previous next

2 TAS 1

Gaisuwa

1  t Daga Bulus, da Sila, da Timoti, zuwa ga Ikkilisiyar Tasalonikawa, wadda take ta Allah ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu.

2  t Alheri da salama na Allah Uba, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Bayyanar Almasihu don Yin Hukunci


3  t Lalle ne a kullum mu gode wa Allah saboda ku, 'yan'uwa, haka kuwa ya kyautu, da yake bangaskiyarku haɓaka take yi ƙwarai da gaske, har ma ƙaunar kowane ɗayanku ga juna ƙaruwa take yi.

4 t Saboda haka, mu kanmu ma taƙama muke yi da ku a cikin ikilisiyoyin Allah, saboda jimirinku, da bangaskiyarku a cikin yawan tsananin da kuke sha, da ƙuncin da kuke a ciki.
5  t Wannan kuwa ita ce tabbatar hukunci mai adalci na Allah, domin a lasafta ku a cikin waɗanda suka cancanci zama a Mulkin Allah, wanda kuke shan wuya dominsa, 6 t domin kuwa Allah ya ga adalci ne, yă yi sakamokon ƙunci ga waɗanda suke ƙuntata muku, 7 t yă kuma ba ku hutu har da mu ma, ku da ake ƙuntata wa ɗin, a ranar bayyanar Ubangiji Yesu daga Sama tare da manyan mala'ikunsa, a cikin wuta mai ruruwa, 8 t yana ta sāka wa waɗanda suke ƙi sanin Allah, da kuma waɗanda suka ƙi bin bisharar Ubangijinmu Yesu. 9 t Za su sha hukuncin madawwamiyar hallaka, suna a ware da zatin Ubangiji, da kuma, maɗaukakin ikonsa, 10 t wato, a lokacin da ya dawo, tsarkakansa su ɗaukaka shi, duk masu ba da gaskiya kuma su yi al'ajabinsa a ranar nan, don kun gaskata shaidar da muka yi muku. 11 t Da wannan maƙasudi, a kullum muke yi muku addu'a, Allahnmu yă sa ku cancanci kiransa, ya biya muku duk muradinku na yin nagarta, da aikin bangaskiya ta wurin ƙarfin ikonsa, 12 t don a ɗaukaka sunan Ubangijinmu Yesu a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu.

2 Thessalonians 1

1 Paul, and Silvanus, and Timothy, unto the church of the Thessalonians in God our Father and the Lord Jesus Christ;2 Grace to you and peace from God the Father and the Lord Jesus Christ.3 We are bound to give thanks to God always to you, brethren, even as it is meet, for that your faith growth exceedingly, and the love of each one of you all toward one another aboundeth;4 so that we ourselves glory in you in the churches of God for your patience and faith in all your persecutions and in the afflictions which ye endure;5 which is a manifest token of the righteous judgment of God; to the end that ye may be counted worthy of the kingdom of God, for which ye also suffer:6 if so be that it is a righteous thing with God to recompense affliction to them that afflict you,7 and to you that are afflicted rest with us, at the revelation of the Lord Jesus from heaven with the angels of his power in flaming fire,8 rendering vengeance to them that know not God, and to them that obey not the gospel of our Lord Jesus:9 who shall suffer punishment, even eternal destruction from the face of the Lord and from the glory of his might,10 when he shall come to be glorified in his saints, and to be marvelled at in all them that believed (because our testimony unto you was believed) in that day.11 To which end we also pray always for you, that our God may count you worthy of your calling, and fulfil every desire of goodness and every work of faith, with power;12 that the name of our Lord Jesus may be glorified in you, and ye in him, according to the grace of our God and the Lord Jesus Christ.