previous next

2 TIM 3

Halin Ƙarshen Zamani

1  t Amma ka fahimta, a zamanin ƙarshe za a sha wuya ƙwarai. 2 t Mutane za su zama masu sonkai, da masu son kuɗi, da masu ruba, da masu girmankai, da masu zagezage, da marasa bin iyayensu, da masu butulci, da marasa tsarkaka, 3 da marasa ƙauna, da masu riƙo a zuci, da masu yanke, da fajirai, da maƙetata, da maƙiyan nagarta, 4 t da maciya amana, da masu taurinkai, da masu homa, da masu son annashuwa fiye da son Allah, 5 suna riƙe da siffofin ibada, amma suna sāɓa wa ikonta. Ka yi nesa da irin waɗannan mutane. 6 t A cikinsu kuwa akwai masu saɗaɗawa su shiga gidajen mutane, suna rinjayar mata marasa wayo, waɗanda zunubi ya sha kansu, muguwar sha'awa iri iri kuma ta ɗauke musu hankali, 7 kullum suna koyo, amma kullum sai su kāsa kaiwa ga sanin gaskiya. 8 t Kamar yadda Yanisu da Yambirisu suka tayar wa Musa, haka mutanen nan kuma suke tayar wa gaskiya, mutane ne masu ɓataccen hankali ƙwarai, bangaskiyarsu kuwa ta banza ce.

9 t Amma ba za su yi nisa ba, don rashin hankalinsu zai bayyana ga kowa, kamar na mutanen nan biyu.

Gargaɗin Bulus ga Timoti na Ƙarshe


10  t Kai kam, ka riga ka kiyaye koyarwata, da halina, da niyyata, da bangaskiyata, da haƙurina, da ƙaunata, da jimirina, 11 t da kuma yawan tsanani, da wuyar da na sha, da suka same ni a Antakiya, da Ikoniya, da Listira, wato irin tsanance-tsanancen da na jure. Amma Ubangiji ya kuɓutar da ni daga cikinsu duka. 12 t Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna ga Almasihu Yesu, za su sha tsanani. 13 t Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu. 14 t Amma kai kuwa, ka zauna a kan abin da ka koya, ka kuma haƙƙaƙe, gama ka san wurin waɗanda ka koye su, 15 t da kuma yadda tun kana ɗan ƙaramin yaro ka san Littattafai masu tsarki, waɗanda suke koya maka hanyar samun ceto ta dalilin bangaskiya ga Almasihu Yesu. 16 t Kowane Nassi hurarre na Allah ne, mai amfani ne kuma wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali, da kuma tarbiyyar aikin adalci, 17 t domin bawan Allah yă zama cikakke, shiryayye sosai ga kowane kyakkyawan aiki.

2 Timothy 3

1 But know this, that in the last days grievous times shall come.2 For men shall be lovers of self, lovers of money, boastful, haughty, railers, disobedient to parents, unthankful, unholy,3 without natural affection, implacable, slanderers, without self-control, fierce, no lovers of good,4 traitors, headstrong, puffed up, lovers of pleasure rather than lovers of God;5 holding a form of godliness, but having denied the power therefore. From these also turn away.6 For of these are they that creep into houses, and take captive silly women laden with sins, led away by divers lusts,7 ever learning, and never able to come to the knowledge of the truth.8 And even as Jannes and Jambres withstood Moses, so do these also withstand the truth. Men corrupted in mind, reprobate concerning the faith.9 But they shall proceed no further. For their folly shall be evident unto all men, as theirs also came to be.10 But thou didst follow my teaching, conduct, purpose, faith, longsuffering, love, patience,11 persecutions, sufferings. What things befell me at Antioch, at Iconium, at Lystra; what persecutions I endured. And out of them all the Lord delivered me.12 Yea, and all that would live godly in Christ Jesus shall suffer persecution.13 But evil men and impostors shall wax worse and worse, deceiving and being deceived.14 But abide thou in the things which thou hast learned and hast been assured of, knowing of whom thou hast learned them.15 And that from a babe thou hast known the sacred writings which are able to make thee wise unto salvation through faith which is in Christ Jesus.16 Every scripture inspired of God is also profitable for teaching, for reproof, for correction, for instruction which is in righteousness.17 That the man of God may be complete, furnished completely unto every good work.