A.M. 13
1 t To, a Ikkilisiyar da take Antakiya akwai waɗansu annabawa, da masu koyarwa, wato Barnaba, da Saminu wanda ake kira Baƙi, da Lukiyas Bakurane, da Manayan wanda aka goya tare da sarki Hirudus, da kuma Shawulu. 2 t Sa'ad da suke yi wa Ubangiji ibada, suna kuma yin azumi, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Sai ku keɓe mini Barnaba da Shawulu domin aikin da na kira su a kai.”
3 t Bayan kuma sun yi azumi, sun kuma yi addu'a, sai suka ɗora musu hannu, suka sallame su.Manzanni Sun Yi Wa'azi a Kubrus
4 t Su kuwa, da Ruhu Mai Tsarki ya aike su, suka tafi Salukiya, daga can kuma suka shiga jirgin ruwa sai tsibirin Kubrus. 5 t Da suka kai Salamis, suka sanar da Maganar Allah a majami'un Yahudawa, ga kuma Yahaya na taimakonsu. 6 t Bayan sun zazzaga tsibirin duka har Bafusa, suka iske wani mai sihiri, annabin ƙarya, Bayahude, mai suna Bar-yashu'a, 7 t Wanda yake tare da muƙaddas Sarjiyas Bulus, mutum mai basira. Sai muƙaddashin ya kira Barnaba da Shawulu ya nemi jin Maganar Allah. 8 t Amma Alimas mai sihirin nan, (don wannan ita ce ma'anar sunansa), ya mūsa musu, yana neman bauɗar da muƙaddashin nan daga bangaskiya. 9 t Shawulu kuwa, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya zuba masa ido, 10 t ya ce, “Kai babban maha'inci, munafiƙi, ɗan Iblis, magabcin adalci duka, ba za ka daina karkata miƙaƙƙun hanyoyin Ubangiji ba? 11 t To, ga shi, hannun Ubangiji na kanka, za ka makance, ba za ka ga rana ba har wani lokaci.” A nan take kuwa sai wani hazo da duhu suka rufe shi, ya yi ta neman wanda zai yi masa jagora.
12 t Da muƙaddashin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, yana mamaki da koyarwar Ubangiji.Bulus da Barnaba a Antakiya ta Bisidiya
13 t Sai Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafusa a jirgin ruwa, suka isa Bariyata ta ƙasar Bamfiliya. Yahaya kuwa ya bar su, ya koma Urushalima. 14 t Amma suka wuce gaba daga Bariyata, suka tafi Antakiya ta ƙasar Bisidiya. Ran Asabar kuma sai suka shiga majami'a suka zauna. 15 t Bayan an yi karatun Attaura da littattafan annabawa, shugabannin majami'ar suka aika musu, suka ce, “'Yan'uwa, in kuna da wata maganar gargaɗi da za ku yi wa jama'a, ai, sai ku yi.”
16 t Sai Bulus ya miƙe, ya ɗaga hannu a yi shiru, ya ce,
“Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, da sauran masu tsoron Allah, ku saurara! 17 t Allahn jama'ar nan Isra'ila ya zaɓi kakanninmu, ya ɗaukaka jama'ar sa'ad da suke baƙunci a ƙasar Masar, da maɗaukakin iko kuma ya fito da su daga cikinta. 18 t Wajen shekara arba'in yake haƙuri da su cikin jeji. 19 t Ya kuma hallaka al'umma bakwai a ƙasar Kan'ana, sai ya raba musu ƙasar tasu gādo, suka zauna har shekara arbaminya da hamsin. 20 t Bayan haka kuma ya naɗa musu mahukunta har ya zuwa zamanin Annabi Sama'ila. 21 t Sa'an nan suka roƙa a naɗa musu sarki, sai Allah ya ba su Saul ɗan Kish, mutumin kabilar Biliyaminu, har shekara arba'in. 22 t Bayan da ya kawar da shi sai ya gabatar da Dawuda ya zama sarkinsu, ya kuma shaide shi da cewa, ‘Na sami Dawuda ɗan Yesse, mutum ne da nake ƙauna ƙwarai, wanda kuma zai aikata dukan nufina.’ 23 t Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Isra'ila Mai Ceto, Yesu kamar yadda ya yi alkawari. 24 t Kafin ya bayyana a fili kuwa, Yahaya ya yi wa duk jama'ar Isra'ila wa'azi su tuba a kuma yi musu baftisma.
25 t Yayin da Yahaya ya kusa gama nasa zamani, sai ya ce, ‘Wa kuke tsammani nake? Ba fa ni ne shi ɗin nan ba. Amma ga shi akwai wani mai zuwa a bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in balle ba.’
