2 KOR 13
Kashedi da Gaisuwa
1 t Wannan shi ne zai zama zuwana na uku a gare ku. Lalle ne kuwa a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku. 2 t Na gargaɗi waɗanda suka yi zunubi a dā, da kuma saura duka, a yanzu kuma da ba na nan ina yi musu gargaɗi, kamar yadda na yi sa'ad da nake nan a zuwana na biyu, cewa in na sāke zuwa ba zan sawwaƙe musu ba. 3 t In dai nema kuke yi ku tabbata, cewa da izinin Almasihu nake magana, to, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku.
4 t Ko da yake an gicciye shi ne da rashin ƙarfi, duk da haka a raye yake ta ikon Allah. Mu ma marasa ƙarfi ne kamarsa, amma a game da al'amuranku da za mu zartar, a raye muke tare da shi, ta ikon Allah.
5 t Ku jarraba kanku ku gani, ko har yanzu kuna a raye da bangaskiya. Ku riƙa auna kanku. Ashe, ba ku tabbata Almasihu yana a cikinku ba? Sai ko in kun kasa ga gwajin! 6 Muna fata ku gane, mu ba mu kāsa ba. 7 Amma muna roƙon Allah kada ku yi wani mugun abu, ba don mu mu zama kamar mun ci gwajin kawai ba, sai dai domin ku yi abin da yake daidai, ko da yake za ku ga kamar mun kāsa. 8 Domin ba dama mu sāɓa wa gaskiya, sai dai mu bi bayan gaskiyar. 9 t Gama farin ciki muke yi in muna raunana, ku kuna ƙarfafa. Addu'armu ita ce ku kammala.
10 t Ina rubuta wannan ne sa'ad da ba na tare da ku, domin sa'ad da na zo, kada ya zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.
11 t Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, sai wata rana. Ku kammala halinku. Ku kula da roƙona, ku yi zaman lafiya da juna, ku yi zaman salama, Allah mai zartar da ƙauna da salama kuwa zai kasance a tare da ku. 12 t Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba.
13 t Dukan tsarkaka suna gaishe ku.
14 t Alherin Ubangiji Yesu Almasihu, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su tabbata a gare ku duka.
2 Corinthians 13
1 This is the third time I am coming to you. At the mouth of two witnesses or three shall every word established.2 I have said beforehand, and I do say beforehand, as when I was present the second time, so now, being absent, to them that have sinned heretofore, and to all the rest, that, if I come again, I will not spare;3 seeing that ye seek a proof of Christ that speaketh in me; who to you-ward is not weak, but is powerful in you:4 for he was crucified through weakness, yet he liveth through the power of God. For we also are weak in him, but we shall live with him through the power of God toward you.5 Try your own selves, whether ye are in the faith; prove your own selves. Or know ye not as to your own selves, that Jesus Christ is in you? unless indeed ye be reprobate.6 But I hope that ye shall know that we are not reprobate.7 Now we pray to God that ye do no evil; not that we may appear approved, but that ye may do that which is honorable, though we be as reprobate.8 For we can do nothing against the truth, but for the truth.9 For we rejoice, when we are weak, and ye are strong: this we also pray for, even your perfecting.10 For this cause I write these things while absent, that I may not when present deal sharply, according to the authority which the Lord gave me for building up, and not for casting down.11 Finally, brethren, farewell. Be perfected; be comforted; be of the same mind; live in peace: and the God of love and peace shall be with you.12 Salute one another with a holy kiss.13 All the saints salute you.14 The grace of the Lord Jesus Christ, and the love of God, and the communion of the Holy Spirit, be with you all.