2 TIM 1
Gaisuwa
1 t Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, don sanar da alkawarin nan na rai wanda yake ga Almasihu Yesu,
2 t zuwa ga Timoti ƙaunataccen ɗana.
Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijinmu su tabbata a gare ka.Kada Ka Ji Kunya
3 t Ina gode wa Allah, wanda nake bauta wa da lamiri mai tsabta, kamar yadda kakannina suka yi, duk sa'ad da nake tunawa da kai a cikin addu'ata ba fāsawa. 4 t Sa'ad da nake tunawa da hawayenka, nakan yi began ganinka dare da rana, domin in yi farin ciki matuƙa. 5 t Ina tunawa da sahihiyar bangaskiyarka, wadda da farko take tare da kakarka Loyis, da mahaifiyarka Afiniki, a yanzu kuma na tabbata tana tare da kai. 6 t Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwar nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗora maka hannuwana.
7 t Ai, Allah ba halin tsoro ya ba mu ba, hali mai ƙarfi ne, mai ƙauna, da kuma kamunkai.
8 t Saboda haka, kada ka ji kunyar ba da shaidar Ubangijinmu, da kuma tawa, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi, sai dai mu jure wa shan wuya tare, saboda bishara, bisa ga ikon Allah, 9 t wanda ya cece mu, ya kuma kira mu da kira mai tsarki, ba don wani aikin lada da muka yi ba, sai dai domin nufinsa, da kuma alherinsa, da aka yi mana baiwa tun fil'azal, a cikin Almasihu Yesu, 10 t wadda a yanzu aka bayyana ta bayyanar Mai Cetonmu Almasihu Yesu, wanda ya shafe mutuwa, ya kuma bayyana rai da rashin mutuwa, ta wurin bishara. 11 t A wannan bishara an sa ni mai wa'azi, da kuma manzonta, da mai koyarwarta kuma. 12 t Saboda haka, ne nake shan wuya haka. Duk da haka, ban kunyata ba, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata yana da iko ya kiyaye abin da na danƙa masa, har ya zuwa waccan rana. 13 t Ka yi koyi da sahihiyar maganar da ka ji daga gare ni, da bangaskiya da ƙauna da take ga Almasihu Yesu.
14 t Kyakkyawan abin nan da aka ba ka amana, ka kiyaye shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki, wanda yake zaune a zuciyarmu.
15 t Ka dai sani duk waɗanda suke ƙasar Asiya sun juya mini baya, a cikinsu kuwa har da Fijalas da kuma Harmajanas. 16 t Ubangiji yă yi wa iyalin Onisifaras jinƙai, don sau da yawa yake sanyaya mini zuciya, bai kuwa ji kunyar ɗaurina da aka yi ba. 17 Har ma da ya zo Roma, sai ya neme ni ido a rufe, ya kuwa same ni. 18 t Ubangiji ya yi masa jinƙai a waccan rana. Ka dai sani sarai yadda ya yi ɗawainiya mai yawa a Afisa.
2 Timothy 1
1 Paul, an apostle of Christ Jesus through the will of God, according to the promise of the life which is in Christ Jesus,2 to Timothy, my beloved child: Grace, mercy, peace, from God the Father and Christ Jesus our Lord.3 I thank God, whom I serve from my forefathers in a pure conscience, how unceasing is my remembrance of thee in my supplications, night and day4 longing to see thee, remembering thy tears, that I may be filled with joy;5 having been reminded of the unfeigned faith that is in thee; which dwelt first in thy grandmother Lois, and thy mother Eunice; and, I am persuaded, in thee also.6 For which cause I put thee in remembrance that thou stir up the gift of God, which is in thee through the laying on of my hands.7 For God gave us not a spirit of fearfulness; but of power and love and discipline.8 Be not ashamed therefore of the testimony of our Lord, nor of me his prisoner: but suffer hardship with the gospel according to the power of God;9 who saved us, and called us with a holy calling, not according to our works, but according to his own purpose and grace, which was given us in Christ Jesus before times eternal,10 but hath now been manifested by the appearing of our Saviour Christ Jesus, who abolished death, and brought life and immortality to light through the gospel,11 whereunto I was appointed a preacher, and an apostle, and a teacher.12 For which cause I suffer also these things: yet I am not ashamed; for I know him whom I have believed, and I am persuaded that he is able to guard that which I have committed unto him against that day.13 Hold the pattern of sound words which thou hast heard from me, in faith and love which is in Christ Jesus.14 That good thing which was committed unto thee guard through the Holy Spirit which dwelleth in us.15 This thou knowest, that all that are in Asia turned away from me; of whom are Phygelus and Hermogenes.16 The Lord grant mercy unto the house of Onesiphorus: for he oft refreshed me, and was not ashamed of my chain;17 but, when he was in Rome, he sought me diligently, and found me18 (the Lord grant unto him to find mercy of the Lord in that day); and in how many things he ministered at Ephesus, thou knowest very well.