2 BIT 1
Gaisuwa
1 t Daga Saminu Bitrus, bawan Yesu Almasihu, manzonsa kuma, zuwa ga waɗanda aka yi wa baiwar bangaskiya mai daraja iri ɗaya da tamu, albarkacin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Almasihu.
2 t Alheri da salama su yawaita a gare ku, a wajen sanin Allah da Yesu UbangijinmuKiranku da Zaɓenku
3 t Allah da ikonsa yā yi mana baiwa da dukan abubuwan da suka wajaba ga rayuwa da kuma binsa, ta sanin wanda ya kira mu ga samun ɗaukakarsa da fifikonsa, 4 t waɗanda kuma ta wurinsu ya yi mana baiwa da manyan alkawaransa masu ɗaukaka ƙwarai, domin ta wurin waɗannan ku zama masu tarayya da Allah a wajen ɗabi'arsa, da yake kun tsira daga ɓācin nan dake a duniya da muguwar sha'awa take haifa. 5 t Saboda wannan dalili musamman, sai ku yi matuƙar himma, ku ƙara bangaskiyarku da halin kirki, halin kirki da sanin ya kamata, 6 t sanin ya kamata da kamunkai, kamunkai da jimiri, jimiri da bin Allah, 7 t bin Allah da son 'yan'uwa, son 'yan'uwa kuma da ƙauna. 8 t In kuwa halayen nan sun zama naku ne, har suna yalwata, za su sa ku kada ku yi zaman banza, ko marasa amfani a wajen sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu. 9 t Domin duk wanda ya rasa halayen nan, to, makaho ne ko kuwa ganinsa dishi-dishi ne, ya kuma mance an tsarkake shi daga zunubansa na dā. 10 t Saboda haka, ya ku 'yan'uwa, ku ƙara ba da himma ku tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Domin in kun bi waɗannan halaye, ba za ku fādi ba har abada.
11 Ta haka kuma, za a ba ku cikakken 'yancin shiga madawwamin mulki na Ubangijinmu Mai Cetonmu Yesu Almasihu.
12 t Don haka, lalle kullum ba zan fasa yi muku tunin waɗannan abubuwa ba, ko da yake kun san su, kun kuma kahu a kan gaskiyar nan da kuke da ita. 13 t A ganina daidai ne, muddin ina raye a cikin jikin nan, in riƙa faɗakar da ku ta hanyar tuni, 14 t da yake na sani na yi kusan rabuwa da jikin nan nawa, kamar yadda Ubangijinmu Yesu Almasihu ya yi mini ishara.
15 t Aniyata ce, a kowane lokaci ku iya tunawa da waɗannan abubuwa bayan ƙauracewata.Ganin Ɗaukakarsa Muraran
16 t Ai, ba tatsuniyoyi da aka ƙaga da wayo muka bi ba, sa'ad da muka sanar da ku ikon Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma bayyanarsa, ɗaukakarsa ce muka gani muraran. 17 t Domin sa'ad da Allah Uba ya girmama shi, ya kuma ɗaukaka shi, sai murya ta zo masa daga mafificiyar ɗaukaka cewa, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai,” 18 t mu ne muka ji muryar nan da aka saukar daga sama, don muna tare da shi a kan tsattsarkan Dutsen nan. 19 t Har wa yau kuma, aka ƙara tabbatar mana da maganar annabcin nan, ya kuwa kyautu a gare ku, ku mai da hankali a gare ta, kamar fitila take mai haskakawa a wuri mai duhu har ya zuwa asubahin ranar nan, gamzaki kuma yă bayyana a zukatanku. 20 Da farko dai, lalle ne ku fahimci wannan cewa, ba wani annabci a Littattafai da za a iya fassarawa ta ra'ayin mutum. 21 t Domin ba wani annabcin da ya taɓa samuwa ta nufin mutum, sai dai mutane ne Ruhu Mai Tsarki yake izawa, Allah yana magana ta bakinsu.
2 Peter 1
1 Simon Peter, a servant and apostle of Jesus Christ, to them that have obtained a like precious faith with us in the righteousness of our God and the Saviour Jesus Christ:2 Grace to you and peace be multiplied in the knowledge of God and of Jesus our Lord;3 seeing that his divine power hath granted unto us all things that pertain unto life and godliness, through the knowledge of him that called us by his own glory and virtue;4 whereby he hath granted unto us his precious and exceeding great promises; that through these ye may become partakers of the divine nature, having escaped from the corruption that is in that world by lust.5 Yea, and for this very cause adding on your part all diligence, in your faith supply virtue; and in your virtue knowledge;6 and in your knowledge self-control; and in your self-control patience; and in your patience godliness;7 and in your godliness brotherly kindness; and in your brotherly kindness love.8 For if these things are yours and abound, they make you to be not idle nor unfruitful unto the knowledge of our Lord Jesus Christ.9 For he that lacketh these things is blind, seeing only what is near, having forgotten the cleansing from his old sins.10 Wherefore, brethren, give the more diligence to make your calling and election sure: for if ye do these things, ye shall never stumble:11 for thus shall be richly supplied unto you the entrance into the eternal kingdom of our Lord and Saviour Jesus Christ.12 Wherefore I shall be ready always to put you in remembrance of these things, though ye know them, and are established in the truth which is with you.13 And I think it right, as long as I am in this tabernacle, to stir you up by putting you in remembrance;14 knowing that the putting off of my tabernacle cometh swiftly, even as our Lord Jesus Christ signified unto me.15 Yea, I will give diligence that at every time ye may be able after my decease to call these things to remembrance.16 For we did not follow cunningly devised fables, when we made known unto you the power and coming of our Lord Jesus Christ, but we were eyewitnesses of his majesty.17 For he received from God the Father honor and glory, when there was borne such a voice to him by the Majestic Glory, This is my beloved Son, in whom I am well pleased:18 and this voice we ourselves heard borne out of heaven, when we were with him in the holy mount.19 And we have the word of prophecy made more sure; whereunto ye do well that ye take heed, as unto a lamp shining in a dark place, until the day dawn, and the day-star arise in your hearts:20 knowing this first, that no prophecy of scripture is of private interpretation.21 For no prophecy ever came by the will of man: but men spake from God, being moved by the Holy Spirit.