2 TIM 2
Amintaccen Sojan Almasihu
1 t Saboda haka, ya kai ɗana, sai ka ƙarfafa da alherin da yake ga Almasihu Yesu. 2 t Abin da ka ji a guna a gaban shaidu masu yawa kuwa, sai ka danƙa wa amintattun mutane, waɗanda su ma za su koya wa waɗansu. 3 t Kai kuma ka jure wa shan wuya, kana amintaccen sojan Almasihu Yesu. 4 Ai, ba sojan da yake a bakin dāga da ransa zai sarƙafe da sha'anin duniya, tun da yake burinsa shi ne yă faranta wa wanda ya ɗauke shi soja. 5 t Mai wasan guje-guje da tsalle-tsalle, ba zai sami ɗaukaka ba, sai ko ya bi dokokin wasan. 6 Ma'aikaci, ai, shi ya kamata yă fara cin amfanin gonar.
7 Ka yi tunani a kan abin da nake faɗa, Ubangiji kuwa zai ba ka fahimtar kome.
8 t Ka tuna da Yesu Almasihu fa, shi da aka tashe shi daga matattu, na zuriyar Dawuda bisa ga bisharata, 9 t wadda nake shan wuya saboda ita, har nake ɗaure kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a ɗaure take ba.
10 t Don haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton nan da yake samuwa ta wurin Almasihu, a game da madawwamiyar ɗaukaka.
11 t Maganar nan tabbatacciya ce,
“In mun mutu tare da shi, za mu rayu ma tare da shi,
12 t In mun jure, za mu yi mulki ma tare da shi,
In mun yi musun saninsa, shi ma zai yi musun saninmu,
13 t In ba mu da aminci, shi kam ya tabbata mai aminci,
Domin ba zai yi musun kansa ba.”Yardajjen Ma'aikaci
14 t Ka riƙa tuna musu da haka, ka kuma gama su da Ubangiji, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi. 15 t Ka himmantu, ka miƙa kanka yardajje ga Allah, ma'aikaci wanda ba hanya ya kunyata, mai kuma fassara Maganar gaskiya daidai. 16 t Ka yi nesa da masu maganganun banza na sāɓo. Sai daɗa jan mutane zuwa ga rashin bin Allah suke yi, 17 t maganarsu takan haɓaka kamar gyambo. A cikinsu har da Himinayas da Filitas, 18 t waɗanda suka bauɗe wa gaskiya suna cewa tashin matattu ya riga ya wuce, suna jirkitar da bangaskiyar waɗansu.
19 t Duk da haka, ƙaƙƙarfan harsashin ginin nan na Allah ya tabbata, hatimin nan kuwa yana jikinsa cewa, “Ubangiji ya san nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yă yi nesa da aikata mugunta.”
20 t A babban gida, ba kayan zinariya da na azurfa ne kawai ba, har ma da na itace da na yumɓu, waɗansu don aikin ɗaukaka, waɗansu kuwa don ƙasƙantaccen aiki.
21 t Kowa yă tsarkake kansa daga ayyukan nan ƙasƙantattu, zai zama ma'aikaci mai daraja, tsarkakakke, mai amfani ga Ubangiji, shiryayye ga kowane kyakkyawan aiki.
22 t Don haka, sai ka guje wa mugayen sha'awace-sha'awacen ƙuruciya, ka dimanci aikin adalci, da bangaskiya, da ƙauna, da kuma salama, tare da waɗanda suke roƙon Ubangiji da zuciya tsarkakakkiya. 23 Ka ƙi gardandamin banza marasa ma'ana, ka san lalle suna jawo husuma. 24 t Bawan Ubangiji kuwa lalle ba zai zama mai husuma ba, sai dai ya zama salihi ga kowa, gwanin koyarwa, mai haƙuri, 25 t mai sa abokan hamayyarsa a kan hanya da tawali'u, ko Allah zai sa su tuba, su kai ga sanin gaskiya, 26 t su kuɓuce wa tarkon Iblis, su bi nufin Allah, bayan da Iblis ya tsare su.
2 Timothy 2
1 Thou therefore, my child, be strengthened in the grace that is in Christ Jesus.2 And the things which thou hast heard from me among many witnesses, the same commit thou to faithful men, who shall be able to teach others also.3 Suffer hardship with me, as a good soldier of Christ Jesus.4 No soldier on service entangleth himself in the affairs of this life; that he may please him who enrolled him as a soldier.5 And if also a man contend in the games, he is not crowned, except he have contended lawfully.6 The husbandmen that laboreth must be the first to partake of the fruits.7 Consider what I say; for the Lord shall give thee understanding in all things.8 Remember Jesus Christ, risen from the dead, of the seed of David, according to my gospel:9 wherein I suffer hardship unto bonds, as a malefactor; but the word of God is not bound.10 Therefore I endure all things for the elect’s sake, that they also may obtain the salvation which is in Christ Jesus with eternal glory.11 Faithful is the saying: For if we died with him, we shall also live with him:12 if we endure, we shall also reign with him: if we shall deny him, he also will deny us:13 if we are faithless, he abideth faithful; for he cannot deny himself.14 Of these things put them in remembrance, charging them in the sight of the Lord, that they strive not about words, to no profit, to the subverting of them that hear.15 Give diligence to present thyself approved unto God, a workman that needeth not to be ashamed, handling aright the word of truth.16 But shun profane babblings: for they will proceed further in ungodliness,17 and their word will eat as doth a gangrene: of whom is Hymenaeus an Philetus;18 men who concerning the truth have erred, saying that the resurrection is past already, and overthrow the faith of some.19 Howbeit the firm foundation of God standeth, having this seal, The Lord knoweth them that are his: and, Let every one that nameth the name of the Lord depart from unrighteousness.20 Now in a great house there are not only vessels of gold and of silver, but also of wood and of earth; and some unto honor, and some unto dishonor.21 If a man therefore purge himself from these, he shall be a vessel unto honor, sanctified, meet for the master’s use, prepared unto every good work.22 after righteousness, faith, love, peace, with them that call on the Lord out of a pure heart.23 But foolish and ignorant questionings refuse, knowing that they gender strifes.24 And the Lord’s servant must not strive, but be gentle towards all, apt to teach, forbearing,25 in meekness correcting them that oppose themselves; if peradventure God may give them repentance unto the knowledge of the truth,26 and they may recover themselves out of the snare of the devil, having been taken captive by him unto his will.