2 KOR 12
Wahayan Bulus da Bayani Iri Iri
1 t An tilasta mini ne in yi gadara, ko da yake ba ta amfane ni da kome ba. Amma zan ci gaba da zancen ruya da wahayi da Ubangiji ya yi mini. 2 t Na san wani mutum wanda yau shekara goma sha huɗu ke nan, aka ɗauke shi zuwa Sama ta uku bisa ga ikon Almasihu, ko yana a cikin jiki ne, ko ba a cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ne masani. 3 Na kuma san mutumin nan, an ɗauke shi zuwa Firdausi, ko yana a cikin jiki ne, ko ba a cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ne masani, 4 t ya kuma ji waɗansu maganganu, waɗanda ba dama a faɗa, irin ma waɗanda ɗan adam ba shi da izinin faɗa. 5 Zan yi gadara da mutumin nan kam, amma ba zan yi gadara da kaina ba, sai dai ko da raunanata. 6 t Ko da zan so yin gadara ma, ba zan zama wawa ba, gama gaskiya zan faɗa. Amma na bar zancen haka, don kada wani ya ɗauke ni fiye da yadda yake ganina, ko yadda yake jin maganata. 7 t Don kada kaina yă kumbura kuma saboda mafifitan wahayan da aka yi mini, sai aka saka mini wata cuta, wadda ta zama mini ƙaya, jakadan Shaiɗan, don yă riƙa wahalshe ni, don kada kaina ya kumbura. 8 t Sau uku nake roƙon Ubangiji a kan wannan abu ya rabu da ni, 9 t amma ya ce mini, “Alherina yā isa, domin ta wajen rashin ƙarfi ake ganin cikar ikona.” Saboda haka sai ma in ƙara yin alfarma da raunanata da farinciki fiye da na da, domin ikon Almasihu ya zauna a tare da ni.
10 t Saboda haka, ina murna da raunanata, da cin mutuncin da ake yi mini, da shan wuya, da shan tsanani, da masifu saboda Almasihu, don sa'ad da nake rarrauna, a sa'an nan ne nake da ƙarfi.Alhinin Bulus a kan Ikkilisiyar Koranti
11 t Na yi wauta kam, amma ku ne kuke tilasta mini, ku ne kuwa ya kamata ku yaba mini, domin ba inda na kasa waɗannan mafifitan manzanni, ko da yake ni ba kome ba ne. 12 t An gudanar da tabbatattun alamun manzo a cikinku ta matuƙar jimiri, da alamu da abubuwan al'ajabi da mu'ujizai.
13 t Ta wace hanya ce kuka kasa sauran ikkilisiyoyi? Ko kuwa domin dai ni ban nauyaya muku ba? To, ku yafe mini wannan laifi!
14 t Ga shi, na yi shirin zuwa wurinku, zuwa na uku, ba kuwa zan nauyaya muku ba, don ba abinku nake nema ba, ku nake nema, domin ba yara ne da ɗaukar nauyin iyayensu ba, sai dai iyaye ne da ɗaukar nauyin yaran. 15 t Ni kam, zan kashe dukan abin hannuna da dukan zarafina da matuƙar farin ciki saboda ranku. In na ƙara ƙaunarku, ashe, sai a rage ƙaunata? 16 t To, a ce ban nauyaya muku ba ɗin, ashe, sai ku ce dabara na yi muku, na shawo kanku ta hanyar yaudara! 17 Na cuce ku ne ta wurin wani daga cikin waɗanda na aiko a gare ku?
18 t Na roƙi Titus ya je, na kuma aiko ɗan'uwan nan tare da shi. To, Titus ya cuce ku ne? Ashe, ba Ruhu ɗaya yake bi da mu ba, ni da shi? Ba kuma hanya ɗaya muke bi ba?
19 t Ashe, tun dā tsammani kuke yi muna kawo hanzarinmu a gare ku ne? A'a, a gaban Allah muke magana, muna na Almasihu, wannan kuwa duk domin inganta ku ne, ya ku ƙaunatattu. 20 t Ina tsoro kada watakila in na zo in same ku ba a yadda nake so ba, ku kuma ku gan ni ba a yadda kuke so ba, ko ma a tarar da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da yanke, da tsegunguma, da girmankai, da tashin hankali. 21 t Ina tsoro kada in na sāke zuwa, Allahna ya ƙasƙanta ni a gabanku, in kuma yi baƙin ciki saboda waɗansu da yawa da suka yi zunubi a dā, ba su kuwa tuba da aikinsu na lalata ba, da fasikancinsu, da fajircinsu da suka aikata.
2 Corinthians 12
1 I must needs glory, though it is not expedient; but I will come to visions and revelations of the Lord.2 I know a man in Christ, fourteen years ago (whether in the body, I know not; or whether out of the body, I know not; God knoweth), such a one caught up even to the third heaven.3 And I know such a man (whether in the body, or apart from the body, I know not; God knoweth),4 how that he was caught up into Paradise, and heard unspeakable words, which it is not lawful for a man to utter.5 On behalf of such a one will I glory: but on mine own behalf I will not glory, save in my weaknesses.6 For if I should desire to glory, I shall not be foolish; for I shall speak the truth: but I forbear, lest any man should account of me above that which he seeth me to be, or heareth from me.7 And by reason of the exceeding greatness of the revelations, that I should not be exalted overmuch, there was given to me a thorn in the flesh, a messenger of Satan to buffet me, that I should not be exalted overmuch.8 Concerning this thing I besought the Lord thrice, that it might depart from me.9 And he hath said unto me, My grace is sufficient for thee: for my power is made perfect in weakness. Most gladly therefore will I rather glory in my weaknesses, that the power of Christ may rest upon me.10 Wherefore I take pleasure in weaknesses, in injuries, in necessities, in persecutions, in distresses, for Christ’s sake: for when I am weak, then am I strong.11 I am become foolish: ye compelled me; for I ought to have been commended of you: for in nothing was I behind the very chiefest apostles, though I am nothing.12 Truly the signs of an apostle were wrought among you in all patience, by signs and wonders and mighty works.13 For what is there wherein ye were made inferior to the rest of the churches, except it be that I myself was not a burden to you? forgive me this wrong.14 Behold, this is the third time I am ready to come to you; and I will not be a burden to you: for I seek not yours, but you: for the children ought not to lay up for the parents, but the parents for the children.15 And I will most gladly spend and be spent for your souls. If I love you more abundantly, am I loved the less?16 But be it so, I did not myself burden you; but, being crafty, I caught you with guile.17 Did I take advantage of you by any one of them whom I have sent unto you?18 I exhorted Titus, and I sent the brother with him. Did Titus take any advantage of you? walked we not in the same spirit? walked we not in the same steps?19 Ye think all this time that we are excusing ourselves unto you. In the sight of God speak we in Christ. But all things, beloved, are for your edifying.20 For I fear, lest by any means, when I come, I should find you not such as I would, and should myself be found of you such as ye would not; lest by any means there should be strife, jealousy, wraths, factions, backbitings, whisperings, swellings, tumults;21 lest again when I come my God should humble me before you, and I should mourn for many of them that have sinned heretofore, and repented not of the uncleanness and fornication and lasciviousness which they committed.