A.M. 21
Tafiyar Bulus zuwa Urushalima
1 t Sa'ad da muka rabu da su da ƙyar, muka shiga jirgi muka miƙa sosai zuwa tsibirin Kos, kashegari kuma sai Rodusa, daga nan kuma sai Batara. 2 t Da muka sami jirgi mai hayewa zuwa ƙasar Finikiya, muka shiga muka tafi. 3 Da muka tsinkayo tsibirin Kubrus, muka mai da shi hagun, muka ci gaba zuwa ƙasar Suriya, muka sauka a Taya, don a nan ne jirgin zai sauke kayansa. 4 t Da muka sami inda masu bi suke, muka zauna a nan kwana bakwai. Sai Ruhu ya iza su suka gaya wa Bulus kada ya je Urushalima. 5 t Amma da lokacin tashinmu ya yi, muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu, dukansu kuma har da matansu da 'ya'yansu, suka raka mu bayan gari, sa'an nan muka durƙusa a kan gaci, muka yi addu'a, muka yi bankwana da juna.
6 Sai muka shiga jirgi, su kuma suka koma gida.
7 t Da muka gama tafiyarmu daga Taya, muka isa Talamayas, muka gaisa da 'yan'uwa, muka kuma kwana ɗaya a wurinsu. 8 t Kashegari muka tashi muka zo Kaisariya, muka shiga gidan Filibus mai yin bishara, wanda yake ɗaya daga cikin bakwai ɗin nan, muka sauka a wurinsa. 9 t Shi kuwa yana da 'ya'ya huɗu 'yan mata, masu yin annabci. 10 t To, muna nan zaune 'yan kwanaki, sai wani annabi, mai suna Agabas, ya zo daga Yahudiya. 11 t Da ya zo gare mu, ya ɗauki ɗamarar Bulus ya ɗaure kansa sawu da hannu, ya ce, “Ga abin da Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su ɗaure mai wannan ɗamara, su kuma bashe shi ga al'ummai.’ ” 12 Da muka ji haka, mu da waɗanda suke wurin muka roƙi Bulus kada ya je Urushalima. 13 t Sai Bulus ya amsa ya ce, “Me ke nan kuke yi, kuna kuka kuna baƙanta mini rai? Ai, ni a shirye nake, ba wai a ɗaure ni kawai ba, har ma a kashe ni a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”
14 Da dai ya ƙi rarrasuwa, muka yi shiru, muka ce, “Ubangiji ya yi yadda ya so.”
15 Bayan 'yan kwanakin nan muka shirya muka tafi Urushalima.
16 t Waɗansu masu bi daga Kaisariya suka rako mu, suka kawo mu wurin Manason, mutumin Kubrus, wani daɗaɗɗen mai bi, wanda za mu sauka a gunsa.Bulus Ya Ziyarci Yakubu
17 t Da muka zo Urushalima, 'yan'uwa suka karɓe mu da murna. 18 t Kashegari Bulus ya tafi tare da mu wurin Yakubu, dattawan Ikkilisiya kuwa duk suna nan. 19 t Bayan da ya gaisa da su, sai ya shiga bayyana musu filla filla abubuwan da Allah ya yi a cikin al'ummai ta wurin hidimarsa. 20 t Su kuwa da suka ji haka, suka ɗaukaka Allah. Suka ce wa Bulus, “To, kā gani ɗan'uwa, dubban mutane sun ba da gaskiya a cikin Yahudawa, dukansu kuwa masu himma ne wajen bin Shari'a. 21 t An kuwa sha gaya musu labarinka, cewa kai ne kake koya wa dukan Yahudawan da suke cikin al'ummai su yar da Shari'ar Musa. Wai kuma kana ce musu kada su yi wa 'ya'yansu kaciya, ko kuwa su bi al'adu. 22 To, ƙaƙa ke nan? Lalle za su ji labarin zuwanka. 23 t Saboda haka sai ka yi abin da za mu faɗa maka. Muna da mutum huɗu da suka ɗauki wa'adi. 24 t Sai ka tafi da su ku tsarkaka gaba ɗaya, ka kuma biya musu kome don su samu su yi aski. Ta haka, kowa zai sani duk abin da aka gaya musu game da kai, ba wata gaskiya a ciki, kai kuma kana kiyaye Shari'a. 25 t Amma game da al'ummai da suka ba da gaskiya, mun aika da wasiƙa a kan mun hukunta, cewa su guji cin abin da aka yanka wa gunki, da fasikanci, da cin abin da aka maƙure, da kuma cin nama tare da jini.”
