previous next

A.M. 9

Juyowar Shawulu

(A.M. 22.6-16; 26.12-18)

1  t Shawulu kuwa yana kan tsananta kashedi da gāba da masu bin Ubangiji, cewa zai kashe su, sai ya je wurin babban firist, 2 t ya roƙe shi ya yi masa wasiƙu zuwa majami'un Dimashƙu, don in ya sami masu bin wannan hanya, mata ko maza, yă zo da su birnin Urushalima a ɗaure. 3 t Yana tafiya ke nan, ya yi kusa da Dimashƙu, ba zato sai ga wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi. 4 Sai ya fāɗi, ya kuma ji wata murya tana ce masa, “Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?” 5 Shi kuma ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Sai ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa. 6 t Amma ka tashi ka shiga gari, can za a faɗa maka abin da za ka yi.” 7 t Abokan tafiyarsa kuwa suka rasa bakin magana, suna jin muryar, amma ba su ga kowa ba. 8 Sai Shawulu ya tashi, amma da ya buɗe ido ya kasa gani. Sai aka yi masa jagora, aka kai shi Dimashƙu.

9 Kwanansa uku ba ya gani, ba ya kuma ci, ba ya sha.
10  t To, akwai wani mai bi a Dimashƙu, mai suna Hananiya. Ubangiji ya yi masa magana cikin wahayi ya ce, “Hananiya.” Shi kuwa ya ce, “Na'am, ya Ubangiji.” 11 t Sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi ka tafi titin nan da ake kira Miƙaƙƙiye, ka tambaya a gidan Yahuza, ko akwai wani mutumin Tarsus, mai suna Shawulu, ga shi nan, yana addu'a, 12 t har ma a cikin wahayi ya ga wani mutum, mai suna Hananiya, ya shigo ya ɗora masa hannu, don ya sāke samun ganin gari.” 13 t Amma Hananiya ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, na sha jin labarin mutumin nan gun mutane da yawa, kan yawan muguntar da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima. 14 t Ga shi kuma manyan firistoci sun ba shi izini ya ɗaure duk mai yin addu'a da sunan har a nan ma.” 15 t Amma Ubangiji ya ce masa, “Kai dai, je ka, domin shi ma'aikacina ne zaɓaɓɓe, domin yă sanar da sunana ga al'ummai, da sarakuna, da kuma Isra'ilawa. 16 t Domin zan sanar da shi yawan wuyar da lalle zai sha saboda sunana.” 17 t Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Da ya ɗora masa hannu, ya ce, “Ya ɗan'uwana Shawulu, Ubangiji ne ya aiko ni, wato Yesu, wanda ya bayyana a gare ka a kan hanyar da ka biyo, domin ka sāke gani, a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.” 18 Nan take sai wani abu kamar ɓawo ya faɗo daga idanunsa, sai ya sāke gani. Sa'an nan ya tashi, aka yi masa baftisma.

19 t Sai ya ci abinci, ƙarfinsa kuma ya komo.

Shawulu Ya Yi Wa'azi a Dimashƙu


Shawulu kuwa ya yi 'yan kwanaki tare da masu bi da suke Dimashƙu. 20 t Nan da nan ya fara wa'azin Yesu a majami'unsu, cewa shi ne Ɗan Allah. 21 t Duk waɗanda suka ji shi, suka yi ta al'ajabi, suka ce, “Ashe, ba wannan ne ya watsa masu yin addu'a da sunan nan a Urushalima ba? Ya zo nan ne ma da niyyar ya kai su gaban manyan firistoci a ɗaure.”

22 t Sai Shawulu ya ƙara ƙarfafa, yana ta dama hankalin Yahudawan da suke zaune a Dimashƙu, yana tabbatarwa, cewa Yesu shi ne Almasihu.

Shawulu Ya Kuɓuce wa Yahudawa


23 Bayan an ɗan daɗe Yahudawa suka ƙulla shawara su kashe shi. 24 t Amma Shawulu ya sami labarin makircinsu. Dare da rana suna fako a ƙofofin gari don su kashe shi,

25 t amma da daddare almajiransa suka tafi da shi, suka zura shi ta wata taga a jikin garu cikin babban kwando.

