KOL 1
Gaisuwa
1 t Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, tare da Timoti, ɗan'uwanmu,
2 t zuwa ga tsarkaka da amintattun 'yan'uwa cikin Almasihu da suke a Kolosi.
Alheri da salamar Allah Ubanmu su tabbata a gare ku.Addu'ar Bulus domin Kolosiyawa Masu Bin Almasihu
3 t A kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu, duk sa'ad da muke yi muku addu'a, 4 t saboda mun ji labarin bangaskiyarku ga Almasihu Yesu, da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan tsarkaka, 5 t saboda bege ga abin da aka tanadar muku a sama. Kun riga kun ji labarin wannan a maganar gaskiya, 6 t wato, bisharar da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda take yi a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji, kuka kuma fahimci alherin Allah na hakika. 7 t Haka ma kuka koya wurin Abafaras, ƙaunataccen abokin bautarmu. Shi amintaccen mai hidima ne na Almasihu a madadinmu,
8 t ya kuma sanasshe mu ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu.
9 t Shi ya sa tun a ran da muka ji labarin, ba mu fāsa yi muku addu'a ba, muna roƙo a cika ku da sanin nufin Allah da matuƙar hikima da fahimta na ruhu, 10 t domin ku yi zaman da ya cancanci bautar Ubangiji, kuna faranta masa ta kowane fanni, kuna ba da amfani a kowane aiki nagari, kuna ƙaruwa da sanin Allah. 11 t Allah yă dai ƙarfafa ku da matuƙar ƙarfi bisa ga ƙarfin ɗaukakarsa, domin ku jure matuƙa a game da haƙuri da farin ciki, 12 t kuna gode wa Uba, wanda ya maishe mu mu isa samun rabo cikin gādon tsarkakan da suke a cikin haske. 13 t Ya tsamo mu daga mulkin duhu, ya maishe mu ga mulkin ƙaunataccen Ɗansa,
14 t wanda ta gare shi ne muka sami fansa, wato, gafarar zunubanmu.Cikar Allah
15 t Shi ne surar Allah marar ganuwa, magāji ne tun ba a halicci kome ba, 16 t don ta gare shi ne aka halicci dukkan kome, abubuwan da suke a sama da abubuwan da suke a ƙasa, masu ganuwa da marasa ganuwa, ko kursiyai, ko masu mulki, ko masarauta, ko masu iko, wato, dukkan abubuwa an halicce su ne ta wurinsa, shi ne kuma makomarsu. 17 t Shi ne a gaba da dukkan abubuwa, dukkan abubuwa kuma shi ne yake riƙe da su. 18 t Shi ne kai ga jikin nan, wato Ikilisiya. Shi ne tushe, na farko a cikin masu tashi daga matattu, domin ta wurin kowane abu ya zama shi ne mafifici. 19 t A gare shi dukkan cikar Allah ta tabbata, domin Allah yana farin ciki da haka,
20 t da nufin ta wurinsa, Allah yă sulhunta dukkan abubuwa da shi kansa, na ƙasa ko na sama, yana ƙulla zumunci ta wurin jininsa na gicciye.
21 t Ku kuma dā a rabe kuke da Allah, maƙiyansa a zuci, masu mugun aiki. 22 t Amma a yanzu ya sulhunta ku ta hanyar jikinsa na mutuntaka, wato, ta wurin mutuwarsa, domin ya miƙa ku tsarkakakku, marasa aibu, marasa abin zargi kuma a gabansa.
23 t Sai dai fa ku nace wa bangaskiya, zaunannu, kafaffu, ba tare da wata ƙaura daga begen nan na bishara wadda kuka ji ba, wadda aka yi wa dukkan talikan da suke a duniya, wadda kuma ni Bulus na zama mai hidimarta.Hidimar Bulus zuwa ga Ikilisiya
24 t To, a yanzu ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, a jikina kuma ina cikasa abin da ya saura ga wahalar Almasihu, da aka aza mini saboda jikinsa, wato Ikilisiya, 25 t wadda na zama mai hidimarta bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da Maganar Allah sosai, 26 t wato, asirin nan da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, amma a yanzu an bayyana shi ga tsarkakansa. 27 t Su ne Allah ya so ya sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al'ummai, asirin nan kuwa shi ne Almasihu a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana. 28 t Shi ne kuwa muke sanarwa, muna yi wa kowane mutum gargaɗi, muna kuma koya wa kowane mutum da matuƙar hikima, da nufin mu miƙa kowane mutum cikakke a cikin Almasihu. 29 t Saboda wannan nake shan wahala, nake fama da matuƙar himma, wadda yake sa mini ta ƙarfin ikonsa.
Colossians 1
1 Paul, an apostle of Christ Jesus through the will of God, and Timothy our brother,2 To the saints and faithful brethren in Christ that are at Colossae: Grace to you and peace from God our Father.3 We give thanks to God the Father of our Lord Jesus Christ, praying always for you,4 having heard of your faith in Christ Jesus, and of the love which ye have toward all the saints,5 because of the hope which is laid up for you in the heavens, whereof ye heard before in the word of the truth of the gospel,6 which is come unto you; even as it is also in all the world bearing fruit and increasing, as it doth in you also, since the day ye heard and knew the grace of God in truth;7 even as ye learned of Epaphras our beloved fellow-servant, who is a faithful minister of Christ on our behalf,8 who also declared unto us your love in the Spirit.9 For this cause we also, since the day we heard it, do not cease to pray and make request for you, that ye may be filled with the knowledge of his will in all spiritual wisdom and understanding,10 to walk worthily of the Lord unto all pleasing, bearing fruit in every good work, and increasing in the knowledge of God;11 strengthened with all power, according to the might of his glory, unto all patience and longsuffering with joy;12 giving thanks unto the Father, who made us meet to be partakers of the inheritance of the saints in light;13 who delivered us out of the power of darkness, and translated us into the kingdom of the Son of his love;14 in whom we have our redemption, the forgiveness of our sins:15 who is the image of the invisible God, the firstborn of all creation;16 for in him were all things created, in the heavens and upon the earth, things visible and things invisible, whether thrones or dominions or principalities or powers; all things have been created through him, and unto him;17 and he is before all things, and in him all things consist.18 And he is the head of the body, the church: who is the beginning, the firstborn from the dead; that in all things he might have the preeminence.19 For it was the good pleasure of the Father that in him should all the fulness dwell;20 and through him to reconcile all things unto himself, having made peace through the blood of his cross; through him, I say, whether things upon the earth, or things in the heavens.21 And you, being in time past alienated and enemies in your mind in your evil works,22 yet now hath he reconciled in the body of his flesh through death, to present you holy and without blemish and unreproveable before him:23 if so be that ye continue in the faith, grounded and stedfast, and not moved away from the hope of the gospel which ye heard, which was preached in all creation under heaven; whereof I Paul was made a minister.24 Now I rejoice in my sufferings for your sake, and fill up on my part that which is lacking of the afflictions of Christ in my flesh for his body’s sake, which is the church;25 whereof I was made a minister, according to the dispensation of God which was given me to you-ward, to fulfil the word of God,26 even the mystery which hath been hid for ages and generations: but now hath it been manifested to his saints,27 to whom God was pleased to make known what is the riches of the glory of this mystery among the Gentiles, which is Christ in you, the hope of glory:28 whom we proclaim, admonishing every man and teaching every man in all wisdom, that we may present every man perfect in Christ;29 whereunto I labor also, striving according to his working, which worketh in me mightily.