A.M. 5
Hananiya da Safiratu
1 Amma wani mutum mai suna Hananiya, da mata tasa Safiratu, ya sayar da wata mallaka tasa, 2 t sai ya ɓoye wani abu daga cikin kuɗin, da sanin matarsa, ya kawo sashin kuɗin kurum ya ajiye a gaban manzanni. 3 t Sai Bitrus ya ce, “Kai, Hananiya, ta ƙaƙa Shaiɗan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya, ka kuma ɓoye wani abu daga kuɗin gonar? 4 Kafin ka sayar, ba taka ba ce? Bayan ka sayar kuma, kuɗin ba halalinka ba ne? Ta ƙaƙa ka riya wannan aiki a zuciyarka? Ai, ba mutum ka yi wa ƙarya ba, Allah ka yi wa.” 5 t Da jin wannan magana Hananiya ya fāɗi ya mutu. Duk waɗanda suka ji kuwa, matsanancin tsoro ya kama su.
6 t Samari suka taso, suka sa shi a likkafani, suka ɗauke shi suka fitar da shi, suka je suka binne shi.
7 Bayan misalin sa'a uku mata tasa ta shigo, ba da sanin abin da ya faru ba. 8 t Sai Bitrus ya ce mata, “Gaya mini, shin, haka kuka sayar da gonar nan?” Sai ta ce, “I, haka ne.” 9 t Amma Bitrus ya ce mata, “Ƙaƙa kuka gama baki ku gwada Ruhun Ubangiji? Kin ji tafiyar waɗanda suka binne mijinki, har sun iso bakin ƙofa ma, za su kuwa ɗauke ki, su fitar da ke.” 10 t Nan tāke, ta fāɗi a gabansa, ta mutu. Da dai samarin suka shigo, suka iske ta matacciya, suka ɗauke ta suka fitar da ita, suka binne ta a jikin mijinta.
11 t Sai matsanancin tsoro ya kama dukan Ikkilisiyar, da kuma dukan waɗanda suka ji labarin waɗannan abubuwa.An Yi Mu'ujizai da Abubuwan Al'ajabi Masu Yawa
12 t To, an yi mu'ujizai da abubuwan al'ajabi masu yawa a cikin mutane ta hannun manzanni. Dukansu kuwa da nufi ɗaya sukan taru a Shirayin Sulemanu. 13 t Amma a cikin sauran mutane ba wanda ya yi ƙarfin halin shiga cikinsu, duk da haka kuwa jama'a suna girmama su. 14 Masu ba da gaskiya sai ƙaruwa suke ta yi ga Ubangiji fiye da dā, jama'a masu yawan gaske mata da maza. 15 t Har ma ya kai ga suna fito da marasa lafiya tafarku, suna shimfiɗa su a kan gadaje da tabarmi, don in Bitrus ya zo wucewa, ko da inuwa tasa ma ta bi ta kan waɗansunsu.
16 t Mutane kuwa suka yi ta taruwa daga garuruwan da suke kewayen Urushalima, suna ta kawo marasa lafiya da waɗanda baƙaƙen aljannu suke wahalshe su, dukansu kuwa aka warkar da su.An Tsananta wa Manzanni
17 t Amma babban firist ya taso, da duk waɗanda suke tare da shi, wato 'yan ɗariƙa Sadukiyawa, suna kishi gaya, 18 t suka kama manzannin, suka sa su kurkuku. 19 t Amma da daddare sai wani mala'ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun, ya fito da su, ya ce, 20 t “Ku tafi, ku tsaya a cikin Haikali, ku sanar da jama'a duk maganar wannan rai.”
21 t Da suka ji haka, suka shiga Haikalin da sassafe, suna koyarwa.
