previous next

KOL 3

1 To, da yake an tashe ku tare da Almasihu, sai ku nemi abubuwan da suke a Sama, inda Almasihu yake, a zaune a dama ga Allah. 2 t Ku ƙwallafa ranku a kan abubuwan da suke Sama, ba a kan abubuwan da suke a ƙasa ba. 3 t Gama kun mutu, ranku kuwa a ɓoye yake a gun Almasihu cikin Allah.

4 t Sa'ad da Almasihu wanda yake shi ne ranmu ya bayyana, sai ku ma ku bayyana tare da shi a cikin ɗaukaka.

Tsohon Rai da Sabon Rai


5  t Saboda haka, sai ku kashe zukatanku ga sha'awace-sha'wacen duniya, wato fasikanci, da aikin lalata, da muguwar sha'awa, da mummunan buri, da kuma kwaɗayi, wanda shi ma bautar gumaka ne. 6 t Saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake sauka a kan kangararru. 7 t A dā kuna bin waɗannan sa'ad da suke jiki a gare ku. 8 t Amma yanzu sai ku yar da duk waɗannan ma, wato fushi, da hasala, da ƙeta, da yanke, da alfasha. 9 t Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun yar da halinku na dā, da ayyukansa, 10 t kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa.

11 t A nan kam, ba hanyar nuna bambanci a tsakanin Ba'al'umme da Bayahude, ko mai kaciya da marar kaciya, ko bare da baubawa, ko ɗa da bawa, sai dai Almasihu shi ne kome, shi kuma yake cikinmu duka.
12  t Saboda haka, sai ku ɗauki halin tausayi, da kirki, da tawali'u, da salihanci, da haƙuri, idan ku zaɓaɓɓu ne na Allah, tsarkaka, ƙaunatattu, 13 t kuna jure wa juna, in kuma wani yana da ƙara game da wani, sai su yafe wa juna. Kamar yadda Ubangiji ya yafe muku, ku kuma sai ku yafe. 14 t Fiye da waɗannan duka, ku ɗau halin ƙauna, wadda dukkan kammala take ƙulluwa a cikinta. 15 t Salamar Almasihu kuma tă mallaki zuciyarku, domin lalle ga haka aka kira ku in kuna jiki guda, ku kuma kasance masu gode wa Allah. 16 t Maganar Almasihu tă kahu a cikin zuciyarku a yalwace, kuna koya wa juna, kuna yi wa juna gargaɗi da matuƙar hikima ta wurin rairar waƙoƙin Zabura da na yabon Allah, kuna kuma raira waƙa ga Allah, kuna gode masa tun daga zuci.

17 t Kome kuke yi, a game da magana ko aikatawa, ku yi duka da sunan Ubangiji Yesu, kuna gode wa Allah Uba ta wurinsa.

Zaman Dacewa na Sabon Rai


18  t Ku matan aure, ku bi mazanku yadda ya dace a cikin Ubangiji. 19 Ku maza, ku ƙaunaci matanku, kada kuma ku yi musu kaushin hali. 20 Ku 'ya'ya, ku yi wa iyayenku biyayya ta kowane hali, domin haka Ubangiji yake so. 21 Ku ubanni, kada ku ƙuntata wa 'ya'yanku, domin kada su karai. 22 Ku bayi, ku yi biyayya ga waɗanda suke iyayengijinku na duniya ta kowace hanya, ba da aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane rai, sai dai da zuciya ɗaya, kuna tsoron Ubangiji. 23 Kome za ku yi, ku yi shi da himma kuna bauta wa Ubangiji ne, ba mutum ba, 24 t da yake kun sani Ubangiji zai ba ku gādo sakamakonku. Ubangiji Almasihu fa kuke bauta wa! 25 t Mai mugun aiki kuwa za a sāka masa da mugun aikin da ya yi, babu kuma tāra.

Colossians 3

1 If then ye were raised together with Christ, seek the things that are above, where Christ is, seated on the right hand of God.2 Set your mind on the things that are above, not on the things that are upon the earth.3 For ye died, and your life is hid with Christ in God.4 When Christ, who is our life, shall be manifested, then shall ye also with him be manifested in glory.5 Put to death therefore your members which are upon the earth: fornication, uncleanness, passion, evil desire, and covetousness, which is idolatry;6 for which things’ sake cometh the wrath of God upon the sons of disobedience:7 wherein ye also once walked, when ye lived in these things;8 but now do ye also put them all away: anger, wrath, malice, railing, shameful speaking out of your mouth:9 lie not one to another; seeing that ye have put off the old man with his doings,10 and have put on the new man, that is being renewed unto knowledge after the image of him that created him:11 where there cannot be Greek and Jew, circumcision and uncircumcision, barbarian, Scythian, bondman, freeman; but Christ is all, and in all.12 Put on therefore, as God’s elect, holy and beloved, a heart of compassion, kindness, lowliness, meekness, longsuffering;13 forbearing one another, and forgiving each other, if any man have a complaint against any; even as the Lord forgave you, so also do ye:14 and above all these things put on love, which is the bond of perfectness.15 And let the peace of Christ rule in your hearts, to the which also ye were called in one body; and be ye thankful.16 Let the word of Christ dwell in you richly; in all wisdom teaching and admonishing one another with psalms and hymns and spiritual songs, singing with grace in your hearts unto God.17 And whatsoever ye do, in word or in deed, do all in the name of the Lord Jesus, giving thanks to God the Father through him.18 Wives, be in subjection to your husbands, as is fitting in the Lord.19 Husbands, love your wives, and be not bitter against them.20 Children, obey your parents in all things, for this is well-pleasing in the Lord.21 Fathers, provoke not your children, that they be not discouraged.22 Servants, obey in all things them that are your masters according to the flesh; not with eye-service, as men-pleasers, but in singleness of heart, fearing the Lord:23 whatsoever ye do, work heartily, as unto the Lord, and not unto men;24 knowing that from the Lord ye shall receive the recompense of the inheritance: ye serve the Lord Christ.25 For he that doeth wrong shall receive again for the wrong that he hath done: and there is no respect of persons.