AFI 3
Hidimar Bulus ga Al'ummai
1 t Domin haka, ni Bulus, ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu domin amfanin ku al'ummai, 2 t in dai kun ji labarin mai da ni mai hidimar alherin Allah wanda aka yi mini baiwa saboda ku, 3 t wato yadda aka sanar da ni asirin Ubangiji ta wahayi, kamar yadda na riga na rubuta a taƙaice. 4 t A yayin da kuka karanta wannan, za ku iya gane basirata saboda asirin Almasihu, 5 t wanda a zamanin dā ba a sanar da 'yan adam ba, kamar yadda a yanzu aka bayyana wa manzanninsa tsarkaka da annabawa, ta wurin Ruhu,
6 t wato, yadda ta wurin bishara al'ummai da suke abokan gādo da mu, gaɓoɓin jiki guda, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Almasihu Yesu.
7 t An kuwa sa ni mai hidimar wannan bishara, a bisa ga baiwar alherin Allah da aka yi mini ta ƙarfin ikonsa. 8 t Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa, 9 t in kuma bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda shekara da shekaru yake a ɓoye a gun Allah, wanda ya halicci dukkan abubuwa. 10 t An yi wannan ne kuwa domin a yanzu a sanar da hikimar Allah iri iri ga manyan mala'iku da masu iko a samaniya, ta hanyar Ikkilisiya. 11 Wannan kuwa bisa ga dawwamammen nufin nan ne da Allah ya zartar a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu. 12 t A cikinsa muke da gabagaɗin isa ga Allah, da amincewa, ta wurin bangaskiyarmu a gare shi.
13 Saboda haka, ina roƙonku kada ku karai da ganin wahalar da nake sha dominku, wannan kuwa ɗaukakarku ce.A San Ƙaunar Almasihu
14 t Saboda haka, nake durƙusawa a gaban Uban, 15 shi da yake sa wa kowace kabila ta sama da ta ƙasa suna, 16 t ina addu'a ya yi muku baiwa bisa ga yalwar ɗaukakarsa, ku ƙarfafa matuƙa a birnin zuciyarku ta wurin Ruhunsa, 17 t har ma Almasihu yă zauna a zukatanku ta wurin bangaskiyarku, domin ƙauna ta kahu da gindinta sosai a zukatanku, 18 t har ku sami kaifin basira tare da dukan tsarkaka, ku fahimci ko mene ne fāɗin ƙaunar Almasihu, da tsawonta da zacinta, da kuma zurfinta,
19 t ku kuma san ƙaunar da Almasihu yake yi mana, wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan falala ta Allah.
20 t Ɗaukaka tā tabbata ga wannan da yake da ikon aikatawa fiye da dukkan abin da za mu roƙa, ko za mu zata nesa, wato, aikatawa ta ƙarfin ikonsa da yake aiki a zuciyarmu. 21 t Ɗaukaka tă tabbata a gare shi a cikin Ikkilisiya ta wurin Almasihu Yesu, har ya zuwa dukkan zamanai har abada abadin. Amin.
Ephesians 3
1 For this cause I Paul, the prisoner of Christ Jesus in behalf of you Gentiles,--2 if so be that ye have heard of the dispensation of that grace of God which was given me to you-ward;3 how that by revelation was made known unto me the mystery, as I wrote before in few words,4 whereby, when ye read, ye can perceive my understanding in the mystery of Christ;5 which in other generations was not made known unto the sons of men, as it hath now been revealed unto his holy apostles and prophets in the Spirit;6 to wit, that the Gentiles are fellow-heirs, and fellow-members of the body, and fellow-partakers of the promise in Christ Jesus through the gospel,7 whereof I was made a minister, according to the gift of that grace of God which was given me according to the working of his power.8 Unto me, who am less than the least of all saints, was this grace given, to preach unto the Gentiles the unsearchable riches of Christ;9 and to make all men see what is the dispensation of the mystery which for ages hath been hid in God who created all things;10 to the intent that now unto the principalities and the powers in the heavenly places might be made known through the church the manifold wisdom of God,11 according to the eternal purpose which he purposed in Christ Jesus our Lord:12 in whom we have boldness and access in confidence through our faith in him.13 Wherefore I ask that ye may not faint at my tribulations for you, which are your glory.14 For this cause I bow my knees unto the Father,15 from whom every family in heaven and on earth is named,16 that he would grant you, according to the riches of his glory, that ye may be strengthened with power through his Spirit in the inward man;17 that Christ may dwell in your hearts through faith; to the end that ye, being rooted and grounded in love,18 may be strong to apprehend with all the saints what is the breadth and length and height and depth,19 and to know the love of Christ which passeth knowledge, that ye may be filled unto all the fulness of God.20 Now unto him that is able to do exceeding abundantly above all that we ask or think, according to the power that worketh in us,21 unto him be the glory in the church and in Christ Jesus unto all generations for ever and ever. Amen.