previous next

AFI 2

Daga Mutuwa zuwa Rai

1  t Ku kuma yā raya ku sa'ad da kuke matattu ta wurin laifofinku da zunubanku, 2 t waɗanda dā kuke a ciki, kuna biye wa al'amarin duniyar nan, kuna bin sarkin masu iko a sararin sama, wato iskar nan da take zuga zuciyar kangararru a yanzu. 3 t Dukkanmu dā mun zauna a cikinsu, muna biye wa sha'awoyin halin mutuntaka, muna aikata abin da jiki da zuciya suke buri, har ma ga ɗabi'a wajibi ne fushin Allah ya bayyana a kanmu, kamar sauran 'yan adam. 4 Amma Allah da yake mai yalwar jinƙai ne, saboda matsananciyar ƙaunar da yake yi mana, 5 t ko a sa'ad da muke matattu ma ta wurin laifofinmu, sai ya rayar da mu tare da Almasihu (ta wurin alheri an cece ku), 6 t a cikin Almasihu Yesu kuma ya tashe mu tare, har ya ba mu wurin zama tare a samaniya. 7 t Allah ya yi wannan kuwa domin a zamani mai zuwa ya bayyana yalwar alherinsa marar misaltuwa, ta wajen nuna mana alheri ta wurin Almasihu Yesu. 8 t Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya, wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku ba ne, baiwa ce ta Allah, 9 t ba kuwa saboda da aikin lada ba, kada wani ya yi fariya.

10 t Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Almasihu Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

Zama Ɗaya da Almasihu


11  t Saboda haka, ku tuna dā ku al'ummai ne bisa ɗabi'a, ga waɗanda ake kira masu kaciyar nan kuwa, sukan kira ku marasa kaciya (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu). 12 t Ku kuma tuna a lokacin nan a rabe kuke da Almasihu, bare ne ga jama'ar Isra'ila, bāƙi ne ga alkawaran nan da Allah ya yi, marasa bege, marasa Allah kuma a duniya. 13 t Amma a yanzu, a cikin Almasihu, ku da dā kuke can nesa, an kawo ku kusa ta wurin jinin Almasihu. 14 t Domin Almasihu shi ne salamarmu, shi wanda ya mai da Yahudawa da al'ummai ɗaya, wato ya rushe katangar nan da ta raba su a kan gāba. 15 t Har ya soke Shari'ar nan mai umarni da dokoki, ta wurin ba da jikinsa, domin ta gare shi yă halicci sabon mutum guda daga mutanen nan biyu, ta haka yă kawo salama, 16 t yă kuma sulhunta su duka biyu ga Allah, su zama jiki ɗaya ta wurin gicciye, ta haka yă kashe gābar. 17 t Ya kuwa zo ya yi muku albishirin salama, ku da kuke nesa, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa. 18 t Domin ta gare shi ne dukanmu biyu muka sami isa gun Uba ta hanyar Ruhu guda. 19 t Wato ashe, ku ba baƙi ba ne kuma, ko kuwa bāre, ai, ku abokan 'yanci ne na tsarkaka, iyalin Allah kuma, 20 t waɗanda aka gina bisa tushen manzanni da annabawa, Almasihu Yesu kansa kuwa shi ne mafificin dutsen ginin, 21 t dukan wanda aka haɗa tsarin ginin a cikinsa, yana kuma tashi ya zama haikali tsattsarka na Ubangiji. 22 A cikinsa ne ku kuma aka gina ku, ku zama mazaunin Allah ta wurin Ruhu.

Ephesians 2

1 And you did he make alive, when ye were dead through your trespasses and sins,2 wherein ye once walked according to the course of this world, according to the prince of the powers of the air, of the spirit that now worketh in the sons of disobedience;3 among whom we also all once lived in the lust of our flesh, doing the desires of the flesh and of the mind, and were by nature children of wrath, even as the rest:--4 but God, being rich in mercy, for his great love wherewith he loved us,5 even when we were dead through our trespasses, made us alive together with Christ (by grace have ye been saved),6 and raised us up with him, and made us to sit with him in the heavenly places, in Christ Jesus:7 that in the ages to come he might show the exceeding riches of his grace in kindness toward us in Christ Jesus:8 for by grace have ye been saved through faith; and that not of yourselves, it is the gift of God;9 not of works, that no man should glory.10 For we are his workmanship, created in Christ Jesus for good works, which God afore prepared that we should walk in them.11 Wherefore remember, that once ye, the Gentiles in the flesh, who are called Uncircumcision by that which is called Circumcision, in the flesh, made by hands;12 that ye were at that time separate from Christ, alienated from the commonwealth of Israel, and strangers from the covenants of the promise, having no hope and without God in the world.13 But now in Christ Jesus ye that once were far off are made nigh in the blood of Christ.14 For he is our peace, who made both one, and brake down the middle wall of partition,15 having abolished in the flesh the enmity, even the law of commandments contained in ordinances; that he might create in himself of the two one new man, so making peace;16 and might reconcile them both in one body unto God through the cross, having slain the enmity thereby:17 and he came and preached peace to you that were far off, and peace to them that were nigh:18 for through him we both have our access in one Spirit unto the Father.19 So then ye are no more strangers and sojourners, but ye are fellow-citizens with the saints, and of the household of God,20 being built upon the foundation of the apostles and prophets, Christ Jesus himself being the chief corner stone;21 in whom each several building, fitly framed together, groweth into a holy temple in the Lord;22 in whom ye also are builded together for a habitation of God in the Spirit.