previous next

2 KOR 10

Bulus Ya Ƙare Aikinsa

1  t Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali'u da sanyin hali na Almasihu, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” ne a cikinku, amma “mai matsawa” ne sa'ad da nake rabe da ku, 2 t ina roƙonku kada ku tilasta ni in matsa muku sa'ad da na zo, gama na tabbata zan iya tsaya wa waɗanda suka ce abin da muke yi sha'anin duniya ne. 3 Ko da yake a cikin jiki muke tafiya, famarmu ba irin na mutuntaka ba ne. 4 t Don kuwa makamanmu na fama ba na mutuntaka ba ne, na ikon Allah ne, masu rushe maƙamai masu ƙarfi. 5 t Muna ka da masu hujjoji a cikin zace-zacensu, muna rushe kowace ganuwar alfarma mai tare sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Almasihu.

6 t A shirye muke kuma mu hori kowane marar biyayya, muddin biyayyarku ta tabbata.
7  t Ku dubi abin da yake bayyane mana! in dai wani ya amince na Almasihu ne, to, ya ƙara tunawa, wato kamar yadda yake shi na Almasihu ne, mu ma haka muke. 8 t Ko da zan yi gadara fiye da kima a game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba zan kunyata ba. 9 Kada fa a ga kamar ina tsorata ku da wasiƙu ne. 10 t Don waɗansu suna cewa, “Wasiƙunsa masu ratsa jiki ne, masu ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi ba shi da kwarjini, maganarsa kuma ba wata magana ba ce.” 11 Irin mutanen nan dai su fahimci yadda abin da muke faɗa a cikin wasiƙa sa'ad da ba ma nan, shi muke aikatawa sa'ad da muke nan.

12 t Wane mu mu daidaita kanmu, ko mu gwada kanmu da waɗansu masu yabon kansu! Ashe, waɗannan mutane masu auna kansu da juna, suna kuma neman bambanci a tsakaninsu da juna, ba su da basira.
13  t Amma dai ba za mu yi alfarma fiye da yadda ya kamata ba, sai dai mu tsaya a kan iyakar da Allah ya yanke mana, wadda ta game har da ku. 14 t Ai, ba mu wuce gona da iri ba, kamar ba a hannunmu kuke ba, domin mu ne muka fara shan nisa, muka je a gare ku da bisharar Almasihu. 15 t Fahariyarmu ba fiye da yadda ya kamata take ba, ba ta kuma shafi aikin waɗansu ba. Amma muna sa zuciya bangaskiyarku ta riƙa ƙaruwa, ta haka kuma fagen aikinmu a cikinku ya riƙa ƙaruwa ƙwarai da gaske, 16 t har ma mu samu mu yi bishara a ƙasashen da suke a gaba da ku, ba tare da wata fahariya da aikin da wani ya riga ya yi a fagensa ba. 17 t Amma, “Duk mai yin fahariya, ya yi fahariya da Ubangiji.” 18 t Ai, ba mai yabon kansa ake yarda da shi ba, sai dai wanda Ubangiji ya yaba wa.

2 Corinthians 10

1 Now I Paul myself entreat you by the meekness and gentleness of Christ, I who in your presence am lowly among you, but being absent am of good courage toward you:2 yea, I beseech you, that I may not when present show courage with the confidence wherewith I count to be bold against some, who count of us as if we walked according to the flesh.3 For though we walk in the flesh, we do not war according to the flesh4 (for the weapons of our warfare are not of the flesh, but mighty before God to the casting down of strongholds),5 casting down imaginations, and every high thing that is exalted against the knowledge of God, and bringing every thought into captivity to the obedience of Christ;6 and being in readiness to avenge all disobedience, when your obedience shall be made full.7 Ye look at the things that are before your face. If any man trusteth in himself that he is Christ’s, let him consider this again with himself, that, even as he is Christ’s, so also are we.8 For though I should glory somewhat abundantly concerning our authority (which the Lord gave for building you up, and not for casting you down), I shall not be put to shame:9 that I may not seem as if I would terrify you by my letters.10 For, His letters, they say, are weighty and strong; but his bodily presence is weak, and his speech of no account.11 Let such a one reckon this, that, what we are in word by letters when we are absent, such are we also in deed when we are present.12 For we are not bold to number or compare ourselves with certain of them that commend themselves: but they themselves, measuring themselves by themselves, and comparing themselves with themselves, are without understanding.13 But we will not glory beyond our measure, but according to the measure of the province which God apportioned to us as a measure, to reach even unto you.14 For we stretch not ourselves overmuch, as though we reached not unto you: for we came even as far as unto you in the gospel of Christ:15 not glorying beyond our measure, that is, in other men’s labors; but having hope that, as your faith groweth, we shall be magnified in you according to our province unto further abundance,16 so as to preach the gospel even unto the parts beyond you, and not to glory in another’s province in regard of things ready to our hand.17 But he that glorieth, let him glory in the Lord.18 For not he that commendeth himself is approved, but whom the Lord commendeth.