To, babban firist ya fito, shi da waɗanda suke tare da shi, suka kira majalisa, da dukan shugabannin Isra'ilawa, suka aika kurkuku a kawo su. 22 Amma da dogaran Haikali suka je, ba su same su a kurkukun ba, suka dawo suka ba da labari, suka ce, 23 “Mun iske kurkukun a kulle sosai, masu tsaro kuma na tsaro a bakin ƙofofin, amma da muka buɗe, sai muka tarar ba kowa a ciki.” 24 t To, da shugaban dogaran Haikali da manyan firistocin suka ji haka, suka ruɗe ƙwarai a game da su, suka rasa inda abin zai kai. 25 Sai wani ya zo ya ce musu, “Ai, ga shi, mutanen nan da kuka sa a kurkuku suna nan a tsaye a Haikali, suna koya wa jama'a.”
26 t Sai shugaban dogaran Haikali da dogaran suka je suka kawo manzannin, amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada jama'a su jejjefe su da duwatsu.
27 t Da suka kawo su, suka tsai da su a gaban majalisar. Sai babban firist ya tambaye su, 28 t ya ce, “Mun fa kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa da sunan nan, amma ga shi, kun gama Urushalima da koyarwarku, har ma kuna nema ku ɗafa mana alhakin jinin mutumin nan.” 29 t Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum. 30 t Allahn kakanninmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe ta wurin kafe shi a jikin gungume. 31 t Shi ne Allah ya ɗaukaka ga damansa, Shugaba da kuma Mai Ceto, domin ya buɗe wa Isra'ila hanyar tuba, su kuma sami gafarar zunubansu.
32 t Mu kuwa shaidu ne ga waɗannan al'amura, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya bai wa masu yi masa biyayya.”
33 t Da suka ji haka, sai suka husata ƙwarai da gaske, suna so su kashe su. 34 t Amma wani Bafarisiye, wai shi Gamaliyal, masanin Attaura, wanda duk jama'a suke girmamawa, ya miƙe cikin majalisa, ya yi umarni a fitar da mutanen nan waje tukuna. 35 Sa'an nan ya ce musu, “Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, ku kula fa da abin da kuke niyyar yi wa mutanen nan. 36 Shekarun baya wani mutum ya ɓullo, wai shi Tudas, yana mai da kansa wani abu, wajen mutum arbaminya kuma suka bi shi, amma aka kashe shi, mabiyansa kuwa aka watsa su, suka lalace. 37 t Bayansa kuma, a lokacin ƙirgen mutane, wai shi Yahuza Bagalile ya ɓullo, ya zuga waɗansu suka yi turu, suka bi shi. Shi ma ya hallaka, duk mabiyansa ma aka warwatsa su. 38 t To, yanzu ma, ina gaya muku, ku fita sha'anin mutanen nan, ku ƙyale su. Idan dai niyyarsu ko aikinsu na mutum ne, ai, zai rushe,
39 t amma in na Allah ne, ba dama ku rushe su. Kada fa a same ku kuna gāba da Allah.”
40 t Sai suka bi shawara tasa, suka kuma kirawo manzannin, suka yi musu dūka, suka kwaɓe su kada su ƙara magana da sunan Yesu, sa'an nan suka sake su. 41 t To, suka tashi daga gaban majalisar, suna farin ciki a kan an ga sun isa su sha wulakanci saboda sunan Yesu. 42 t Kowace rana kuwa, ko a Haikali ko a gida, ba su daina koyarwa da yin bishara, cewa Yesu shi ne Almasihu ba.