26 t “Ya ku 'yan'uwa, zuriyar Ibrahim, da kuma sauran masu tsoron Allah a cikinku, mu fa aka aiko wa kalmar ceton nan. 27 t Ga shi, mazaunan Urushalima da shugabanninsu ba su gane shi ba, sa'an nan kuma ba su fahimci maganar annabawa da ake karantawa kowace Asabar ba, har suka cika maganar nan ta annabawa, yayin da suka hukunta shi. 28 t Ko da yake ba su same shi da wani laifin kisa ba, duk da haka suka roƙi Bilatus a kashe shi. 29 t Da suka cikasa dukkan abin da aka rubuta game da shi, suka sauko da shi daga kan gungumen, suka sa shi a kabari. 30 t Amma Allah ya tashe shi daga matattu. 31 t Kwanaki da yawa kuwa yana bayyana ga waɗanda suka zo tare da shi Urushalima daga Galili, waɗanda a yanzu su ne shaidunsa ga jama'a. 32 t Mu ma mun kawo muku albishir, cewa, alkawarin nan da Allah ya yi wa kakanninmu,
33 t ya cika mana shi, mu zuriyarsu, da ya ta da Yesu daga matattu, yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa,
‘Kai Ɗana ne,
Ni Ubanka ne yau.’
34 t Game da ta da shi daga matattu da Allah ya yi, a kan cewa ba zai sāke komawa cikin halin ruɓa ba kuwa, ga abin da ya ce,
‘Zan yi muku tsattsarkar albarkar nan da na tabbatar wa Dawuda.’
35 t Domin a wata Zabura ma ya ce,
‘Ba za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.’
36 t Dawuda kam, bayan da ya bauta wa mutanen zamaninsa bisa ga nufin Allah, ya yi barci, aka binne shi tare da kakanninsa, ya kuwa ruɓe. 37 Amma shi wannan da Allah ya tashe shi, bai ruɓa ba. 38 t Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku sani albarkacin mutumin nan ne ake sanar da ku gafarar zunubanku. 39 t Ta gare shi kuma, duk masu ba da gaskiya suka kuɓuta daga dukan abubuwan da ba dama Shari'ar Musa ta kuɓutar da ku.
40 Saboda haka sai ku mai da hankali, kada abin nan da littattafan annabawa suke faɗa ya aukar muku, wato
41 t ‘Ga shi, ku masu rainako,
Za ku ruɗe don mamaki, ku shuɗe!
Domin zan yi wani aiki a zamaninku,
Aikin da ba yadda za a yi ku gaskata,
Ko da wani ya gaya muku.’ ”
42 t Suna fita majami'a ke nan, sai mutane suka roƙe su su ƙara yi musu wannan magana a ran Asabar mai zuwa.
43 t Da jama'a suka watse, Yahudawa da yawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci, masu ibada, suka bi Bulus da Barnaba. Su kuma suka yi musu magana, suna yi musu gargaɗi su zauna a cikin alherin Allah.
44 Da Asabar ta kewayo, kusan duk birnin, suka hallara su ji Maganar Allah. 45 t Amma da Yahudawa suka ga taro masu yawa, suka yi kishi gaya, suka yi ta musun abubuwan da Bulus ya faɗa, suna zaginsa. 46 t Sai Bulus da Barnaba suka yi magana gabagaɗi, suka ce, “Ku, ya wajaba a fara yi wa Maganar Allah, amma da yake kun ture ta, kun nuna ba ku cancanci samun rai madawwami ba, to, za mu juya ga al'ummai.
47 t Domin haka ubangiji ya umarce mu, ya ce,
‘Na sa ka haske ga al'ummai,
Don ka zama sanadin ceto, har ya zuwa iyakar duniya.’ ”
48 Da al'ummai suka ji haka, suka yi farin ciki, suka ɗaukaka Maganar Ubangiji, ɗaukacin kuma waɗanda aka ƙaddara wa samun rai madawwami suka ba da gaskiya. 49 Maganar Ubangiji kuwa, sai ta yi ta yaɗuwa a duk ƙasar. 50 t Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu ibada, masu daraja, da kuma waɗansu manyan gari, suka haddasa tsanani ga Bulus da Barnaba, suka kore su daga ƙasarsu. 51 t Su kuwa suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaida a kansu, suka tafi Ikoniya. 52 Amma kuwa masu bi suna farin ciki matuƙa, suna kuma a cike da Ruhu Mai Tsarki.
