previous next

A.M. 19

Bulus a Afisa

1  t To, lokacin da Afolos yake Koranti, Bulus ya zazzaga ƙasar ta kan tudu, ya gangara zuwa Afisa. A can ya tarar da waɗansu masu bi, 2 sai ya ce musu, “Kun sami Ruhu Mai Tsarki sa'ad da kuka ba da gaskiya?” Suka ce masa, “Ba mu ma ji zuwan Ruhu Mai Tsarki ba.” 3 Sai ya ce, “To, wace baftisma ke nan aka yi muku?” Suka ce, “Irin ta Yahaya ce.” 4 t Bulus ya ce, “Ai, Yahaya baftisma ya yi a tuba, yana faɗa wa mutane su gaskata da mai zuwa bayansa, wato Yesu.” 5 Da suka ji haka, aka yi musu baftisma da sunan Ubangiji Yesu. 6 t Da Bulus ya ɗora musu hannu, Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu, suka kuwa yi magana da waɗansu harsuna, suna annabci.

7 Su wajen sha biyu ne duka duka.
8  t Sai ya shiga majami'a yana wa'azi gabagaɗi, ya kuma yi wata uku yana muhawwara da su, yana kuma rinjayarsu a kan al'amarin Mulkin Allah. 9 t Amma da waɗansu suka taurare, suka ƙi ba da gaskiya, suna kushen wannan hanya gaban jama'a, sai ya rabu da su, ya keɓe masu bi, yana ta muhawwara da su a kowace rana makarantar Tiranas.

10 t Shekara biyu ana wannan, har dukan mazaunan ƙasar Asiya suka ji Maganar Ubangiji, Yahudawa da al'ummai duka.

'Ya'yan Siba


11  t Ta hannun Bulus kuma Allah ya yi waɗansu mu'ujizai da ba a saba gani ba, 12 t har akan kai wa marasa lafiya adikansa, ko tufafinsa da yake sawa yana aiki, sun kuwa warke daga cuce-cucensu, baƙaƙen aljannu kuma sun rabu da su. 13 t Sai waɗansu Yahudawa masu yawo gari gari, matsubbata, suka yi ƙoƙarin kama sunan Ubangiji Yesu ga masu baƙaƙen aljannu, suna cewa, “Mun umarce ku da sunan Yesun nan da Bulus yake wa'azi.” 14 To, akwai 'ya'ya bakwai maza, na wani babban firist na Yahudawa, mai suna Siba, duk suna yin wannan abu. 15 Amma aljanin ya amsa musu ya ce, “Yesu dai na san shi, na kuma san Bulus, to, ku kuma ku wane ne?” 16 Mutumin nan mai aljanin sai ya daka tsalle, ya fāɗa musu, ya fi ƙarfinsu dukkansu, ya ci ɗunguminsu, har suka fita daga gidan a guje, a tuɓe, suna masu rauni. 17 t Wannan abu fa ya sanu ga dukan mazaunan Afisa, Yahudawa da al'ummai duka, duka kuma tsoro ya kama su, aka kuwa ɗaukaka sunan Ubangiji Yesu. 18 Da yawa kuma daga cikin waɗanda suka ba da gaskiya suka zo, suna bayyana ayyukansu a fili. 19 Mutane da yawa kuwa masu yin sihiri, suka tattaro littattafansu suka ƙone a gaban jama'a duka. Da suka yi wa littattafan nan kima, sai suka ga sun kai kuɗi azurfa dubu hamsin.

20 t Sai kuma Maganar Ubangiji ta ƙara haɓaka, ta kuma fifita ƙwarai.

Hargitsi a Afisa


21  t Bayan waɗannan al'amura Bulus ya ƙudura a ransa, cewa in ya zazzaga ƙasar Makidoniya da ta Akaya, za shi Urushalima, ya kuma ce, “Bayan na je can, lalle ne kuma in je in ga birnin Roma.”