Acts 5
1 But a certain man named Ananias, with Sapphira his wife, sold a possession,2 and kept back part of the price, his wife also being privy to it, and brought a certain part, and laid it at the apostles’ feet.3 But Peter said, Ananias, why hath Satan filled thy heart to lie to the Holy Spirit, and to keep back part of the price of the land?4 While it remained, did it not remain thine own? and after it was sold, was it not in thy power? How is it that thou hast conceived this thing in thy heart? thou has not lied unto men, but unto God.5 And Ananias hearing these words fell down and gave up the ghost: and great fear came upon all that heard it.6 And the young men arose and wrapped him round, and they carried him out and buried him.7 And it was about the space of three hours after, when his wife, not knowing what was done, came in.8 And Peter answered unto her, Tell me whether ye sold the land for so much. And she said, Yea, for so much.9 But Peter said unto her, How is it that ye have agreed together to try the Spirit of the Lord? behold, the feet of them that have buried thy husband are at the door, and they shall carry thee out.10 And she fell down immediately at his feet, and gave up the ghost: and the young men came in and found her dead, and they carried her out and buried her by her husband.11 And great fear came upon the whole church, and upon all that heard these things.12 And by the hands of the apostles were many signs and wonders wrought among the people; and they were all with one accord in Solomon’s porch.13 But of the rest durst no man join himself to them: howbeit the people magnified them;14 and believers were the more added to the Lord, multitudes both of men and women;15 insomuch that they even carried out the sick into the streets, and laid them on beds and couches, that, as Peter came by, at the least his shadow might overshadow some one of them.16 And there also came together the multitudes from the cities round about Jerusalem, bring sick folk, and them that were vexed with unclean spirits: and they were healed every one.17 But the high priest rose up, and all they that were with him (which is the sect of the Sadducees), and they were filled with jealousy,18 and laid hands on the apostles, and put them in public ward.19 But an angel of the Lord by night opened the prison doors, and brought them out, and said,20 Go ye, and stand and speak in the temple to the people all the words of this Life.21 And when they heard this, they entered into the temple about daybreak, and taught. But the high priest came, and they that were with him, and called the council together, and all the senate of the children of Israel, and sent to the prison-house to have them brought.22 But the officers that came found them not in the prison; and they returned, and told,23 saying, The prison-house we found shut in all safety, and the keepers standing at the doors: but when we had opened, we found no man within.24 Now when the captain of the temple and the chief priests heard these words, they were much perplexed concerning them whereunto this would grow.25 And there came one and told them, Behold, the men whom ye put in the prison are in the temple standing and teaching the people.26 Then went the captain with the officers, and brought them, but without violence; for they feared the people, lest they should be stoned.27 And when they had brought them, they set them before the council. And the high priest asked them,28 saying, We strictly charged you not to teach in this name: and behold, ye have filled Jerusalem with your teaching, and intend to bring this man’s blood upon us.29 But Peter and the apostles answered and said, We must obey God rather than men.30 The God of our fathers raised up Jesus, whom ye slew, hanging him on a tree.31 Him did God exalt with his right hand to be a Prince and a Saviour, to give repentance to Israel, and remission of sins.32 And we are witnesses of these things; and so is the Holy Spirit, whom God hath given to them that obey him.33 But they, when they heard this, were cut to the heart, and minded to slay them.34 But there stood up one in the council, a Pharisee, named Gamaliel, a doctor of the law, had in honor of all the people, and commanded to put the men forth a little while.35 And he said unto them, Ye men of Israel, take heed to yourselves as touching these men, what ye are about to do.36 For before these days rose up Theudas, giving himself out to be somebody; to whom a number of men, about four hundred, joined themselves: who was slain; and all, as many as obeyed him, were dispersed, and came to nought.37 After this man rose up Judas of Galilee in the days of the enrolment, and drew away some of the people after him: he also perished; and all, as many as obeyed him, were scattered abroad.38 And now I say unto you, Refrain from these men, and let them alone: for if this counsel or this work be of men, it will be overthrown:39 but if it is of God, ye will not be able to overthrow them; lest haply ye be found even to be fighting against God.40 And to him they agreed: and when they had called the apostles unto them, they beat them and charged them not to speak in the name of Jesus, and let them go.41 They therefore departed from the presence of the council, rejoicing that they were counted worthy to suffer dishonor for the Name.42 And every day, in the temple and at home, they ceased not to teach and to preach Jesus as the Christ.