previous next

1 TAS 5

Ku Zauna a Faɗake don Zuwan Ubangiji

1  t Amma ga zancen ainihin lokaci ko rana, ba lalle sai an rubuto muku kome ba. 2 t Domin ku da kanku kun sani sarai, ranar Ubangiji za ta zo ne kamar ɓarawo da dare. 3 Lokacin da mutane suke cewa, “Muna zaman salama da zaman lafiya,” wuf; sai halaka ta auko musu, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba kuwa hanyar tsira. 4 t Amma, ai, ba a cikin duhu kuke ba, 'yan'uwa, har da ranar nan za ta mamaye ku kamar ɓarawo. 5 Domin duk mutanen haske kuke, na rana kuma. Mu ba na dare ko na duhu ba ne. 6 t Ashe, saboda haka kada mu yi barci yadda waɗansu suke yi, sai dai mu zauna a faɗake, da natsuwa. 7 t Don masu barci da daddare suke barci, masu sha su bugu ma da daddare suke sha su bugu. 8 t Amma da yake mu na rana ne, sai mu natsu, muna saye da sulken bangaskiya da ƙauna, muna begen samun ceto, shi ne kuma kwalkwakinmu. 9 t Allah bai ƙaddara mu ga fushinsa ba, sai dai ga samun ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, 10 t wanda ya mutu saboda mu, domin ko muna a raye, ko muna barci, mu zama muna tare da shi.

11 Saboda haka, sai ku ƙarfafa wa juna zuciya, kuna riƙa inganta juna, kamar dai yadda kuke yi.

Gargaɗi da kuma Gaisuwa


12  t Amma muna roƙonku 'yan'uwa, ku girmama masu fama da aiki a cikinku, wato waɗanda suke shugabanninku cikin Ubangiji, suke kuma yi muku gargaɗi. 13 t Ku riƙe su da mutunci ƙwarai game da ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna. 14 t Muna kuma yi muku gargaɗi, 'yan'uwa, ku tsawata wa malalata, ku ƙarfafa masu rarraunar zuciya, ku taimaki marasa tsayayyiyar zuciya, ku yi haƙuri da kowa da kowa. 15 t Ku lura fa, kada kowa ya rama mugunta da mugunta. Sai dai kullum ku nace yi wa juna aiki nagari, da kuma dukkan mutane. 16 t Ku riƙa yin farin ciki a kullum. 17 Ku riƙa yin addu'a ba fāsawa. 18 Ku godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu. 19 t Kada ku danne maganar Ruhu. 20 t Kada ku raina annabci, 21 t sai dai ku jarraba kome, ku riƙi abin da yake nagari kankan.

22 Ku yi nesa da kowace irin mugunta.
23  t Allah kansa, mai zartar da salama, yă tsarkake ku sarai, ya kuma kiyaye ruhunku da ranku da jikinku ƙalau, ku kasance marasa abin zargi a ranar komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

24 t Wanda yake kiranku ɗin nan mai alkawari ne, zai kuwa zartar.

25  t Ya ku 'yan'uwa, ku yi mana addu'a.

26  t Ku gai da dukkan 'yan'uwa da tsattsarkar sumba.

27  t Na gama ku da Ubangiji, a karanta wa dukkan 'yan'uwa wasiƙar nan.
28  t Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku.

1 Thessalonians 5

1 But concerning the times and the seasons, brethren, ye have no need that aught be written unto you.2 For yourselves know perfectly that the day of the Lord so cometh as a thief in the night.3 When they are saying, Peace and safety, then sudden destruction cometh upon them, as travail upon a woman with child; and they shall in no wise escape.4 But ye, brethren, are not in darkness, that that day should overtake you as a thief:5 for ye are all sons of light, and sons of the day: we are not of the night, nor of darkness;6 so then let us not sleep, as do the rest, but let us watch and be sober.7 For they that sleep sleep in the night: and they that are drunken are drunken in the night.8 But let us, since we are of the day, be sober, putting on the breastplate of faith and love; and for a helmet, the hope of salvation.9 For God appointed us not into wrath, but unto the obtaining of salvation through our Lord Jesus Christ,10 who died for us, that, whether we wake or sleep, we should live together with him.11 Wherefore exhort one another, and build each other up, even as also ye do.12 But we beseech you, brethren, to know them that labor among you, and are over you in the Lord, and admonish you;13 and to esteem them exceeding highly in love for their work’s sake. Be at peace among yourselves.14 And we exhort you, brethren, admonish the disorderly, encourage the fainthearted, support the weak, be longsuffering toward all.15 See that none render unto any one evil for evil; but always follow after that which is good, one toward another, and toward all.16 Rejoice always;17 pray without ceasing;18 in everything give thanks: for this is the will of God in Christ Jesus to you-ward.19 Quench not the Spirit;20 despise not prophesyings;21 prove all things; hold fast that which is good;22 abstain from every form of evil.23 And the God of peace himself sanctify you wholly; and may your spirit and soul and body be preserved entire, without blame at the coming of our Lord Jesus Christ.24 Faithful is he that calleth you, who will also do it.25 Brethren, pray for us.26 Salute all the brethren with a holy kiss.27 I adjure you by the Lord that this epistle be read unto all the brethren.28 The grace of our Lord Jesus Christ be with you.