previous next

A.M. 2

Zuwan Ruhu Mai Tsarki

1  t Da ranar Fentikos ta yi, duk suna tare a wuri ɗaya, 2 t farat ɗaya, sai aka ji wani amo daga sama, kamar na busowar gawurtacciyar iska, ya cika duk gidan da suke zaune. 3 Sai waɗansu harsuna kamar na wuta suka bayyana a gare su, suna rarrabuwa, suna sassauka a kan ko wannensu.

4 t Sai duk, aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka kuma fara magana da waɗansu harsuna dabam dabam, gwargwadon yadda Ruhun ya yi musu baiwar yin magana.
5  t To, a Urushalima a lokacin, akwai waɗansu Yahudawa masu bautar Allah daga ko'ina cikin ƙasashen duniya. 6 Da jin dirin nan kuwa, taron ya haɗe, ya ruɗe, domin ko wannensu ya ji suna magana da bakin garinsu. 7 t Sai suka yi al'ajabi suka yi mamaki, suna cewa, “Ashe, duk masu maganar nan ba Galilawa ba ne? 8 Ƙaƙa kuwa ko wannenmu yake ji da bakin garinsu ake magana? 9 t Ga mu kuwa, Fartiyawa, da Madayanawa, da Elamawa, da mutanen ƙasar Bagadaza, da na Yahudiya, da na Kafadokiya, da na Fantas, da na Asiya, 10 t da na Firijiya, da na Bamfiliya, da na Masar, da kuma na kewayen Kurane ta ƙasar Libiya, har ma da baƙi daga Roma, wato Yahudawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci, 11 da kuma Karitawa, da Larabawa, duk muna ji suna maganar manyan al'amuran Allah da bakunan garuruwanmu.” 12 Duk kuwa suka yi mamaki, suka ruɗe, suna ce wa juna, “Me ke nan kuma?”

13 t Amma waɗansu suka yi ba'a suka ce, “Ruwan inabi suka sha suka yi tatul!”

Jawabin Bitrus a Ranar Fentikos


14 Amma Bitrus ya miƙe tare da sha ɗayan nan, ya ɗaga murya ya yi musu jawabi, ya ce, “Ya ku 'yan'uwana Yahudawa da dukan mazaunan Urushalima, ku kula da wannan, ku kuma saurari maganata. 15 t Ai, mutanen nan ba bugaggu ba ne yadda kuke zato, tun da yake yanzu ƙarfe tare na safe ne kawai.

16 Wannan, ai, shi ne abin da Annabi Yowel ya faɗa cewa,

17  t ‘Allah ya ce,
A zamanin karshe zai zamanto zan zubo wa dukan 'yan adam Ruhuna.
'Ya'yanku mata da maza za su yi annabci,
Wahayi zai zo wa samarinku,
Dattawanku kuma za su yi mafarkai.

18  t Hakika, har ma a kwanakin nan zan zubo Ruhuna a kan bayina mata da maza,
Za su kuma yi annabci.

19 Zan nuna abubuwan al'ajabi a sararin sama,
Da mu'ujizai a nan ƙasa,
Wato jini, da wuta, da kuma, hauhawan hayaƙi.

20  t Za a mai da rana duhu,
Wata kuma jini,
Kafin Ranar Ubangiji ta zo,
Babbar ranar nan mai girma.

21  t A sa'an nan ne zai zamanto kowa ya yi addu'a da sunan Ubangiji zai sami ceto.’
22  t “Ya ku 'yan'uwa, Isra'ilawa, ku ji wannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar muku cewa shi yardajjensa ne, ta mu'ujizai, da abubuwan al'ajabi, da alamu waɗanda ya yi ta wurinsa a cikinku, kamar yadda ku kanku kuka sani, 23 t shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi. 24 t Amma Allah ya tashe shi bayan ya ɓalle masa ƙangin mutuwa, domin ba shi yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.

25 Dawuda kuma ya yi faɗi a game da shi ya ce,
‘Kullum hankalina yana kan Ubangiji,
Yana damana, domin kada in jijjigu.

26 Saboda haka, zuciyata ta yi fari, ina farin ciki matuƙa.
Ko da yake kuma ni jiki ne, zan zauna ina sa zuciya,

27  t Domin ba za ka yar da raina a Hades ba,
Ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.