22 t Da ya aiki mataimakansa biyu Makidoniya, wato Timoti da Arastas, shi kuwa ya ɗan dakata a ƙasar Asiya.
23  t A lokacin nan kuwa ba ƙaramin hargitsi aka yi game da wannan hanya ba. 24 Domin akwai wani maƙerin farfaru, mai suna Dimitiriyas, mai ƙera surorin haikalin Artimas da azurfa, ba kuwa ƙaramar riba yake jawo wa masu yin wannan sana'a ba. 25 t Sai ya tara su da duk ma'aikatan irin wannan sana'a, ya ce, “Ya ku jama'a, kun sani fa da sana'ar nan muke arziki. 26 t Kuna kuwa ji, kuna gani, ba a nan Afisa kawai ba, kusan ma a duk ƙasar Asiya, Bulus ɗin nan ya rinjayi mutane masu yawan gaske, ya juyar da su, yana cewa, allolin da mutum ya ƙera ba alloli ba ne.

27 Ga shi kuma, akwai hatsari, ba wai cinikinmu kawai ne zai zama wulakantacce ba, har ma haikalin nan na uwargijiya Artimas mai girma zai zama ba a bakin kome ba, har kuma a raba ta da darajarta, ita da duk ƙasar Asiya, kai, har duniya ma duka suke bauta wa.”
28  t Da suka ji haka suka hasala ƙwarai, suka kuma ɗaga murya gaba ɗaya suna cewa, “Girma yā tabbata ga Artimas ta Afisawa!” 29 t Sai garin duk ya ruɗe, jama'a suka ruga zuwa dandali da nufi ɗaya, suna jan Gayus da Aristarkus, mutanen Makidoniya, abokan tafiyar Bulus. 30 Bulus ya so shiga taron nan, amma masu bi suka hana shi. 31 Waɗansu zaɓaɓɓun mutanen ƙasar Asiya, waɗanda suke abokansa, su ma suka aika masa, suka roƙe shi kada ya kuskura ya shiga dandalin nan. 32 t Taron kuwa, waɗansu suka ta da murya su ce kaza, waɗansu su ce kaza, don duk taron a ruɗe yake, yawancinsu ma ba su san dalilin da ya sa suka taru ba. 33 t Da Yahudawa suka gabatar da Iskandari, waɗansu suka ɗauka a kan shi ne sanadin abin. Iskandari kuwa ya ɗaga hannu a yi shiru, don ya kawo musu hanzari,

34 amma da suka fahimci, cewa shi Bayahude ne, suka ɗaga murya gaba ɗaya har wajen sa'a biyu, suna cewa, “Girma yā tabbata ga Artimas ta Afisawa!”
35  t To, da magatakardan garin ya kwantar da hankalin jama'a, ya ce, “Ku mutanen Afisa! Wane mutum ne bai san cewa musamman birnin Afisawa ne suke kula da haikalin mai girma Artimas ba, da kuma dutsen nan da ya faɗo daga sama? 36 To, da yake ba dama a yi musun waɗannan abubuwa, ai, ya kamata ku natsu, kada ku yi kome da garaje. 37 t Ga shi, kun kawo mutanen nan, su kuwa ba su yi sata a ɗakin uwargijiya ba, ba su kuma saɓi uwargijiyarmu ba. 38 t To, in Dimitiriyas da abokan sana'arsa suna da wata magana a game da wani, ai, ga ɗakin shari'a a buɗe, ga kuma mahukunta, sai su kai ƙara. 39 Amma in wani abu kuke nema dabam, to, ai, sai a daidaita a majalisa ke nan. 40 Hakika muna cikin hatsarin amsa ƙara a kan tawaye saboda al'amarin nan na yau, tun da yake ba za mu iya ba da wani hanzari game da taron hargitsin nan ba.” 41 Da ya faɗi haka ya sallami taron.

