2 KOR 1
Gaisuwa
1 t Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, da kuma ɗan'uwanmu Timoti, zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Koranti, tare da dukan tsarkaka na duk ƙasar Akaya.
2 t Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.Godiyar Bulus Bayan Shan Wuya
3 t Godiya ta tabbata a gare shi, shi wanda yake Allah, da Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uba mai yawan jinƙai, Allah na dukan ta'aziyya, 4 t shi da yake yi mana ta'aziyya a dukan wahalarmu, domin mu kuma mu iya ta'azantar da masu shan kowace irin wahala, da ta'aziyyar nan da mu ma muka samu a gun Allah. 5 t Domin kuwa kamar yadda muke shan wuya ƙwarai, irin wadda Almasihu ya sha, haka kuma ake yi mana ta'aziyya ƙwarai, ta wurin Almasihu. 6 t Ko ana wahalshe mu ma, ai, saboda ta'azantuwarku ce, da kuma lafiyarku. Ko ana ta'azantar da mu, ai, saboda ta'azantuwarku ce, wadda take sa ku, ku jure wa irin wuyan nan, da muke sha.
7 t Sa zuciyarmu a kanku ƙaƙƙarfa ce, domin mun sani, kamar yadda kuka yi tarayya da mu a cikin shan wuya, haka kuma, za ku yi tarayya a cikin ta'aziyyar.
8 t 'Yan'uwa, ba ma so ku jahilta da wahalar da muka sha a ƙasar Asiya, domin kuwa mun ji jiki ƙwarai da gaske, har abin ya fi ƙarfinmu, har ma muka fid da tsammanin rayuwa. 9 t Har ma muka ji kamar hukuncin kisa aka yi mana, wannan kuwa don kada mu dogara ga kanmu ne, sai dai ga Allah, mai ta da matattu. 10 t Shi ne ya kuɓutar da mu daga muguwar mutuwa a fili, zai kuwa kuɓutar da mu, ga shi kuma muke dogara yă kuɓutar da mu har ila yau.
11 t Ku ma sai ku taimake mu da addu'a, domin mutane da yawa su gode wa Allah, ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu'o'i masu yawa.Bulus Ya Dakatar da Ziyararsa
12 t Fariyarmu ke nan, lamirinmu yana ba da shaida, cewa mun yi zaman tsarki a duniya da zuciya ɗaya, tsakani da Allah, tun ba ma a gare ku ba, ba bisa ga wayo irin na ɗan adam ba, sai dai bisa ga alherin Allah. 13 Domin wasiƙarmu zuwa gare ku, ba ta ƙunshi wani abu dabam ba, sai dai ainihin abin da kuka karanta kuka kuma fahimta, ina kuwa fata ku fahimta sosai da sosai,
14 t kamar yadda kuka riga kuka ɗan fahimce mu, cewa kwa iya yin fāriya da mu, kamar yadda mu ma za mu iya yi da ku, a ranar Ubangijinmu Yesu.
15 t Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu. 16 t Wato niyyata in bi a kanku in za ni Makidoniya, in kuma komo wurinku daga Makidoniya, sa'an nan ku yi mini rakiya in zan tafi Yahudiya. 17 t Ashe, a lokacin da na yi niyyar yin haka, wato na nuna rashin tsai da zuciya ke nan? Ko kuwa shiririta nake yi kawai irin ta halin mutuntaka, in ce, “I” in koma in ce, “A'a”? 18 t Yadda ba shakka Allah yake mai alkawari, haka ma maganar da muka yi muku, ba shiririta a ciki. 19 t Domin kuwa, Ɗan Allah, Yesu Almasihu, wanda ni, da Sila, da Timoti muka yi muku wa'azi, ai, ba shiririta a game da shi, har kullum a kan gaskiya yake. 20 t Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi take, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah. 21 t Domin kuwa, Allah shi ne mai tabbatar da mu da ku gaba ɗaya ga Almasihu, shi ne wanda ya shafe mu kuma.
22 t Ya buga mana hatiminsa cewa mu nasa ne, ya kuma yi mana baiwa da Ruhunsa a zukatanmu, domin tabbatar da abin da zai yi a nan gaba.
23 t Labudda, Allah shi ne mashaidina a kan cewa, musamman don sawwaƙe muku ne, na fāsa zuwa Koranti. 24 t Ba cewa muna nuna muku iko a kan bangaskiyarku ba ne, a'a, sai dai muna aiki tare ne, domin ku yi farin ciki, domin a game da bangaskiyarmu kam, kuna tsaye kankan.
2 Corinthians 1
1 Paul, an apostle of Christ Jesus through the will of God, and Timothy our brother, unto the church of God which is at Corinth, with all the saints that are in the whole of Achaia:2 Grace to you and peace from God our Father and the Lord Jesus Christ.3 Blessed be the God and Father of our Lord Jesus Christ, the Father of mercies and God of all comfort;4 who comforteth us in all our affliction, that we may be able to comfort them that are in any affliction, through the comfort wherewith we ourselves are comforted of God.5 For as the sufferings of Christ abound unto us, even so our comfort also aboundeth through Christ.6 But whether we are afflicted, it is for your comfort and salvation; or whether we are comforted, it is for your comfort, which worketh in the patient enduring of the same sufferings which we also suffer:7 and our hope for you is stedfast; knowing that, as ye are partakers of the sufferings, so also are ye of the comfort.8 For we would not have you ignorant, brethren, concerning our affliction which befell us in Asia, that we were weighed down exceedingly, beyond our power, insomuch that we despaired even of life:9 yea, we ourselves have had the sentence of death within ourselves, that we should not trust in ourselves, but in God who raiseth the dead:10 who delivered us out of so great a death, and will deliver: on whom we have set our hope that he will also still deliver us;11 ye also helping together on our behalf by your supplication; that, for the gift bestowed upon us by means of many, thanks may be given by many persons on our behalf.12 For our glorifying is this, the testimony of our conscience, that in holiness and sincerity of God, not in fleshly wisdom but in the grace of God, we behaved ourselves in the world, and more abundantly to you-ward.13 For we write no other things unto you, than what ye read or even acknowledge, and I hope ye will acknowledge unto the end:14 as also ye did acknowledge us in part, that we are your glorying, even as ye also are ours, in the day of our Lord Jesus.15 And in this confidence I was minded to come first unto you, that ye might have a second benefit;16 and by you to pass into Macedonia, and again from Macedonia to come unto you, and of you to be set forward on my journey unto Judaea.17 When I therefore was thus minded, did I show fickleness? or the things that I purpose, do I purpose according to the flesh, that with me there should be the yea yea and the nay nay?18 But as God is faithful, our word toward you is not yea and nay.19 For the Son of God, Jesus Christ, who was preached among you by us, even by me and Silvanus and Timothy, was not yea and nay, but in him is yea.20 For how many soever be the promises of God, in him is the yea: wherefore also through him is the Amen, unto the glory of God through us.21 Now he that establisheth us with you in Christ, and anointed us, is God;22 who also sealed us, and gave us the earnest of the Spirit in our hearts.23 But I call God for a witness upon my soul, that to spare you I forbare to come unto Corinth.24 Not that we have lordship over your faith, but are helpers of your joy: for in faith ye stand fast.