28 Kā sanar da ni hanyoyin rai.
Za ka cika ni da farin ciki ta zamana a zatinka.’
29  t Ya 'yan'uwa, na iya yi muku magana da amincewa a game da kakanmu Dawuda, cewa ya mutu, an binne shi, kabarinsa kuma yana nan gare mu har ya zuwa yau. 30 t To, da yake shi annabi ne, ya kuma san Allah ya rantse masa, cewa zai ɗora wani daga cikin zuriya tasa kan kursiyinsa, 31 t sai ya hango, ya kuma yi faɗi a kan tashin Almasihu daga matattu, cewa ba za a yashe shi a Hades ba, jikinsa kuwa ba zai ruɓa ba. 32 t Yesun nan kam, Allah ya tashe shi daga matattu, mu kuwa duk shaidu ne ga haka. 33 t Da yake an ɗaukaka shi a dama ga Allah, ya kuma sami cikar alkawarin nan na baiwar Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, sai ya zubo da wannan da kuke gani, kuke kuma ji.

34 Ai, ba Dawuda ne ya hau Sama ba, amma shi kansa ya ce,
‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
Zauna a damana,

35  t Sai na sa ka take maƙiyanka.’

36  t “Don haka sai duk jama'ar Isra'ila su sakankance, cewa shi Yesun na da kuka gicciye, Allah ya mai da shi Ubangiji, da kuma Almasihu.”
37  t To, da suka ji haka, maganar ta soke su a zuci, suka ce wa Bitrus da sauran manzannin, “'Yan'uwa, me za mu yi?” 38 t Sai Bitrus ya ce musu, “Sai ku tuba, a yi wa ko wannenku baftisma, a kan kun yarda da sunan Yesu Almasihu, domin a gafarta zunubanku, za ku kuwa sami baiwar Ruhu Mai Tsarki, 39 t domin alkawarin nan ku aka yi wa, ku da 'ya'yanku, da kuma dukan manisanta, wato duk waɗanda Ubangiji Allahnmu ya kira.” 40 t Sai ya yi ta tabbatar musu da maganganu masu yawa, yana ta yi musu gargaɗi, yana cewa, “Ku tsirar da kanku daga wannan karkataccen zamani.” 41 Waɗanda suka ya na'am da maganarsa kuwa aka yi musu baftisma. A ran nan kuma suka ƙaru da mutum wajen dubu uku.

42 t Sai suka himmantu ga koyarwar manzanni da tarayya da juna, da gutsuttsura gurasa, da kuma yin addu'a.

Yadda Zaman Masu Bi Yake


43  t Sai tsoro ya kama kowa, aka kuma yi abubuwan al'ajabi da mu'ujizai da yawa ta wurin manzannin. 44 t Dukan masu ba da gaskiya suna tare, suna mallakar kome nasu gaba ɗaya. 45 t Suka sayar da mallakarsu da kayansu, suka rarraba wa kowa kuɗin, gwargwadon bukatarsa. 46 t Kowace rana kuma sukan riƙa zuwa Haikali da nufi ɗaya, suna gutsuttsura gurasa a gidajensu, suna cin abinci da farin ciki ƙwarai, rai kwance, 47 t suna yabon Allah, suna da farin jini a wurin dukan mutane. Kowace rana kuma Ubangiji yana ƙara masu waɗanda ake ceta.

