A.M. 6
Zaɓen Mutum Bakwai Masu Hidima
1 t To, a kwanakin nan da yawan masu bi suke Ƙaruwa, sai Yahudawa masu jin Helenanci suka yi wa Ibraniyawa gunaguni domin bā a kula da matayensu waɗanda mazansu suka mutu, a wajen rabon gudunmawa a kowace rana. 2 Sai goma sha biyun nan suka kirawo duk jama'ar masu bi, suka ce, “Ai, bai kyautu ba mu mu bar wa'azin Maganar Allah, mu shagala a kan sha'anin abinci. 3 t Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku, waɗanda ake yabawa, cike da Ruhu da kuma hikima, waɗanda za mu danƙa wa wannan aiki. 4 t Mu kuwa sai mu nace da yin addu'a da kuma koyar da Maganar.” 5 t Abin da suka faɗa kuwa ya ƙayatar da jama'a duka. Sai suka zaɓi Istifanas, mutumin da yake cike da bangaskiya da Ruhu Mai Tsarki, da Filibus, da Burokoras, da Nikanar, da Timan, da Barminas, da Nikolas mutumin Antakiya wanda dā ya shiga Yahudanci.
6 t Waɗannan ne aka gabatar a gaban manzannin. Bayan sun yi addu'a kuma, suka ɗora musu hannu.
7 t Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka take yi, yawan masu bi kuma a birnin Urushalima sai ta ƙaruwa yake yi ƙwarai da gaske, firistoci masu yawan gaske kuma suka yi na'am da bangaskiyar nan.An Kama Istifanas
8 t To, Istifanas, cike da alheri da iko, ya yi ta yin manyan al'ajabai da mu'ujizai a cikin jama'a. 9 t Sa'an nan waɗansu na majami'ar da ake kira majami'ar Libartinawa, wato Kuraniyawa da Iskandariyawa, da kuma waɗansu daga ƙasar Kilikiya da ta Asiya, suka tasar wa Istifanas da muhawwara. 10 t Amma ko kaɗan ba dama su yi masa mūsu, domin ya yi magana da hikima, Ruhu na iza shi. 11 t Sai suka zuga mutane a asirce, su kuwa suka ce, “Mun ji shi yana zagin Musa, yana saɓon Allah.” 12 t Ta haka suka ta da hankalin jama'a, da shugabanni, da malaman Attaura, su kuma suka aukar masa, suka kama shi, suka kawo shi a gaban majalisa. 13 t Sai suka gabatar da masu shaidar zur, suka ce, “Mutumin nan ba ya rabuwa da kushe tsattsarkan wurin nan, da kuma Attaura, 14 t don mun ji shi yana cewa wai wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan, yă kuma sauya al'adun da Musa ya bar mana.” 15 t Da duk waɗanda suke zaune a majalisar suka zura masa ido, suka ga fuska tasa kamar fuskar mala'ika take.
Acts 6
1 Now in these days, when the number of the disciples was multiplying, there arose a murmuring of the Grecian Jews against the Hebrews, because their widows were neglected in the daily ministration.2 And the twelve called the multitude of the disciples unto them, and said, It is not fit that we should forsake the word of God, and serve tables.3 Look ye out therefore, brethren, from among you seven men of good report, full of the Spirit and of wisdom, whom we may appoint over this business.4 But we will continue stedfastly in prayer, and in the ministry of the word.5 And the saying pleased the whole multitude: and they chose Stephen, a man full of faith and of the Holy Spirit, and Philip, and Prochorus, and Nicanor, and Timon, and Parmenas, and Nicolaus a proselyte of Antioch;6 whom they set before the apostles: and when they had prayed, they laid their hands upon them.7 And the word of God increased; and the number of the disciples multiplied in Jerusalem exceedingly; and a great company of the priests were obedient to the faith.8 And Stephen, full of grace and power, wrought great wonders and signs among the people.9 But there arose certain of them that were of the synagogue called the synagogue of the Libertines, and of the Cyrenians, and of the Alexandrians, and of them of Cilicia and Asia, disputing with Stephen.10 And they were not able to withstand the wisdom and the Spirit by which he spake.11 Then they suborned men, who said, We have heard him speak blasphemous words against Moses, and against God.12 And they stirred up the people, and the elders, and the scribes, and came upon him, and seized him, and brought him into the council,13 and set up false witnesses, who said, This man ceaseth not to speak words against this holy place, and the law:14 for we have heard him say, that this Jesus of Nazareth shall destroy this place, and shall change the customs which Moses delivered unto us.15 And all that sat in the council, fastening their eyes on him, saw his face as it had been the face of an angel.