Acts 19

1 And it came to pass, that, while Apollos was at Corinth, Paul having passed through the upper country came to Ephesus, and found certain disciples:2 and he said unto them, Did ye receive the Holy Spirit when ye believed? And they said unto him, Nay, we did not so much as hear whether the Holy Spirit was given.3 And he said, Into what then were ye baptized? And they said, Into John’s baptism.4 And Paul said, John baptized with the baptism of repentance, saying unto the people that they should believe on him that should come after him, that is, on Jesus.5 And when they heard this, they were baptized into the name of the Lord Jesus.6 And when Paul had laid his hands upon them, the Holy Spirit came on them; and they spake with tongues, and prophesied.7 And they were in all about twelve men.8 And he entered into the synagogue, and spake boldly for the space of three months, reasoning and persuading as to the things concerning the kingdom of God.9 But when some were hardened and disobedient, speaking evil of the Way before the multitude, he departed from them, and separated the disciples, reasoning daily in the school of Tyrannus.10 And this continued for the space of two years; so that all they that dwelt in Asia heard the word of the Lord, both Jews and Greeks.11 And God wrought special miracles by the hands of Paul:12 insomuch that unto the sick were carried away from his body handkerchiefs or aprons, and the evil spirits went out.13 But certain also of the strolling Jews, exorcists, took upon them to name over them that had the evil spirits the name of the Lord Jesus, saying, I adjure you by Jesus whom Paul preacheth.14 And there were seven sons of one Sceva, a Jew, a chief priest, who did this.15 And the evil spirit answered and said unto them, Jesus I know, and Paul I know, but who are ye?16 And the man in whom the evil spirit was leaped on them, and mastered both of them, and prevailed against them, so that they fled out of that house naked and wounded.17 And this became known to all, both Jews and Greeks, that dwelt at Ephesus; and fear fell upon them all, and the name of the Lord Jesus was magnified.18 Many also of them that had believed came, confessing, and declaring their deeds.19 And not a few of them that practised magical arts brought their books together and burned them in the sight of all; and they counted the price of them, and found it fifty thousand pieces of silver.20 So mightily grew the word of the Lord and prevailed.21 Now after these things were ended, Paul purposed in the spirit, when he had passed through Macedonia and Achaia, to go to Jerusalem, saying, After I have been there, I must also see Rome.22 And having sent into Macedonia two of them that ministered unto him, Timothy and Erastus, he himself stayed in Asia for a while.23 And about that time there arose no small stir concerning the Way.24 For a certain man named Demetrius, a silversmith, who made silver shrines of Diana, brought no little business unto the craftsmen;25 whom he gathered together, with the workmen of like occupation, and said, Sirs, ye know that by this business we have our wealth.26 And ye see and hear, that not alone at Ephesus, but almost throughout all Asia, this Paul hath persuaded and turned away much people, saying that they are no gods, that are made with hands:27 and not only is there danger that this our trade come into disrepute; but also that the temple of the great goddess Diana be made of no account, and that she should even be deposed from her magnificence whom all Asia and the world worshippeth.28 And when they heard this they were filled with wrath, and cried out, saying, Great is Diana of the Ephesus.29 And the city was filled with the confusion: and they rushed with one accord into the theatre, having seized Gaius and Aristarchus, men of Macedonia, Paul’s companions in travel.30 And when Paul was minded to enter in unto the people, the disciples suffered him not.31 And certain also of the Asiarchs, being his friends, sent unto him and besought him not to adventure himself into the theatre.32 Some therefore cried one thing, and some another: for the assembly was in confusion; and the more part knew not wherefore they were come together.33 And they brought Alexander out of the multitude, the Jews putting him forward. And Alexander beckoned with the hand, and would have made a defense unto the people.34 But when they perceived that he was a Jew, all with one voice about the space of two hours cried out, Great is Diana of the Ephesians.35 And when the townclerk had quieted the multitude, he saith, Ye men of Ephesus, what man is there who knoweth not that the city of the Ephesians is temple-keeper of the great Diana, and of the image which fell down from Jupiter?36 Seeing then that these things cannot be gainsaid, ye ought to be quiet, and to do nothing rash.37 For ye have brought hither these men, who are neither robbers of temples nor blasphemers of our goddess.38 If therefore Demetrius, and the craftsmen that are with him, have a matter against any man, the courts are open, and there are proconsuls: let them accuse one another.39 But if ye seek anything about other matters, it shall be settled in the regular assembly.40 For indeed we are in danger to be accused concerning this day’s riot, there being no cause for it: and as touching it we shall not be able to give account of this concourse.41 And when he had thus spoken, he dismissed the assembly.