2 KOR 5
1 t Gama mun sani in an rushe jikinmu na wannan duniya, Allah ya tanadar mana jiki a Sama, wato, wanda shi kansa ya yi, wanda zai dawwama. 2 t A jikin nan muna ajiyar zuciya, mun ƙosa mu samu a suturta mu da jiki namu na Sama, 3 gama in aka suturta mu da shi, ba za a same mu tsirara ba. 4 t Sa'ad da muke zaune a cikin jikin nan na duniya, nishi muke domin matsuwar da muke sha, ba domin muna so mu rabu da jikinmu na wannan duniya ba ne, amma don so muke yi a suturta mu da na Sama, domin mai rai ya shafe mai mutuwa.
5 t Allah kuwa shi ya tanadar mana wannan sākewar, shi da ya ba mu Ruhunsa, domin tabbatar da abin da zai yi a nan gaba.
6 Saboda haka, kullum muke da ƙarfin zuciya, mun kuma sani, muddin muna tare da wannan jiki, a rabe muke da Ubangiji, 7 t domin zaman bangaskiya muke yi, ba na ganin ido ba. 8 t Hakika muna da ƙarfin zuciya, mun kuma gwammace mu rabu da jikin nan, mu zauna a gun Ubangiji. 9 t Saboda haka, ko muna gunsa, ko muna a rabe da shi, burinmu shi ne mu faranta masa zuciya.
10 t Don lalle ne a gabatar da mu duka, a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, domin kowa yă sami sakamakon abin da ya yi tun yana tare da wannan jiki, ko mai kyau ne, ko kuma marar kyau.Aikin Sulhuntawa
11 t Da yake muna tsoron Ubangiji, shi ya sa muke ƙoƙarin rinjayar mutane. Yadda muke kuwa, ai, sananne ne ga Allah, muna fata ku ma haka abin yake a lamirinku. 12 t Har wa yau kuma, ba yabon kanmu muke yi a gare ku ba, sai dai muna ba ku hanyar yin taƙama da mu, don ku sami yadda za ku mai da jawabi ga waɗanda suke fariya da maƙaminsu, ba da halinsu ba. 13 t In hankalinmu ya fita, ai, saboda Allah ne, in kuwa a cikin hankalinmu muke, ai, ribarku ce. 14 t Ƙaunar Almasihu a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu.
15 t Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin waɗanda suke a raye, kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.
16 t Saboda haka, a nan gaba ba mā ƙara duban kowane mutum bisa ga ɗabi'ar jiki kawai, domin ko da yake mun taɓa duban Almasihu bisa ga ɗabi'ar jiki, yanzu ba ma ƙara dubansa haka. 17 t Saboda haka, duk wanda yake na Almasihu sabuwar halitta ne, tsohon al'amari duk ya shuɗe, ga shi, kome ya zama sabo. 18 t Duk wannan kuwa yin Allah ne, shi da ya sulhunta mu da kansa ta wurin Almasihu, ya kuma ba mu aikin shelar sulhuntawar, 19 t wato, Allah ne, ta wurin Almasihu, yake sulhunta 'yan adam da shi kansa, ba ya kuwa lasafta laifofinsu a kansu ba, ya kuma danƙa mana maganar nan ta sulhuntawa. 20 t Saboda haka, mu jakadu ne na Almasihu, wato, Allah na neman mutane ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Almasihu, ku sulhuntu da Allah. 21 t Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurinsa.
2 Corinthians 5
1 For we know that if the earthly house of our tabernacle be dissolved, we have a building from God, a house not made with hands, eternal, in the heavens.2 For verily in this we groan, longing to be clothed upon with our habitation which is from heaven:3 if so be that being clothed we shall not be found naked.4 For indeed we that are in this tabernacle do groan, being burdened; not for that we would be unclothed, but that we would be clothed upon, that what is mortal may be swallowed up of life.5 Now he that wrought us for this very thing is God, who gave unto us the earnest of the Spirit.6 Being therefore always of good courage, and knowing that, whilst we are at home in the body, we are absent from the Lord7 (for we walk by faith, not by sight);8 we are of good courage, I say, and are willing rather to be absent from the body, and to be at home with the Lord.9 Wherefore also we make it our aim, whether at home or absent, to be well-pleasing unto him.10 For we must all be made manifest before the judgment-seat of Christ; that each one may receive the things done in the body, according to what he hath done, whether it be good or bad.11 Knowing therefore the fear of the Lord, we persuade men, but we are made manifest unto God; and I hope that we are made manifest also in your consciences.12 We are not again commending ourselves unto you, but speak as giving you occasion of glorying on our behalf, that ye may have wherewith to answer them that glory in appearance, and not in heart.13 For whether we are beside ourselves, it is unto God; or whether we are of sober mind, it is unto you.14 For the love of Christ constraineth us; because we thus judge, that one died for all, therefore all died;15 and he died for all, that they that live should no longer live unto themselves, but unto him who for their sakes died and rose again.16 Wherefore we henceforth know no man after the flesh: even though we have known Christ after the flesh, yet now we know him so no more.17 Wherefore if any man is in Christ, he is a new creature: the old things are passed away; behold, they are become new.18 But all things are of God, who reconciled us to himself through Christ, and gave unto us the ministry of reconciliation;19 to wit, that God was in Christ reconciling the world unto himself, not reckoning unto them their trespasses, and having committed unto us the word of reconciliation.20 We are ambassadors therefore on behalf of Christ, as though God were entreating by us: we beseech you on behalf of Christ, be ye reconciled to God.21 Him who knew no sin he made to be sin on our behalf; that we might become the righteousness of God in him.