1 BIT 5
Ku Yi Kiwon Garken Allah
1 t Don haka, ku dattawan ikkilisiya da suke cikinku, ni da nike dattijon ikkilisiya, ɗan'uwanku, mashaidin shan wuyar Almasihu, mai samun rabo kuma a cikin ɗaukakar da za a bayyana, ina yi muku gargaɗi, 2 t ku yi kiwon garken Allah da yake tare da ku, ba a kan tilas ba, sai dai a kan yarda, ba ma don neman ribar banza ba, sai dai da himma. 3 t Kada ku nuna wa waɗanda suke hannunku iko, sai dai ku zama abin koyi ga garken nan. 4 t Sa'ad da kuma Sarkin Makiyaya ya bayyana, za ku sami kambin ɗaukaka marar dusashewa.
5 t Haka nan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikkilisiya. Dukanku ku yi wa kanku ɗamara da tawali'u, kuna bauta wa juna, gama “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana wa masu tawali'u alheri.”
6 t Don haka, sai dai ku ƙasƙantar da kanku ga maɗaukakin ikon Allah, domin ya ɗaukakaku a kan kari. 7 t Ku jibga masa dukan taraddadinku, domin yana kula da ku. 8 t Ku natsu, ku kuma zauna a faɗake. Magabcinku Iblis yana zazzāgawa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai lanƙwame. 9 t Ku yi tsayayya da shi, kuna dagewa a kan bangaskiyarku, da yake kun san 'yan'uwanku a duniya duka an ɗora musu irin wannan shan wuya. 10 t Bayan kun sha wuya kuma ta ɗan lokaci kaɗan, Allah mai alheri duka, wanda ya kira ku ga samun madawwamiyar ɗaukakarsa a cikin Almasihu, shi kansa zai kammala ku, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku.
11 t Mulki yā tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!Gaisuwa
12 t Na rubuto muku wasiƙar nan a taƙaice ta hannun Sila, ɗan'uwa mai aminci, a yadda na ɗauke shi, domin in yi muku gargaɗi, in kuma sanar da ku, cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske, ku tsaya a gare shi da ƙarfi. 13 t Ita da take a Babila, wadda ita ma zaɓaɓɓiya ce, ta aiko muku da gaisuwa. Haka kuma, ɗana, Markus.
14 t Ku gai da juna da sumbar ƙauna.
Salama tă tabbata a gare ku duka, ku na Almasihu.
1 Peter 5
1 The elders among you I exhort, who am a fellow-elder, and a witness of the sufferings of Christ, who am also a partaker of the glory that shall be revealed:2 Tend the flock of God which is among you, exercising the oversight, not of constraint, but willingly, according to the will of God; nor yet for filthy lucre, but of a ready mind;3 neither as lording it over the charge allotted to you, but making yourselves ensamples to the flock.4 And when the chief Shepherd shall be manifested, ye shall receive the crown of glory that fadeth not away.5 Likewise, ye younger, be subject unto the elder. Yea, all of you gird yourselves with humility, to serve one another: for God resisteth the proud, but giveth grace to the humble.6 Humble yourselves therefore under the mighty hand of God, that he may exalt you in due time;7 casting all your anxiety upon him, because he careth for you.8 Be sober, be watchful: your adversary the devil, as a roaring lion, walketh about, seeking whom he may devour,9 whom withstand stedfast in your faith, knowing that the same sufferings are accomplished in your brethren who are in the world.10 And the God of all grace, who called you unto his eternal glory in Christ, after that ye have suffered a little while, shall himself perfect, establish, strengthen you.11 To him be the dominion for ever and ever. Amen.12 By Silvanus, our faithful brother, as I account him, I have written unto you briefly, exhorting, and testifying that this is the true grace of God. Stand ye fast therein.13 She that is in Babylon, elect together with you, saluteth you; and so doth Mark my son.14 Salute one another with a kiss of love. Peace be unto you all that are in Christ.