Acts 13
1 Now there were at Antioch, in the church that was there, prophets and teachers, Barnabas, and Symeon that was called Niger, and Lucius of Cyrene, and Manaen the foster-brother of Herod the tetrarch, and Saul.2 And as they ministered to the Lord, and fasted, the Holy Spirit said, Separate me Barnabas and Saul for the work whereunto I have called them.3 Then, when they had fasted and prayed and laid their hands on them, they sent them away.4 So they, being sent forth by the Holy Spirit, went down to Seleucia; and from thence they sailed to Cyprus.5 And when they were at Salamis, they proclaimed the word of God in the synagogues of the Jews: and they had also John as their attendant.6 And when they had gone through the whole island unto Paphos, they found a certain sorcerer, a false prophet, a Jew, whose name was Bar-jesus;7 who was with the proconsul, Sergius Paulus, a man of understanding. The same called unto him Barnabas and Saul, and sought to hear the word of God.8 But Elymas the sorcerer (for so is his name by interpretation) withstood them, seeking to turn aside the proconsul from the faith.9 But Saul, who is also called Paul, filled with the Holy Spirit, fastened his eyes on him,10 and said, O full of all guile and all villany, thou son of the devil, thou enemy of all righteousness, wilt thou not cease to pervert the right ways of the Lord?11 And now, behold, the hand of the Lord is upon thee, and thou shalt be blind, not seeing the sun for a season. And immediately there fell on him a mist and a darkness; and he went about seeking some to lead him by the hand.12 Then the proconsul, when he saw what was done, believed, being astonished at the teaching of the Lord.13 Now Paul and his company set sail from Paphos, and came to Perga in Pamphylia: and John departed from them and returned to Jerusalem.14 But they, passing through from Perga, came to Antioch of Pisidia; and they went into the synagogue on the sabbath day, and sat down.15 And after the reading of the law and the prophets the rulers of the synagogue sent unto them, saying, Brethren, if ye have any word of exhortation for the people, say on.16 And Paul stood up, and beckoning with the hand said, Men of Israel, and ye that fear God, hearken:17 The God of this people Israel chose our fathers, and exalted the people when they sojourned in the land of Egypt, and with a high arm led he them forth out of it.18 And for about the time of forty years as a nursing-father bare he them in the wilderness.19 And when he had destroyed seven nations in the land of Canaan, he gave them their land for an inheritance, for about four hundred and fifty years:20 and after these things he gave them judges until Samuel the prophet.21 And afterward they asked for a king: and God gave unto them Saul the son of Kish, a man of the tribe of Benjamin, for the space of forty years.22 And when he had removed him, he raised up David to be their king; to whom also he bare witness and said, I have found David the son of Jesse, a man after My heart, who shall do all My will.23 Of this man’s seed hath God according to promise brought unto Israel a Saviour, Jesus;24 when John had first preached before his coming the baptism of repentance to all the people of Israel.25 And as John was fulfilling his course, he said, What suppose ye that I am? I am not he. But behold, there cometh one after me the shoes of whose feet I am not worthy to unloose.26 Brethren, children of the stock of Abraham, and those among you that fear God, to us is the word of this salvation sent forth.27 For they that dwell in Jerusalem, and their rulers, because they knew him not, nor the voices of the prophets which are read every sabbath, fulfilled them by condemning him.28 And though they found no cause of death in him, yet asked they of Pilate that he should be slain.29 And when they had fulfilled all things that were written of him, they took him down from the tree, and laid him in a tomb.30 But God raised him from the dead:31 and he was seen for many days of them that came up with him from Galilee to Jerusalem, who are now his witnesses unto the people.32 And we bring you good tidings of the promise made unto the fathers,33 that God hath fulfilled the same unto our children, in that he raised up Jesus; as also it is written in the second psalm, Thou art my Son, this day have I begotten thee.34 And as concerning that he raised him up from the dead, now no more to return to corruption, he hath spoken on this wise, I will give you the holy and sure blessings of David.35 Because he saith also in another psalm, Thou wilt not give Thy Holy One to see corruption.36 For David, after he had in his own generation served the counsel of God, fell asleep, and was laid unto his fathers, and saw corruption:37 but he whom God raised up saw no corruption.38 Be it known unto you therefore, brethren, that through this man is proclaimed unto you remission of sins:39 and by him every one that believeth is justified from all things, from which ye could not be justified by the law of Moses.40 Beware therefore, lest that come upon you which is spoken in the prophets:
41 Behold, ye despisers, and wonder, and perish; For I work a work in your days, A work which ye shall in no wise believe, if one declare it unto you.
42 And as they went out, they besought that these words might be spoken to them the next sabbath.43 Now when the synagogue broke up, many of the Jews and of the devout proselytes followed Paul and Barnabas; who, speaking to them, urged them to continue in the grace of God.44 And the next sabbath almost the whole city was gathered together to hear the word of God.45 But when the Jews saw the multitudes, they were filled with jealousy, and contradicted the things which were spoken by Paul, and blasphemed.46 And Paul and Barnabas spake out boldly, and said, It was necessary that the word of God should first be spoken to you. Seeing ye thrust it from you, and judge yourselves unworthy of eternal life, lo, we turn to the Gentiles.47 For so hath the Lord commanded us, saying, I have set thee for a light of the Gentiles, That thou shouldest be for salvation unto the uttermost part of the earth.
48 And as the Gentiles heard this, they were glad, and glorified the word of God: and as many as were ordained to eternal life believed.49 And the word of the Lord was spread abroad throughout all the region.50 But the Jews urged on the devout women of honorable estate, and the chief men of the city, and stirred up a persecution against Paul and Barnabas, and cast them out of their borders.51 But they shook off the dust of their feet against them, and came unto Iconium.52 And the disciples were filled with joy with the Holy Spirit.