A.M. 18
Bulus a Koranti
1 t Bayan haka Bulus ya tashi daga Atina ya tafi Koranti. 2 t Can ya tarar da wani Bayahude mai suna Akila, asalinsa kuwa mutumin Fantas ne, bai daɗe da zuwa daga ƙasar Italiya ba, tare da mata tasa Bilkisu, don wai Kalaudiyas ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya je wurinsu. 3 t Da yake kuma sana'arsu ɗaya ce, maɗinkan tanti ne, ya sauka a wurinsu, suka yi ta aiki tare.
4 t Ya kuma yi ta yin muhawwara a majami'a a kowace Asabar, yana ta rinjayar Yahudawa da al'ummai.
5 t Sa'ad da Sila da Timoti suka zo daga Makidoniya, Bulus ya dukufa a kan yin wa'azi, yana tabbatar wa Yahudawa, cewa Almasihu dai Yesu ne. 6 t Da suka mūsa masa, suna ta zaginsa, ya karkaɗe tufafinsa ya ce musu, “Alhakinku yana a wuyanku! Ni kam na fita. Daga yau wurin al'ummai zan je.” 7 t Sai ya tashi daga nan ya je gidan wani mutum mai suna Titus Yustus mai ibada, gidansa kuwa gab da majami'a yake. 8 t Sai Kirisbus, shugaban majami'ar ya ba da gaskiya ga Ubangiji, shi da jama'ar gidansa duka. Korantiyawa kuma da yawa da suka ji maganar Bulus suka ba da gaskiya, aka kuwa yi musu baftisma. 9 Wata rana da daddare, Ubangiji ya yi wa Bulus wahayi, ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, sai dai ka yi ta wa'azi, kada ka yi shiru, 10 t domin ina tare da kai, ba kuma wanda zai fāɗa ka ya cuce ka, domin ina da mutane da yawa a wannan birni.”
11 Sai Bulus ya zauna a nan har shekara ɗaya da wata shida, yana ta koyar da Maganar Allah a cikinsu.
12 t Amma sa'ad da Galiyo yake muƙaddashin ƙasar Akaya, Yahudawa suka tasar wa Bulus da nufi ɗaya suka kawo shi a gaban shari'a, 13 suka ce, “Mutumin nan na rarrashin mutane, wai su bauta wa Allah ta hanyar da Shari'ar ta hana.” 14 Bulus na shirin yin magana ke nan sai Galiyo ya ce wa Yahudawan, “Ku Yahudawa! Da ma wani laifi ya yi, ko munafunci, da sai in iya sauraronku. 15 t Amma tun da yake gardama ce kawai a kan kalmomi, da sunaye, da kuma shari'arku, ai, sai ku ji da ita, ku da kanku. Ni kam, ba ni da niyyar yin shari'a irin waɗannan abubuwa.” 16 Sai ya kore su daga ɗakin shari'a.
17 t Sai duk suka kama Sastanisu, shugaban majami'a, suka yi masa dūka a gaban gadon shari'a. Amma Galiyo ko yă kula.Bulus Ya Koma Antakiya ta Suriya
18 t Bulus kuwa da ya ƙara kwanaki da yawa, bayan ya sausaye kansa a Kankiriya don ya cika wa'adin da ya ɗauka, ya yi bankwana da 'yan'uwa, ya shiga jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, tare da Bilikisu da Akila. 19 t Sai suka isa Afisa, a can ne kuma ya bar su, shi kuwa ya shiga majami'a ya yi muhawwara da Yahudawa. 20 Sai suka roƙe shi ya ƙara jimawa a wurinsu, amma bai yarda ba.
21 t Sai dai ya yi bankwana da su, ya ce, “Zan dawo wurinku in Allah ya so.” Sa'an nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa.
22 t Da ya sauka a Kaisariya, sai ya je Urushalima, ya gaisa da Ikkilisiya, sa'an nan ya tafi Antakiya.
