previous next

1 TIM 4

Faɗi a kan Malaman Ƙarya

1  t To, Ruhu musamman ya ce, a can wani zamani waɗansu za su fanɗare wa bangaskiya, su mai da hankali ga aljannu masu ruɗi, da kuma koyarwar aljannu, 2 t ta wurin makircin waɗansu maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu lalas. 3 t Su ne masu hana aure da cin abinci iri iri, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka ba da gaskiya, suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya. 4 t Domin duk abin da Allah ya halitta kyakkyawa ne, kada kuma a ƙi kome muddin an karɓe shi da godiya,

5 gama an tsarkake shi ta wurin Maganar Allah da addu'a

Amintaccen Bawan Almasihu


6  t In kana tuna wa 'yan'uwa wadannan abubuwa, za ka zama amintaccen bawan Almasihu Yesu, wanda aka goya da maganar bangaskiya, da kuma sahihiyar koyarwar nan wadda ka bi har ya zuwa yau. 7 t Ka ƙi tatsuniyoyin saɓo da na banza da wofi. Ka hori kanka ga bin Allah. 8 t Horon jiki yana da ɗan amfaninsa, amma bin Allah yana da amfani ta kowace hanya, da yake shi ne da alkawarin rai na a yanzu da na nan gaba. 9 t Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum.

10 Saboda wannan maƙasudi muke wahala, muke ta fama, domin mun dogara ne ga Allah Rayayye, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman masu ba da gaskiya.
11  t Ka yi umarni da waɗannan abubuwa, ka kuma koyar da su. 12 t Kada ka yarda kowa yă raina ƙuruciyarka, sai dai ka zama gurbi ga masu ba da gaskiya ta wurin magana, da hali, da ƙauna, da bangaskiya, da kuma tsarkaka. 13 Kafin in zo, ka lazamci karanta wa mutane Littattafai, da yin gargaɗi, da kuma koyarwa. 14 t Kada ka shagala da baiwar da aka yi maka, wadda aka ba ka ta wurin annabci, sa'ad da dattawan ikkilisiya suka ɗora maka hannu. 15 Ka himmantu ga waɗannan abubuwa, ka kuma lazamce su ƙwarai, don kowa yă ga ci gaban da kake yi. 16 Ka kula da kanka da kuma koyarwarka. Ka nace da haka, domin ta yin haka za ka ceci kanka da masu sauraronka.

1 Timothy 4

1 But the Spirit saith expressly, that in later times some shall fall away from the faith, giving heed to seducing spirits and doctrines of demons,2 through the hypocrisy of men that speak lies, branded in their own conscience as with a hot iron;3 forbidding to marry, and commanding to abstain from meats, which God created to be received with thanksgiving by them that believe and know the truth.4 For every creature of God is good, and nothing is to be rejected, if it be received with thanksgiving:5 for it is sanctified through the word of God and prayer.6 If thou put the brethren in mind of these things, thou shalt be a good minister of Christ Jesus, nourished in the words of the faith, and of the good doctrine which thou hast followed until now:7 but refuse profane and old wives’ fables. And exercise thyself unto godliness:8 for bodily exercise is profitable for a little; but godliness is profitable for all things, having promise of the life which now is, and of that which is to come.9 Faithful is the saying, and worthy of all acceptation.10 For to this end we labor and strive, because we have our hope set on the living God, who is the Saviour of all men, specially of them that believe.11 These things command and teach.12 Let no man despise thy youth; but be thou an ensample to them that believe, in word, in manner of life, in love, in faith, in purity.13 Till I come, give heed to reading, to exhortation, to teaching.14 Neglect not the gift that is in thee, which was given thee by prophecy, with the laying on of the hands of the presbytery.15 Be diligent in these things; give thyself wholly to them; that thy progress may be manifest unto all.16 Take heed to thyself, and to thy teaching. Continue in these things; for in doing this thou shalt save both thyself and them that hear thee.