previous next

3 YAH 1

Gaisuwa

1  t Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga Gayus, ƙaunatacce, wanda nake ƙauna da gaske.
2 Ya ƙaunataccena, ina addu'a kă sami zaman lafiya ta kowace hanya da kuma lafiya jiki, kamar yadda ruhunka yake a zaune lafiya. 3 t Na yi farin ciki ƙwarai sa'ad da waɗansu 'yan'uwa suka zo suka shaida gaskiyarka, yadda hakika kake bin gaskiya.

4 t Ba abin da ya fi faranta mini rai kamar in ji 'ya'yana suna bin gaskiya.

Yaba Kirkin Gayus


5  t Ya ƙaunataccena, duk abin da kake yi wa 'yan'uwa, aikin bangaskiya kake yi, tun ba ma ga baƙi ba. 6 Su ne suka shaida ƙaunarka a gaban ikkilisiya. Zai kyautu ka raka su a guzuri, kamar yadda ya cancanci bautar Allah, 7 t domin saboda sunan nan ne suka fito, ba sa kuma karɓar kome daga al'ummai.

8 Domin haka ya kamata mu karɓi irin mutanen nan, mu ɗau nauyinsu, domin mu zama abokan aiki da su a kan gaskiya.

Diyotarifis Mai Ƙin Bin Magana


9 Na yi wa ikkilisiya 'yar wasiƙa, amma shi Diyotarifis wanda yake so ya fi kowa a cikinsu, ya ƙi bin maganarmu.

10 t Saboda haka, in na zo zan tabbatar masa da abin da yake yi, yana surutu game da mu, yana ɓaɓɓata mu. Wannan ma bai ishe shi ba, har ya ƙi yi wa 'yan'uwa maraba, yana kuma hana masu so su marabce su, yana fitar da su daga ikkilisiya.

Kyakkyawar Shaida kan Dimitiriyas


11  t Ya ƙaunataccena, kada ka kwaikwayi mugun aiki, sai dai nagari. Kowa da yake aikin nagari na Allah ne. Mai mugun aiki kuwa bai san Allah ba sam.

12 t Dimitiriyas yana da kyakkyawar shaida a gun kowa, har gaskiya kanta ma tana yi masa shaida. Mu ma mun shaide shi, ka kuwa san shaidarmu tabbatacciya ce.

Gaisuwa


13 Dā kam, ina da abin da zan rubuto maka da yawa, amma yanzu na gwammace kada in rubuto a wasiƙa.

14 t Ina sa zuciya mu sadu ba da daɗewa ba, sa'an nan ma yi magana baka da baka.
15 Salama tă tabbata gare ku. Aminanmu suna gaishe ka. Ka gai da aminanmu kowa da kowa.

3 John 1

1 The elder unto Gaius the beloved, whom I love in truth.2 Beloved, I pray that in all things thou mayest prosper and be in health, even as thy soul prospereth.3 For I rejoiced greatly, when brethren came and bare witness unto thy truth, even as thou walkest in truth.4 Greater joy have I none than this, to hear of my children walking in the truth.5 Beloved, thou doest a faithful work in whatsoever thou doest toward them that are brethren and strangers withal;6 who bare witness to thy love before the church: whom thou wilt do well to set forward on their journey worthily of God:7 because that for the sake of the Name they went forth, taking nothing of the Gentiles.8 We therefore ought to welcome such, that we may be fellow-workers for the truth.9 I wrote somewhat unto the church: but Diotrephes, who loveth to have the preeminence among them, receiveth us not.10 Therefore, if I come, I will bring to remembrance his works which he doeth, prating against us with wicked words: and not content therewith, neither doth he himself receive the brethren, and them that would he forbiddeth and casteth them out of the church.11 Beloved, imitate not that which is evil, but that which is good. He that doeth good is of God: he that doeth evil hath not seen God.12 Demetrius hath the witness of all men, and of the truth itself: yea, we also bear witness: and thou knowest that our witness is true.13 I had many things to write unto thee, but I am unwilling to write them to thee with ink and pen:14 but I hope shortly to see thee, and we shall speak face to face. Peace be unto thee. The friends salute thee. Salute the friends by name.