previous next

AFI 1

Gaisuwa

1  t Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, zuwa ga mutanensa tsarkaka da suke a Afisa, amintattu a cikin Almasihu Yesu.

2  t Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Albarku na Ruhu a Cikin Almasihu


3  t Yabo yā tabbata ga Allahn Ubangijinmu Yesu Almasihu, da Ubansa kuma, wanda ya yi mana albarka da kowace albarka ta Ruhu, basamaniya, a cikin Almasihu, 4 t domin kuwa ya zaɓe mu a cikin Almasihu tun ba a halicci duniya ba, mu zama tsarkaka, marasa aibu a gabansa. 5 t Ya ƙaddara mu mu zama 'ya'yansa ta wurin Yesu Almasihu, bisa ga nufinsa na alheri, 6 t domin mu yabi ɗaukakar alherinsa wanda ya ba mu kyauta hannu sake saboda Ƙaunataccensa. 7 t Ta gare shi ne muka sami fansa albarkacin jininsa, wato yafewar laifofinmu, bisa ga yalwar alherin Allah, 8 wanda ya falala mana. Da matuƙar hikima da basira 9 t ya sanasshe mu asirin nufinsa, bisa ga kyakkyawan nufinsa da ya nufa ya cika ta wurin Almasihu.

10 t Duk wannan kuwa shiri ne, domin a cikar lokaci a harhaɗa dukkan abubuwa ta wurin Almasihu, wato abubuwan da suke sama, da abubuwan da suke a ƙasa.
11  t A cikinsa ne aka maishe mu abin gādo na Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukkan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi, 12 t domin mu da muka fara kafa bege ga Almasihu mu yi zaman yabon ɗaukakarsa. 13 t A cikinsa ne ku kuma da kuka ji maganar gaskiya, wato, bisharar cetonku, a cikinsa, sa'ad da kuka ba da gaskiya kuma, aka hatimce ku da Ruhu Mai Tsarki wanda aka alkawarta.

14 t Shi ne kuwa tabbatawar gādonmu har kafin mu kai ga samunsa, wannan kuma domin yabon ɗaukakarsa ne.

Addu'a don Hikima da Sani


15  t Saboda haka da yake na ji labarin bangaskiyarku ga Ubangiji Yesu, da kuma ƙaunarku ga dukan tsarkaka, 16 t ban fāsa gode wa Allah saboda ku ba, duk sa'ad da nake yi muku addu'a, 17 t da nufin cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhu mai ba da hikima da bayani ga sanin Allah, 18 t a kuma sa ku ku waye ta idon zuci, domin ku san ko mene ne begen nan da ya kira ku a kai, da kuma ko mene ne yalwar gādonsa mai ɗaukaka a game da tsarkaka, 19 t da kuma ko mene ne girman ikonsa marar misaltuwa da yake zartarwa a gare mu, mu masu ba da gaskiya, wato zartarwar ƙarfin ikon nan nasa, 20 t wanda ya zartar ga Almasihu sa'ad da ya tashe shi daga matattu, ya kuma ba shi wurin zama a damansa a samaniya, 21 t a can a birbishin dukkan sarauta da iko, da ƙarfi, da mulki, a birbishin kowane suna da za a sa, ba ma a duniyar nan kawai ba, har ma a lahira ma. 22 t Allah kuma ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikon Almasihu, ya kuma ba da shi ga Ikkilisiya ya zama Kai mai mallakar abu duka. 23 Ikkilisiya ita ce jikin Almasihu, cikar mai cika dukkan abu.

Ephesians 1

1 Paul, an apostle of Christ Jesus through the will of God, to the saints that are at Ephesus, and the faithful in Christ Jesus:2 Grace to you and peace from God our Father and the Lord Jesus Christ.3 Blessed be the God and Father of our Lord Jesus Christ, who hath blessed us with every spiritual blessing in the heavenly places in Christ:4 even as he chose us in him before the foundation of the world, that we should be holy and without blemish before him in love:5 having foreordained us unto adoption as sons through Jesus Christ unto himself, according to the good pleasure of his will,6 to the praise of the glory of his grace, which he freely bestowed on us in the Beloved:7 in whom we have our redemption through his blood, the forgiveness of our trespasses, according to the riches of his grace,8 which he made to abound toward us in all wisdom and prudence,9 making known unto us the mystery of his will, according to his good pleasure which he purposed in him10 unto a dispensation of the fulness of the times, to sum up all things in Christ, the things in the heavens, and the things upon the earth; in him, I say,11 in whom also we were made a heritage, having been foreordained according to the purpose of him who worketh all things after the counsel of his will;12 to the end that we should be unto the praise of his glory, we who had before hoped in Christ:13 in whom ye also, having heard the word of the truth, the gospel of your salvation,-- in whom, having also believed, ye were sealed with the Holy Spirit of promise,14 which is an earnest of our inheritance, unto the redemption of God’s own possession, unto the praise of his glory.15 For this cause I also, having heard of the faith in the Lord Jesus which is among you, and the love which ye show toward all the saints,16 cease not to give thanks for you, making mention of you in my prayers;17 that the God of our Lord Jesus Christ, the Father of glory, may give unto you a spirit of wisdom and revelation in the knowledge of him;18 having the eyes of your heart enlightened, that ye may know what is the hope of his calling, what the riches of the glory of his inheritance in the saints,19 and what the exceeding greatness of his power to us-ward who believe, according to that working of the strength of his might20 which he wrought in Christ, when he raised him from the dead, and made him to sit at his right hand in the heavenly places,21 far above all rule, and authority, and power, and dominion, and every name that is named, not only in this world, but also in that which is to come:22 and he put all things in subjection under his feet, and gave him to be head over all things to the church,23 which is his body, the fulness of him that filleth all in all.