23 t Bayan da ya ɗan jima a nan, ya tashi ya zazzaga ƙasar Galatiya da ta Firijiya, yana bin gari gari, yana ƙarfafa dukan masu bi.Afolos ya Yi Wa'azi a Afisa
24 t To, wani Bayahude mai suna Afolos ya zo Afisa. Shi kuwa asalinsa mutumin Iskandariya ne, masani ne kuwa, ya san Littattafai ƙwarai da gaske. 25 t An karantar da shi tafarkin Ubangiji, da yake kuma muhimmanci ne ƙwarai, yakan yi ta magana kan al'amuran Yesu, yana kuma koyar da su sosai, amma fa baftismar Yahaya kaɗai ya sani. 26 Sai ya fara wa'azi gabagaɗi a majami'a, amma da Bilkisu da Akila suka ji maganarsa, suka ja shi a jika, suka ƙara bayyana masa tafarkin Allah sosai da sosai. 27 t Da ya so hayewa zuwa ƙasar Akaya, 'yan'uwa suka taimake shi, suka rubuta wa masu bi wasiƙa su karɓe shi hannu biyu biyu. Da kuwa ya isa, ya yi matuƙar taimako ga waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin alherin Ubangiji, 28 t don yā kayar da Yahudawa ƙwarai a gaban jama'a, yana tabbatar musu ta wurin Littattafai cewa Almasihu dai Yesu ne.
Acts 18
1 After these things he departed from Athens, and came to Corinth.2 And he found a certain Jew named Aquila, a man of Pontus by race, lately come from Italy, with his wife Priscilla, because Claudius had commanded all the Jews to depart from Rome: and he came unto them;3 and because he was of the same trade, he abode with them, and they wrought, for by their trade they were tentmakers.4 And he reasoned in the synagogue every sabbath, and persuaded Jews and Greeks.5 But when Silas and Timothy came down from Macedonia, Paul was constrained by the word, testifying to the Jews that Jesus was the Christ.6 And when they opposed themselves and blasphemed, he shook out his raiment and said unto them, Your blood be upon your own heads; I am clean: from henceforth I will go unto the Gentiles.7 And he departed thence, and went into the house of a certain man named Titus Justus, one that worshipped God, whose house joined hard to the synagogue.8 And Crispus, the ruler of the synagogue, believed in the Lord with all his house; and many of the Corinthians hearing believed, and were baptized.9 And the Lord said unto Paul in the night by a vision, Be not afraid, but speak and hold not thy peace:10 for I am with thee, and no man shall set on thee to harm thee: for I have much people in this city.11 And he dwelt there a year and six months, teaching the word of God among them.12 But when Gallio was proconsul of Achaia, the Jews with one accord rose up against Paul and brought him before the judgment-seat,13 saying, This man persuadeth men to worship God contrary to the law.14 But when Paul was about to open his mouth, Gallio said unto the Jews, If indeed it were a matter of wrong or of wicked villany, O ye Jews, reason would that I should bear with you:15 but if they are questions about words and names and your own law, look to it yourselves; I am not minded to be a judge of these matters.16 And he drove them from the judgment-seat.17 And they all laid hold on Sosthenes, the ruler of the synagogue, and beat him before the judgment-seat. And Gallio cared for none of these things.18 And Paul, having tarried after this yet many days, took his leave of the brethren, and sailed thence for Syria, and with him Priscilla and Aquila: having shorn his head in Cenchreae; for he had a vow.19 And they came to Ephesus, and he left them there: but he himself entered into the synagogue, and reasoned with the Jews.20 And when they asked him to abide a longer time, he consented not;21 but taking his leave of them, and saying, I will return again unto you if God will, he set sail from Ephesus.22 And when he had landed at Caesarea, he went up and saluted the church, and went down to Antioch.23 And having spent some time there, he departed, and went through the region of Galatia, and Phrygia, in order, establishing all the disciples.24 Now a certain Jew named Apollos, an Alexandrian by race, an eloquent man, came to Ephesus; and he was mighty in the scriptures.25 This man had been instructed in the way of the Lord; and being fervent in spirit, he spake and taught accurately the things concerning Jesus, knowing only the baptism of John:26 and he began to speak boldly in the synagogue. But when Priscilla and Aquila heard him, they took him unto them, and expounded unto him the way of God more accurately.27 And when he was minded to pass over into Achaia, the brethren encouraged him, and wrote to the disciples to receive him: and when he was come, he helped them much that had believed through grace;28 for he powerfully confuted the Jews, and that publicly, showing by the scriptures that Jesus was the Christ.