previous next

2 BIT 2

Annabawan Ƙarya da Malaman Ƙarya

(Yahuza 4-13)

1  t Amma fa annabawan ƙarya sun bayyana a cikin jama'a, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku, waɗanda za su saɗaɗo da maɓarnacciyar fanɗarewa, har ma su ƙi Mamallakin da ya fanso su, suna jawo wa kansu hallaka farat ɗaya. 2 Da yawa kuwa za su bi fajircinsu, har za a kushe hanyar gaskiya saboda su.

3 t Mahaɗantan malaman nan na ƙarya za su ribace ku da tsararrun labarunsu. An riga an yanke hukuncinsu tun dā, wanda zai hallaka su a shirye yake sosai.
4  t Da yake Allah bai rangwanta wa mala'iku ba sa'ad da suka yi zunubi, sai ya jefa su a Gidan Wuta, ya tura su a cikin ramummuka masu zurfi, masu baƙin duhu, a tsare su har ya zuwa ranar hukunci, 5 t tun da yake bai rangwanta wa mutanen tun can dā dā kuma ba, amma ya kiyaye Nuhu mai wa'azin adalci, da waɗansu mutum bakwai, sa'ad da ya aiko da Ruwan Tsufana zuwa a cikin duniyar nan ta marasa bin Allah, 6 t da yake kuma ya mai da biranen Saduma da Gwamrata toka, ya yi musu hukuncin hallaka, ya mai da su abin ishara ga marasa bin Allah, 7 t da yake kuma ya ceci Lutu adali, wanda fajircin kangararru ya baƙanta masa rai ƙwarai 8 (don kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, sa'ad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci), 9 t ashe kuwa, Ubangiji ya san yadda zai kuɓutar da masu tsoronsa daga gwaje-gwaje, ya kuma tsare marasa adalci a kan jiran hukunci, har ya zuwa ranar shari'a,

10 t tun ba waɗanda suka dulmuya a cikin muguwar sha'awa mai ƙazantarwa ba, suke kuma raina mulki.
Masu tsaurin ido ne su, masu taurin kai kuma, ba sa jin tsoron zagin masu ɗaukaka.
11 t Amma kuwa mala'iku, ko da yake sun fi su ƙarfi da iko, duk da haka, ba su ɗora musu laifi da zage-zage a gaban Ubangiji. 12 t Amma waɗannan mutane, kamar daddobi marasa hankali suke, masu bin abin da jikinsu ya ba su kawai, waɗanda aka haifa, don a kama a kashe, har suna kushen abubuwan da ba su fahinta ba, lalle kuwa za su hallaka a sanadin ɓacin nan nasu, 13 t suna shan sakamakon muguntarsu. Sun ɗauka a kan jin daɗi ne a yi annashuwa da rana kata. Sun baƙanta, sun zama abin kunya. Sun dulmuya ga ciye-ciye da shaye-shaye, suna ta nishaɗi a cikinku. 14 t Jarabar zina take a gare su, ba sa ƙoshi da yin zunubi. Suna yaudarar marasa kintsuwa. Sun ƙware da ƙwaɗayi. La'anannun iri! 15 t Sun yar da miƙaƙƙiyar hanya, sun bauɗe, sun bi hanyar Bal'amu ɗan Beyor, wanda ya cika son samu ta hanyar mugunta.

16 t Amma an tsawata masa a kan laifinsa, har dabba marar baki ma ta yi magana kamar mutum, ta kwaɓi haukan annabin nan.
17  t Mutanen nan kamar mabubbugen ruwa wadanda suka kafe, ƙasashi ne da iska take kaɗawa. Su ne aka tanada wa matsanancin duhu. 18 t Ta surutai barkatai marasa kan gado na ruba, da halinsu na fasikanci sukan shammaci waɗanda da ƙyar suke kuɓucewa daga masu zaman saɓo, 19 t suna yi musu alkawarin 'yanci, ga shi kuwa, su da kansu bayin zamba ne. Don mutum bawa ne na duk abin da ya rinjaye shi. 20 t In kuwa bayan da suka tsere wa ƙazantar duniyar albarkacin sanin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu, suka kuma sāke sarƙafewa a ciki, har aka rinjaye su, ƙarshen zamansu ya fi na fari lalacewa ke nan. 21 t Da ba su taɓa sanin hanyar adalci tun da fari ba, da ya fiye musu, bayan sun san ta, sa'an nan su juya ga barin umarnin nan mai tsarki. 22 t Ai kuwa, karin maganar nan na gaskiya ya dace da su cewa, “Kare ya cinye amansa,” da kuma, “Gursunar da aka yi wa wanka ta kome ga birgima cikin laka.”

2 Peter 2

1 But there arose false prophets also among the people, as among you also there shall be false teachers, who shall privily bring in destructive heresies, denying even the Master that bought them, bringing upon themselves swift destruction.2 And many shall follow their lascivious doings; by reason of whom the way of the truth shall be evil spoken of.3 And in covetousness shall they with feigned words make merchandise of you: whose sentence now from of old lingereth not, and their destruction slumbereth not.4 For if God spared not angels when they sinned, but cast them down to hell, and committed them to pits of darkness, to be reserved unto judgment;5 and spared not the ancient world, but preserved Noah with seven others, a preacher of righteousness, when he brought a flood upon the world of the ungodly;6 and turning the cities of Sodom and Gomorrah into ashes condemned them with an overthrow, having made them an example unto those that should live ungodly;7 and delivered righteous Lot, sore distressed by the lascivious life of the wicked8 (for that righteous man dwelling among them, in seeing and hearing, vexed his righteous soul from day to day with their lawless deeds):9 the Lord knoweth how to deliver the godly out of temptation, and to keep the unrighteous under punishment unto the day of judgment;10 but chiefly them that walk after the flesh in the lust of defilement, and despise dominion. Daring, self-willed, they tremble not to rail at dignities:11 whereas angels, though greater in might and power, bring not a railing judgment against them before the Lord.12 But these, as creatures without reason, born mere animals to be taken and destroyed, railing in matters whereof they are ignorant, shall in their destroying surely be destroyed,13 suffering wrong as the hire of wrong-doing; men that count it pleasure to revel in the day-time, spots and blemishes, revelling in their deceivings while they feast with you;14 having eyes full of adultery, and that cannot cease from sin; enticing unstedfast souls; having a heart exercised in covetousness; children of cursing;15 forsaking the right way, they went astray, having followed the way of Balaam the son of Beor, who loved the hire of wrong-doing;16 but he was rebuked for his own transgression: a dumb ass spake with man’s voice and stayed the madness of the prophet.17 These are springs without water, and mists driven by a storm; for whom the blackness of darkness hath been reserved.18 For, uttering great swelling words of vanity, they entice in the lusts of the flesh, by lasciviousness, those who are just escaping from them that live in error;19 promising them liberty, while they themselves are bondservants of corruption; for of whom a man is overcome, of the same is he also brought into bondage.20 For if, after they have escaped the defilements of the world through the knowledge of the Lord and Saviour Jesus Christ, they are again entangled therein and overcome, the last state is become worse with them than the first.21 For it were better for them not to have known the way of righteousness, than, after knowing it, to turn back from the holy commandment delivered unto them.22 It has happened unto them according to the true proverb, The dog turning to his own vomit again, and the sow that had washed to wallowing in the mire.