26 t Sa'an nan Bulus ya ɗibi mutanen nan, kashegari kuma da suka tsarkaka tare, sai ya shiga Haikali domin ya sanar da ranar cikar tsarkakewar tasu, wato ranar da za a ba da sadaka saboda kowannensu.An Kama Bulus Cikin Haikali
27 t Da kwana bakwai ɗin suka yi kusan cika, Yahudawan ƙasar Asiya suka gan shi a Haikalin, sai suka zuga taron duka, suka danƙe shi, 28 t suna ihu suna cewa, “Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, ku taimaka! Ga mutumin da yake bi ko'ina yana koya wa mutane su raina jama'armu da Shari'a, da kuma wannan wuri. Banda haka kuma har ma ya kawo al'ummai a cikin Haikalin, ya ƙazantar da wurin nan tsattsarka.” 29 t Don dā ma can sun ga Tarofimas Ba'afise tare da shi a cikin gari, sun kuma zaci Bulus ya kawo shi Haikalin. 30 t Sai duk garin ya ruɗe, jama'a suka ɗungumo a guje suka danƙe Bulus, suka ja shi waje daga Haikalin, nan da nan kuma aka rufe ƙofofi. 31 Suna neman kashe shi ke nan, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar yaƙi, wai Urushalima duk ta hargitse. 32 t A nan tāke ya ɗibi soja da jarumawa, suka ruga zuwa wajensu. Su kuwa da ganin shugaban da soja suka daina dūkan Bulus. 33 t Sai shugaban ya matsa kusa ya kama Bulus, ya yi umarni a ɗaure shi da sarƙa biyu, sa'an nan ya tambaya ko shi wane ne, da abin da kuma ya yi. 34 t Taron kuwa suka ɗau kururuwa, waɗansu suka ce kaza, waɗansu suka ce kaza. Don tsananin hargowa ma har ya kasa samun ainihin tushen maganar, ya yi umarni a kai shi kagarar sojoji. 35 t Da Bulus ya zo ga bakin matakala, sai da soja suka kinkime shi saboda haukan taron,
36 t don taron jama'a na dannowa a bayansu, suna ihu suna cewa, “A yi da shi!”Hanzarin Bulus
37 t An yi kusan shigar da Bulus kagarar sojoji ke nan, sai ya ce wa shugaban, “Ko ka yarda in yi magana da kai?” Sai shugaban ya ce, “Ashe, ka iya Helenanci? 38 t Shin, ba kai ne Bamasaren nan da shekarun baya ya haddasa tawaye ba, har ya ja mutanen nan dubu huɗu masu kisankai jeji?” 39 t Sai Bulus ya amsa ya ce, “Ai, ni Bayahude ne na Tarsus ta ƙasar Kilikiya, ɗan shahararren birni, ina roƙonka ka bar ni in yi wa mutane jawabi.” 40 t Da ya ba shi izini, sai Bulus ya tsaya a kan matakala, ya ɗaga wa jama'a hannu su yi shiru. Da suka yi tsit, sai ya yi musu magana da Yahudanci.
