1 BIT 4
Amintaccen Mai Riƙon Amanar Alherin Allah
1 Tun da yake Almasihu ya sha wuya a jiki dominmu, sai ku ma ku ɗauki irin wannan ra'ayi. Ai, duk wanda ya sha wuya a jiki, ya daina aikata zunubi ke nan, 2 t domin a nan gaba yă ƙarasa sauran zamansa na jiki ba tare da biye wa muguwar sha'awar zuciya ba, sai dai nufin Allah. 3 t Lalle zaman da kuka yi na dā, irin wanda al'ummai suke son yi, ya isa haka nan, wato zaman fajirci, da mugayen sha'awace-sha'awace, da buguwa, da shashanci, da shaye-shaye, da kuma bautar gumaka, abar ƙyama. 4 t Suna mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, kuna zarmewa, kuna aikata masha'a irin tasu, har suna zaginku. 5 t Amma lalle su ba da hujjojinsu ga wannan da yake a shirye ya yi wa rayayyu da matattu shari'a.
6 t Shi ya sa aka yi bishara har ga matattu ma, waɗanda ko da yake an yi musu hukunci a cikin jiki kamar mutane, su samu su rayu a ruhu kamar Allah.
7 t Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato. Saboda haka, sai ku kanku, ku natsu, domin ku yi addu'a. 8 t Fiye da kome kuma, ku himmantu ga ƙaunar juna, domin ƙauna takan yafe laifofi masu ɗumbun yawa. 9 t Ku riƙa yi wa juna baƙunta, ba tare da ƙunƙuni ba. 10 t Duk baiwar da mutum ya samu, yă yi amfani da ita ga kyautata wa ɗan'uwansa, a kan amintaccen mai riƙon amanar alherin Allah iri iri ne.
11 t Duk mai wa'azi yă dai san faɗar Allah yake yi. Duk mai yin hidima, yă yi da ƙarfin da Allah ya ba shi, domin a cikin al'amura duka a ɗaukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka da mulki sun tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!Shan Wuyar Kirista
12 t Ya ƙaunatattuna, kada ku yi mamakin matsananciyar wahalar da ta same ku a kan gwaji, kamar wani baƙon abu ne yake faruwa a gare ku. 13 t Amma, muddin kuna tarayya da Almasihu a wajen shan wuyarsa, sai ku yi farin ciki, domin sa'ad da aka bayyana ɗaukakarsa, ku yi farin ciki da murna matuƙa. 14 t Albarka ta tabbata a gare ku in ana zaginku saboda sunan Almasihu, don Ruhun ɗaukaka, wato Ruhun Allah yā tabbata a gare ku. 15 Sai dai kada shan wuyar ko ɗaya daga cikinku ya zama na horon laifin kisankai ne, ko na sata, ko na mugun aiki, ko kuma na shisshigi. 16 t Amma in wani ya sha wuya a kan shi Kirista ne, to, kada ya ji kunya, sai dai ya ɗaukaka Allah saboda wannan suna.
17 t Don lokaci ya yi da za a fara shari'a ta kan jama'ar Allah. In kuwa ta kanmu za a fara, to, me zai zama ƙarshen waɗanda ba su bi bisharar Allah ba?
18 t “In adali da ƙyar ya kuɓuta,
Me zai auku ga marar bin Allah da mai zunubi?”
19 Saboda haka, sai duk masu shan wuya bisa ga nufin Allah su danƙa ransu ga Mahalicci mai aminci suna aikata abin da yake daidai.
1 Peter 4
1 Forasmuch then as Christ suffered in the flesh, arm ye yourselves also with the same mind; for he that hath suffered in the flesh hath ceased from sin;2 that ye no longer should live the rest of your time in flesh to the lusts of men, but to the will of God.3 For the time past may suffice to have wrought the desire of the Gentiles, and to have walked in lasciviousness, lusts, winebibbings, revellings, carousings, and abominable idolatries:4 wherein they think it strange that ye run not with them into the same excess of riot, speaking evil of you:5 who shall give account to him that is ready to judge the living and the dead.6 For unto this end was the gospel preached even to the dead, that they might be judged indeed according to men in the flesh, but live according to God in the spirit.7 But the end of all things is at hand: be ye therefore of sound mind, and be sober unto prayer:8 above all things being fervent in your love among yourselves; for love covereth a multitude of sins:9 using hospitality one to another without murmuring:10 according as each hath received a gift, ministering it among yourselves, as good stewards of the manifold grace of God;11 if any man speaketh, speaking as it were oracles of God; is any man ministereth, ministering as of the strength which God supplieth: that in all things God may be glorified through Jesus Christ, whose is the glory and the dominion for ever and ever. Amen.12 Beloved, think it not strange concerning the fiery trial among you, which cometh upon you to prove you, as though a strange thing happened unto you:13 but insomuch as ye are partakers of Christ’s sufferings, rejoice; that at the revelation of his glory also ye may rejoice with exceeding joy.14 If ye are reproached for the name of Christ, blessed are ye; because the Spirit of glory and the Spirit of God resteth upon you.15 For let none of you suffer as a murderer, or a thief, or an evil-doer, or as a meddler in other men’s matters:16 but if a man suffer as a Christian, let him not be ashamed; but let him glorify God in this name.17 For the time is come for judgment to begin at the house of God: and if it begin first at us, what shall be the end of them that obey not the gospel of God?18 And if the righteous is scarcely saved, where shall the ungodly and sinner appear?19 Wherefore let them also that suffer according to the will of God commit their souls in well-doing unto a faithful Creator.