Acts 2

1 And when the day of Pentecost was now come, they were all together in one place.2 And suddenly there came from heaven a sound as of the rushing of a mighty wind, and it filled all the house where they were sitting.3 And there appeared unto them tongues parting asunder, like as of fire; and it sat upon each one of them.4 And they were all filled with the Holy Spirit, and began to speak with other tongues, as the Spirit gave them utterance.5 Now there were dwelling at Jerusalem Jews, devout men, from every nation under heaven.6 And when this sound was heard, the multitude came together, and were confounded, because that every man heard them speaking in his own language.7 And they were all amazed and marvelled, saying, Behold, are not all these that speak Galilaeans?8 And how hear we, every man in our own language wherein we were born?9 Parthians and Medes and Elamites, and the dwellers in Mesopotamia, in Judaea and Cappadocia, in Pontus and Asia,10 in Phrygia and Pamphylia, in Egypt and the parts of Libya about Cyrene, and sojourners from Rome, both Jews and proselytes,11 Cretans and Arabians, we hear them speaking in our tongues the mighty works of God.12 And they were all amazed, and were perplexed, saying one to another, What meaneth this?13 But others mocking said, They are filled with new wine.14 But Peter, standing up with the eleven, lifted up his voice, and spake forth unto them, saying, Ye men of Judaea, and all ye that dwell at Jerusalem, be this known unto you, and give ear unto my words.15 For these are not drunken, as ye suppose; seeing it is but the third hour of the day.16 but this is that which hath been spoken through the prophet Joel:

17 And it shall be in the last days, saith God, I will pour forth of my Spirit upon all flesh: And your sons and your daughters shall prophesy, And your young men shall see visions, And your old men shall dream dreams:

18 Yea and on my servants and on my handmaidens in those days Will I pour forth of my Spirit; and they shall prophesy.

19 And I will show wonders in the heaven above, And signs on the earth beneath; Blood, and fire, and vapor of smoke:

20 The sun shall be turned into darkness, And the moon into blood, Before the day of the Lord come, That great and notable day.

21 And it shall be, that whosoever shall call on the name of the Lord shall be saved.

22 Ye men of Israel, hear these words: Jesus of Nazareth, a man approved of God unto you by mighty works and wonders and signs which God did by him in the midst of you, even as ye yourselves know;23 him, being delivered up by the determinate counsel and foreknowledge of God, ye by the hand of lawless men did crucify and slay:24 whom God raised up, having loosed the pangs of death: because it was not possible that he should be holden of it.25 For David saith concerning him, I beheld the Lord always before my face; For he is on my right hand, that I should not be moved:

26 Therefore my heart was glad, and my tongue rejoiced; Moreover my flesh also shall dwell in hope:

27 Because thou wilt not leave my soul unto Hades, Neither wilt thou give thy Holy One to see corruption.

28 Thou madest known unto me the ways of life; Thou shalt make me full of gladness with thy countenance.

29 Brethren, I may say unto you freely of the patriarch David, that he both died and was buried, and his tomb is with us unto this day.30 Being therefore a prophet, and knowing that God had sworn with an oath to him, that of the fruit of his loins he would set one upon his throne;31 he foreseeing this spake of the resurrection of the Christ, that neither was he left unto Hades, nor did his flesh see corruption.32 This Jesus did God raise up, whereof we all are witnesses.33 Being therefore by the right hand of God exalted, and having received of the Father the promise of the Holy Spirit, he hath poured forth this, which ye see and hear.34 For David ascended not into the heavens: but he saith himself, The Lord said unto my Lord, Sit thou on my right hand,

35 Till I make thine enemies the footstool of thy feet.

36 Let all the house of Israel therefore know assuredly, that God hath made him both Lord and Christ, this Jesus whom ye crucified.37 Now when they heard this, they were pricked in their heart, and said unto Peter and the rest of the apostles, Brethren, what shall we do?38 And Peter said unto them, Repent ye, and be baptized every one of you in the name of Jesus Christ unto the remission of your sins; and ye shall receive the gift of the Holy Spirit.39 For to you is the promise, and to your children, and to all that are afar off, even as many as the Lord our God shall call unto him.40 And with many other words he testified, and exhorted them, saying, Save yourselves from this crooked generation.41 They then that received his word were baptized: and there were added unto them in that day about three thousand souls.42 And they continued stedfastly in the apostles’ teaching and fellowship, in the breaking of bread and the prayers.43 And fear came upon every soul: and many wonders and signs were done through the apostles.44 And all that believed were together, and had all things common;45 and they sold their possessions and goods, and parted them to all, according as any man had need.46 And day by day, continuing stedfastly with one accord in the temple, and breaking bread at home, they took their food with gladness and singleness of heart,47 praising God, and having favor with all the people. And the Lord added to them day by day those that were saved.