previous next

KOL 4

1 Ku iyayengiji kuma, ku riƙi bayinku da gaskiya da daidaita, da yake kun sani ku ma kuna da Ubangiji a Sama.
2  t Ku lazamci yin addu'a, kuna zaune a faɗake a kanta sosai, tare da gode wa Allah, 3 t mu ma ku yi mana addu'a Allah ya buɗe mana hanyar yin Maganarsa, mu sanar da asirin Almasihu, wanda saboda shi ne nake a ɗaure,

4 domin in bayyana shi sosai, kamar yadda ya kamata in faɗa.
5  t Ku tafiyar da al'amuranku da hikima a cikin zamanku tare da marasa bi, kuna matuƙar amfani da lokaci.

6 t A kullum maganarku ta zama mai ƙayatarwa, mai daɗin ji, domin ku san irin amsar da ta dace ku ba kowa.

Gaisuwa


7  t Tikikus zai sanar da ku duk abin da nake ciki. Shi ƙaunataccen ɗan'uwa ne, amintaccen mai hidima, abokin bautarmu kuma a cikin Ubangiji. 8 t Na aiko shi a gare ku musamman, domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa muku zuciya.

9 t Ga kuma Unisimas a nan tare da shi, amintaccen ɗan'uwa ƙaunatacce, wanda shi ma a cikinku yake. Su za su gaya muku duk abin da ya faru a nan.
10  t Aristarkus, abokin ɗaurina, yana gaishe ku, haka kuma Markus, wanda kakansu ɗaya ne da Barnaba. Shi ne aka riga aka yi muku umarni a game da shi. In dai ya zo wurinku, ku karɓe shi. 11 Yasuwa kuma da ake kira Yustus yana gaishe ku. Wato, cikin abokan aikina ga Mulkin Allah, waɗannan su kaɗai ne daga cikin Yahudawa masu bi, sun kuwa sanyaya mini zuciya. 12 t Abafaras wanda yake ɗaya daga cikinku, bawan Almasihu Yesu, yana gaishe ku, a kullum yana yi muku addu'a da himma, ku dage, kuna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah. 13 t Na shaide shi, lalle ya yi muku aiki ƙwarai da gaske, da kuma waɗanda suke na Lawudikiya da na Hirafolis. 14 t Luka, ƙaunataccen likitan nan, da Dimas suna gaishe ku. 15 t A gayar mini da 'yan'uwa na Lawudikiya, da kuma Nimfa da ikilisiyar da take taruwa a gidanta. 16 t Sa'ad da aka karanta wasiƙar nan a gabanku, ku sa a karanta ta kuma a gaban ikilisiyar da take a Lawudikiya, ku kuma ku karanta tasu, wato ta Lawudikiyawa.

17 t Ku kuma faɗa wa Arkibus ya mai da hankali ya cika hidimar da Ubangiji ya sa shi.
18  t Ni Bulus, ni nake rubuta gaisuwar nan da hannuna. Ku tuna da ɗaurina. Alheri yă tabbata a gare ku.

Colossians 4

1 Masters, render unto your servants that which is just and equal; knowing that ye also have a Master in heaven.2 Continue stedfastly in prayer, watching therein with thanksgiving;3 withal praying for us also, that God may open unto us a door for the word, to speak the mystery of Christ, for which I am also in bonds;4 that I may make it manifest, as I ought to speak.5 Walk in wisdom toward them that are without, redeeming the time.6 Let your speech be always with grace, seasoned with salt, that ye may know how ye ought to answer each one.7 All my affairs shall Tychicus make known unto you, the beloved brother and faithful minister and fellow-servant in the Lord:8 whom I have sent you for this very purpose, that ye may know our state, and that he may comfort your hearts;9 together with Onesimus, the faithful and beloved brother, who is one of you. They shall make known unto you all things that are done here.10 Aristarchus my fellow-prisoner saluteth you, and Mark, the cousin of Barnabas (touching whom ye received commandments; if he come unto you, receive him),11 and Jesus that is called Justus, who are of the circumcision: these only are my fellow-workers unto the kingdom of God, men that have been a comfort unto me.12 Epaphras, who is one of you, a servant of Christ Jesus, saluteth you, always striving for you in his prayers, that ye may stand perfect and fully assured in all the will of God.13 For I bear him witness, that he hath much labor for you, and for them in Laodicea, and for them in Hierapolis.14 Luke, the beloved physician, and Demas salute you.15 Salute the brethren that are in Laodicea, and Nymphas, and the church that is in their house.16 And when this epistle hath been read among you, cause that it be read also in the church of the Laodiceans; and that ye also read the epistle from Laodicea.17 And say to Archippus, Take heed to the ministry which thou hast received in the Lord, that thou fulfil it.18 The salutation of me Paul with mine own hand. Remember my bonds. Grace be with you.