maganar Allah ba, halin matansu yă shawo kansu, ba tare da wata magana ba, 2 don ganin tsarkakakken halinku da kuma ladabinku. 3 t Kada adonku ya zama na kwalliyar kitso, da kayan zinariya, ko tufafi masu ƙawa, 4 t sai dai ya zama na hali, da kuma kyan nan marar dushewa na tawali'u da natsuwa. Wannan kuwa abu ne mai martaba ƙwarai a gun Allah. 5 t Don dā ma haka tsarkakan mata masu dogara ga Allah suka yi ado, suka bi mazansu,

6 t kamar yadda Saratu ta bi Ibrahim, tana kiransa ubangijinta. Ku kuma 'ya'yanta ne muddin kuna aiki nagari, ba kwa yarda wani abu ya tsorata ku.

7  t Haka kuma, ku maza, ku yi zaman ɗa'a da matanku, kuna girmama su, da yake su ne raunana, gama ku abokan tarayya ne na Allah. Ku yi haka don kada wani abu ya hana ku yin addu'a tare.

Shan Wuya don Adalci


8  t Daga ƙarshe kuma dukanku ku haɗa hankulanku, ku zama masu juyayi, masu ƙaunar 'yan'uwa, masu tausayi, da kuma masu tawali'u. 9 t Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka, sai ku sa albarka. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka.

10 Domin,
“Duk mai so ya more wa zamansa na duniya da alheri,
Sai ya kame bakinsa daga ɓarna,
Ya kuma hana shi maganar yaudara.

11 Ya rabu da mugunta,
ya kama nagarta,
Ya himmantu ga zaman lafiya, ya kuma dimance ta.

12  t Gama Ubangiji yana lura da masu aikata adalci,
Yana kuma sauraron roƙonsu.
Amma Ubangiji yana gāba da masu aikata mugunta.”
13  t To, wa zai cuce ku in kun himmantu a kan abin da yake nagari? 14 t Amma ko da za ku sha wuya saboda aikata abin da yake daidai, ku masu albarka ne. Kada ku ji tsoronsu, kada kuma ku damu. 15 t Sai dai ku girmama Almasihu a zukatanku da hakikancewa, shi Ubangiji ne. Kullum ku zauna a shirye ku ba da amsa ga duk wanda ya tambaye ku dalilin begen nan naku, amma fa da tawali'u da bangirma. 16 t Ku kuma kasance da lamiri mai kyau, don in an zage ku, waɗanda suka kushe kyakkyawan halinku na bin Almasihu su kunyata. 17 t Zai fi kyau a sha wuya ga yin abin da yake nagari, in haka nufin Allah ne, da a sha don yin abin da ba daidai ba. 18 t Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba ƙari, domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci, domin ya kai mu ga Allah. An kashe shi a jiki, amma an rayar da shi a ruhu. 19 t Da ruhun ne kuma ya je ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku shela, 20 t wato, waɗanda dā ba su bi ba, sa'ad da Allah ya yi jira da haƙuri a zamanin Nuhu, a lokacin sassaƙar jirgin nan, wanda a cikinsa mutane kaɗan, wato takwas suka kuɓuta ta ruwa. 21 t Baftisma kuwa, wadda ita ce kwatancin wannan, ta cece ku a yanzu, ba ta fitar da dauɗa daga jiki ba, sai dai ta wurin roƙon Allah da lamiri mai kyau, ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu, 22 t wanda ya tafi Sama, yake dama ga Allah kuma, mala'iku da manyan mala'iku da masu iko suna binsa.

1 Peter 3

1 In like manner, ye wives, be in subjection to your own husbands; that, even if any obey not the word, they may without the word be gained by the behavior of their wives;2 beholding your chaste behavior coupled with fear.3 Whose adorning let it not be the outward adorning of braiding the hair, and of wearing jewels of gold, or of putting on apparel;4 but let it be the hidden man of the heart, in the incorruptible apparel of a meek and quiet spirit, which is in the sight of God of great price.5 For after this manner aforetime the holy women also, who hoped in God, adorned themselves, being in subjection to their own husbands:6 as Sarah obeyed Abraham, calling him lord: whose children ye now are, if ye do well, and are not put in fear by any terror.7 Ye husbands, in like manner, dwell with your wives according to knowledge, giving honor unto the woman, as unto the weaker vessel, as being also joint-heirs of the grace of life; to the end that your prayers be not hindered.8 Finally, be ye all likeminded, compassionate, loving as brethren, tenderhearted, humbleminded:9 not rendering evil for evil, or reviling for reviling; but contrariwise blessing; for hereunto were ye called, that ye should inherit a blessing.10 For, He that would love life, And see good days, Let him refrain his tongue from evil, And his lips that they speak no guile:

11 And let him turn away from evil, and do good; Let him seek peace, and pursue it.

12 For the eyes of the Lord are upon the righteous, And his ears unto their supplication: But the face of the Lord is upon them that do evil.

13 And who is he that will harm you, if ye be zealous of that which is good?14 But even if ye should suffer for righteousness’ sake, blessed are ye: and fear not their fear, neither be troubled;15 but sanctify in your hearts Christ as Lord: being ready always to give answer to every man that asketh you a reason concerning the hope that is in you, yet with meekness and fear:16 having a good conscience; that, wherein ye are spoken against, they may be put to shame who revile your good manner of life in Christ.17 For it is better, if the will of God should so will, that ye suffer for well-doing than for evil-doing.18 Because Christ also suffered for sins once, the righteous for the unrighteous, that he might bring us to God; being put to death in the flesh, but made alive in the spirit;19 in which also he went and preached unto the spirits in prison,20 that aforetime were disobedient, when the longsuffering of God waited in the days of Noah, while the ark was a preparing, wherein few, that is, eight souls, were saved through water:21 which also after a true likeness doth now save you, even baptism, not the putting away of the filth of the flesh, but the interrogation of a good conscience toward God, through the resurrection of Jesus Christ;22 who is on the right hand of God, having gone into heaven; angels and authorities and powers being made subject unto him.