Acts 21
1 And when it came to pass that were parted from them and had set sail, we came with a straight course unto Cos, and the next day unto Rhodes, and from thence unto Patara:2 and having found a ship crossing over unto Phoenicia, we went aboard, and set sail.3 And when we had come in sight of Cyprus, leaving it on the left hand, we sailed unto Syria, and landed at Tyre; for there the ship was to unlade her burden.4 And having found the disciples, we tarried there seven days: and these said to Paul through the Spirit, that he should not set foot in Jerusalem.5 And when it came to pass that we had accomplished the days, we departed and went on our journey; and they all, with wives and children, brought us on our way till we were out of the city: and kneeling down on the beach, we prayed, and bade each other farewell;6 and we went on board the ship, but they returned home again.7 And when we had finished the voyage from Tyre, we arrived at Ptolemais; and we saluted the brethren, and abode with them one day.8 And on the morrow we departed, and came unto Caesarea: and entering into the house of Philip the evangelist, who was one of the seven, we abode with him.9 Now this man had four virgin daughters, who prophesied.10 And as we tarried there some days, there came down from Judaea a certain prophet, named Agabus.11 And coming to us, and taking Paul’s girdle, he bound his own feet and hands, and said, Thus saith the Holy Spirit, So shall the Jews at Jerusalem bind the man that owneth this girdle, and shall deliver him into the hands of the Gentiles.12 And when we heard these things, both we and they of that place besought him not to go up to Jerusalem.13 Then Paul answered, What do ye, weeping and breaking my heart? for I am ready not to be bound only, but also to die at Jerusalem for the name of the Lord Jesus.14 And when he would not be persuaded, we ceased, saying, The will of the Lord be done.15 And after these days we took up our baggage and went up to Jerusalem.16 And there went with us also certain of the disciples from Caesarea, bringing with them one Mnason of Cyprus, an early disciple, with whom we should lodge.17 And when we were come to Jerusalem, the brethren received us gladly.18 And the day following Paul went in with us unto James; and all the elders were present.19 And when he had saluted them, he rehearsed one by one the things which God had wrought among the Gentiles through his ministry.20 And they, when they heard it, glorified God; and they said unto him, Thou seest, brother, how many thousands there are among the Jews of them that have believed; and they are all zealous for the law:21 and they have been informed concerning thee, that thou teachest all the Jews who are among the Gentiles to forsake Moses, telling them not to circumcise their children neither to walk after the customs.22 What is it therefore? They will certainly hear that thou art come.23 Do therefore this that we say to thee: We have four men that have a vow on them;24 these take, and purify thyself with them, and be at charges for them, that they may shave their heads: and all shall know that there is no truth in the things whereof they have been informed concerning thee; but that thou thyself also walkest orderly, keeping the law.25 But as touching the Gentiles that have believed, we wrote, giving judgment that they should keep themselves from things sacrificed to idols, and from blood, and from what is strangled, and from fornication.26 Then Paul took the men, and the next day purifying himself with them went into the temple, declaring the fulfilment of the days of purification, until the offering was offered for every one of them.27 And when the seven days were almost completed, the Jews from Asia, when they saw him in the temple, stirred up all the multitude and laid hands on him,28 crying out, Men of Israel, help: This is the man that teacheth all men everywhere against the people, and the law, and this place; and moreover he brought Greeks also into the temple, and hath defiled this holy place.29 For they had before seen with him in the city Trophimus the Ephesian, whom they supposed that Paul had brought into the temple.30 And all the city was moved, and the people ran together; and they laid hold on Paul, and dragged him out of the temple: and straightway the doors were shut.31 And as they were seeking to kill him, tidings came up to the chief captain of the band, that all Jerusalem was in confusion.32 And forthwith he took soldiers and centurions, and ran down upon them: and they, when they saw the chief captain and the soldiers, left off beating Paul.33 Then the chief captain came near, and laid hold on him, and commanded him to be bound with two chains; and inquired who he was, and what he had done.34 And some shouted one thing, some another, among the crowd: and when he could not know the certainty for the uproar, he commanded him to be brought into the castle.35 And when he came upon the stairs, so it was that he was borne of the soldiers for the violence of the crowd;36 for the multitude of the people followed after, crying out, Away with him.37 And as Paul was about to be brought into the castle, he saith unto the chief captain, May I say something unto thee? And he said, Dost thou know Greek?38 Art thou not then the Egyptian, who before these days stirred up to sedition and led out into the wilderness the four thousand men of the Assassins?39 But Paul said, I am a Jew, of Tarsus in Cilicia, a citizen of no mean city: and I beseech thee, give me leave to speak unto the people.40 And when he had given him leave, Paul, standing on the stairs, beckoned with the hand unto the people; and when there was made a great silence, he spake unto them in the Hebrew language, saying,