Shawulu a Urushalima


26  t Da ya zo Urushalima ya yi ƙoƙarin shiga cikin masu bi, amma duk suka ji tsoronsa, don ba su gaskata shi mai bi ba ne. 27 t Amma Barnaba ya kama hannunsa ya kai shi wurin manzannin, ya gaya musu yadda Shawulu ya ga Ubangiji a hanya, da yadda Ubangiji ya yi masa magana, da kuma yadda ya yi wa'azi gabagaɗi da sunan Yesu a Dimashƙu. 28 Daga nan ya yi ta cuɗanya da su a Urushalima, 29 t yana wa'azi gabagaɗi da sunan Ubangiji. Ya kuma riƙa magana da Yahudawa masu jin Helenanci, yana muhawwara da su, amma suka yi ta neman kashe shi.

30 t Da 'yan'uwa suka fahimci haka, suka kawo shi Kaisariya, suka aika da shi Tarsus.

31  t Sa'an nan ne Ikkilisiyar duk ƙasar Yahudiya, da ta Galili, da ta Samariya ta sami lafiya, ta ingantu sosai, suna tafiyar da al'amuransu da tsoron Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki na taimakonsu, har suka yawaita.

An Warkar da Iniyasu


32  t To, da Bitrus ya zazzaga lardi duka, sai kuma ya je wurin tsarkakan nan da suke zaune a Lidda. 33 Nan ya tarar da wani mutum, mai suna Iniyasu, wanda yake kwance a kan gado shekara takwas, yana shanyayye. 34 t Sai Bitrus ya ce masa, “Iniyasu, Yesu Almasihu ya warkar da kai. Tashi ka kintsa gadonka.” A nan tāke ya tashi.

35 t Duk mutanen Lidda da na ƙasar Sarona kuwa suka gan shi, suka juyo ga Ubangiji.

Bitrus Ya Ta Da Tabita daga Matattu


36  t A Yafa kuwa akwai wata mai bi, mai suna Tabita, wato Dokas ke nan. Matar nan kuwa lazimar aiki nagari ce, da kuma gudunmawa. 37 t A lokacin nan ta yi rashin lafiya, ta mutu. Da suka yi mata wanka, suka shimfiɗe ta a kan bene. 38 t Da yake Lidda kusa da yafa take, da masu bi suka ji Bitrus na can, suka aiki mutum biyu wurinsa, su roƙe shi ya zo wurinsu ba da jinkiri ba. 39 t Sai Bitrus ya tashi ya tafi tare da su. Da ya iso suka kai shi benen. Dukan mata waɗanda mazansu suka mutu suka tsaya kusa da shi, suna kuka, suna nunnuna riguna da tufafi da Dokas ta yi musu tun suna tare. 40 t Amma Bitrus ya fitar da su duka waje, ya durƙusa, ya yi addu'a. Ya juya wajen gawar, ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe ido, da ta ga Bitrus, ta tashi zaune. 41 Ya kuwa miƙa mata hannu ya tashe ta. Sai ya kira tsarkaka da matan waɗanda mazansu suka mutu ya miƙa musu ita rayayyiya. 42 Labari ya bazu a dukan Yafa, mutane da yawa kuwa suka gaskata da Ubangiji. 43 t To, ya zauna kwanaki da yawa a Yafa a gidan wani majemi mai suna Saminu.

Acts 9

1 But Saul, yet breathing threatening and slaughter against the disciples of the Lord, went unto the high priest,2 and asked of him letters to Damascus unto the synagogues, that if he found any that were of the Way, whether men or women, he might bring them bound to Jerusalem.3 And as he journeyed, it came to pass that he drew nigh unto Damascus: and suddenly there shone round about him a light out of heaven:4 and he fell upon the earth, and heard a voice saying unto him, Saul, Saul, why persecutest thou me?5 And he said, Who art thou, Lord? And he said, I am Jesus whom thou persecutest:6 but rise, and enter into the city, and it shall be told thee what thou must do.7 And the men that journeyed with him stood speechless, hearing the voice, but beholding no man.8 And Saul arose from the earth; and when his eyes were opened, he saw nothing; and they led him by the hand, and brought him into Damascus.9 And he was three days without sight, and did neither eat nor drink.10 Now there was a certain disciple at Damascus, named Ananias; and the Lord said unto him in a vision, Ananias. And he said, Behold, I am here, Lord.11 And the Lord said unto him, Arise, and go to the street which is called Straight, and inquire in the house of Judas for one named Saul, a man of Tarsus: for behold, he prayeth;12 and he hath seen a man named Ananias coming in, and laying his hands on him, that he might receive his sight.13 But Ananias answered, Lord, I have heard from many of this man, how much evil he did to thy saints at Jerusalem:14 and here he hath authority from the chief priests to bind all that call upon thy name.15 But the Lord said unto him, Go thy way: for he is a chosen vessel unto me, to bear my name before the Gentiles and kings, and the children of Israel:16 for I will show him how many things he must suffer for my name’s sake.17 And Ananias departed, and entered into the house; and laying his hands on him said, Brother Saul, the Lord, even Jesus, who appeared unto thee in the way which thou camest, hath sent me, that thou mayest receive thy sight, and be filled with the Holy Spirit.18 And straightway there fell from his eyes as it were scales, and he received his sight; and he arose and was baptized;19 and he took food and was strengthened. And he was certain days with the disciples that were at Damascus.20 And straightway in the synagogues he proclaimed Jesus, that he is the Son of God.21 And all that heard him were amazed, and said, Is not this he that in Jerusalem made havoc of them that called on this name? and he had come hither for this intent, that he might bring them bound before the chief priests.22 But Saul increased the more in strength, and confounded the Jews that dwelt at Damascus, proving that this is the Christ.23 And when many days were fulfilled, the Jews took counsel together to kill him:24 but their plot became known to Saul. And they watched the gates also day and night that they might kill him:25 but his disciples took him by night, and let him down through the wall, lowering him in a basket.26 And when he was come to Jerusalem, he assayed to join himself to the disciples: and they were all afraid of him, not believing that he was a disciple.27 But Barnabas took him, and brought him to the apostles, and declared unto them how he had seen the Lord in the way, and that he had spoken to him, and how at Damascus he had preached boldly in the name of Jesus.28 And he was with them going in and going out at Jerusalem,29 preaching boldly in the name of the Lord: and he spake and disputed against the Grecian Jews; but they were seeking to kill him.30 And when the brethren knew it, they brought him down to Caesarea, and sent him forth to Tarsus.31 So the church throughout all Judaea and Galilee and Samaria had peace, being edified; and, walking in the fear of the Lord and in the comfort of the Holy Spirit, was multiplied.32 And it came to pass, as Peter went throughout all parts, he came down also to the saints that dwelt at Lydda.33 And there he found a certain man named Aeneas, who had kept his bed eight years; for he was palsied.34 And Peter said unto him, Aeneas, Jesus Christ healeth thee: arise and make thy bed. And straightway he arose.35 And all that dwelt at Lydda and in Sharon saw him, and they turned to the Lord.36 Now there was at Joppa a certain disciple named Tabitha, which by interpretation is called Dorcas: this woman was full of good works and almsdeeds which she did.37 And it came to pass in those days, that she fell sick, and died: and when they had washed her, they laid her in an upper chamber.38 And as Lydda was nigh unto Joppa, the disciples, hearing that Peter was there, sent two men unto him, entreating him, Delay not to come on unto us.39 And Peter arose and went with them. And when he was come, they brought him into the upper chamber: and all the widows stood by him weeping, and showing the coats and garments which Dorcas made, while she was with them.40 But Peter put them all forth, and kneeled down and prayed; and turning to the body, he said, Tabitha, arise. And she opened her eyes; and when she saw Peter, she sat up.41 And he gave her his hand, and raised her up; and calling the saints and widows, he presented her alive.42 And it became known throughout all Joppa: and many believed on the Lord.43 And it came to pass, that he abode many days in Joppa with one Simon a tanner.