previous next

GAL 3

Shari'a ko Bangaskiya

1  t Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ɗauke hankalinku? Ku da aka bayyana muku Yesu Almasihu gicciyeyye sosai. 2 t Abu ɗaya kaɗai zan tambaye ku. Kun sami Ruhu saboda bin Shari'a ne, ko kuwa saboda gaskatawa ga maganar da kuka ji? 3 Ashe, rashin azancinku har ya kai ga haka? Da kuka fara da Ruhu, ashe, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku ƙarasa? 4 Ashe, a banza kuka sha wuya iri iri? In dai har a banzan ne!

5 t Wato, shi da yake yi muku baiwar Ruhu, yake kuma yin mu'ujizai a cikinku, saboda kuna bin Shari'a ne yake yin haka, ko kuwa saboda gaskatawa da maganar da kuka ji?
6  t Haka ma Ibrahim “ya gaskata Allah, bangaskiyan nan tasa kuma, aka lasafta ta adalci ce a gare shi.” 7 t Wato kun ga ashe, masu bangaskiya su ne 'ya'yan Ibrahim. 8 t A cikin Nassi kuwa an hango, cewa Allah zai kuɓutar da al'ummai ta wurin bangaskiya, wato, dā ma can an yi wa Ibrahim bishara cewa, “Ta wurinka za a yi wa dukkan al'ummai albarka.”

9 t To, ashe, masu bangaskiya su ne aka yi wa albarka a game da Ibrahim mai bangaskiyar nan.
10  t Gama duk waɗanda suke dogara da bin Shari'a la'anannu ne, don a rubuce yake cewa, “Duk wanda bai tsaya ga aikata duk abin da yake rubuce a littafin Shari'a ba, la'ananne ne.” 11 t To, a fili yake, ba mai samun kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, domin “Wanda yake da adalci ta wurin bangaskiya zai rayu.” 12 t Shari'a kuwa ba ta dangana ga bangaskiya ba, domin ta ce, “Wanda ya aikata ta, ta gare ta ne zai rayu.” 13 t Almasihu ya fanso mu daga la'anar nan ta Shari'a, da ya zama abin la'ana saboda mu, domin a rubuce yake cewa, “Duk wanda aka kafa a jikin itace, la'ananne ne.”

14 t An yi wannan kuwa domin albarkar nan da aka yi wa Ibrahim ta saukar wa al'ummai ta wurin Almasihu Yesu, mu kuma ta hanyar bangaskiya mu sami Ruhun nan da aka yi alkawari.

Shari'a da Alkawari


15 To, 'yan'uwa, bari in yi muku misali. Ko alkawari na mutum ne kawai, in dai an riga an tabbatar da shi, ba mai soke shi, ba kuma mai ƙara wani abu a kai. 16 t To, alkawaran nan, an yi wa Ibrahim ne, da kuma wani a zuriyarsa. Ba a ce, “Da zuriya” ba, kamar suna da yawa. A'a, sai dai ɗaya kawai, aka ce, “Wani a zuriyarka,” wato Almasihu. 17 t Ga abin da nake nufi. Shari'ar nan, wadda ta zo shekara arbaminya da talatin daga baya, ba ta shafe alkawarin nan da Allah ya tabbatar tun tuni ba, har da za ta wofinta shi.

18 t Don da gādon nan ta hanyar Shari'a yake samuwa, ashe, da ba zai zama na alkawarin ke nan ba. Amma Allah ya bai wa Ibrahim ta wurin alkawari ne.
19  t To, mece ce manufar Shari'a? Ƙari aka yi da ita don fitowa da laifi fili, har kafin na zuriyar nan ya zo, wanda aka yi wa alkawarin, an kuma ba da ita ta wurin mala'iku ne, ta hannun matsakanci.

20 t Matsakanci fa ba domin ɗaya ba ne. Amma Allah ɗaya yake.

Manufar Shari'a


21  t Wato, Shari'a ta zama saɓanin alkawaran Allah ke nan? A'a, ko kusa! Domin da an ba da wata shari'a mai iya ba da rai, da sai a sami adalcin Allah ta hanyar bin Shari'ar nan.

22 t Amma Nassi ya kulle kowa a cikin zunubi, don albarkar da aka yi alkawari saboda gaskatawa da Yesu Almasihu, a ba da ita ga masu ba da gaskiya.
23  t Tun kafin bangaskiya ta zo, a cikin ƙangin Shari'a muke a kulle, sai a lokacin da bangaskiya ta bayyana. 24 t Ashe kuwa, Shari'a ta zama uwargijiyarmu da ta kai mu ga Almasihu, domin mu sami kuɓuta ga Allah ta wurin bangaskiya. 25 A yanzu kuwa da bangaskiya ta zo, ba sauran zamanmu a hannun wata uwargijiya. 26 t Domin dukanku 'ya'yan Allah ne, ta wurin bangaskiya ga Almasihu Yesu. 27 t Duk ɗaukacinku da aka yi wa baftisma ga bin Almasihu, kun ɗauki halin Almasihu ke nan. 28 t Ba sauran cewa Bayahude ko Ba'al'umme, ko ɗa, ko bawa, ko namiji ko mace. Ai, dukkanku ɗaya kuke, na Almasihu Yesu. 29 t In kuwa ku na Almasihu ne, ashe, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda ne kuma bisa ga alkawarin nan.

Galatians 3

1 O foolish Galatians, who did bewitch you, before whose eyes Jesus Christ was openly set forth crucified?2 This only would I learn from you. Received ye the Spirit by the works of the law, or by the hearing of faith?3 Are ye so foolish? having begun in the Spirit, are ye now perfected in the flesh?4 Did ye suffer so many things in vain? if it be indeed in vain.5 He therefore that supplieth to you the Spirit, and worketh miracles among you, doeth he it by the works of the law, or by the hearing of faith?6 Even as Abraham believed God, and it was reckoned unto him for righteousness.7 Know therefore that they that are of faith, the same are sons of Abraham.8 And the scripture, foreseeing that God would justify the Gentiles by faith, preached the gospel beforehand unto Abraham, saying, In thee shall all the nations be blessed.9 So then they that are of faith are blessed with the faithful Abraham.10 For as many as are of the works of the law are under a curse: for it is written, Cursed is every one who continueth not in all things that are written in the book of the law, to do them.11 Now that no man is justified by the law before God, is evident: for, The righteous shall live by faith;12 and the law is not of faith; but, He that doeth them shall live in them.13 Christ redeemed us from the curse of the law, having become a curse for us; for it is written, Cursed is every one that hangeth on a tree:14 that upon the Gentiles might come the blessing of Abraham in Christ Jesus; that we might receive the promise of the Spirit through faith.15 Brethren, I speak after the manner of men: Though it be but a man’s covenant, yet when it hath been confirmed, no one maketh it void, or addeth thereto.16 Now to Abraham were the promises spoken, and to his seed. He saith not, And to seeds, as of many; but as of one, And to thy seed, which is Christ.17 Now this I say: A covenant confirmed beforehand by God, the law, which came four hundred and thirty years after, doth not disannul, so as to make the promise of none effect.18 For if the inheritance is of the law, it is no more of promise: but God hath granted it to Abraham by promise.19 What then is the law? It was added because of transgressions, till the seed should come to whom the promise hath been made; and it was ordained through angels by the hand of a mediator.20 Now a mediator is not a mediator of one; but God is one.21 Is the law then against the promises of God? God forbid: for if there had been a law given which could make alive, verily righteousness would have been of the law.22 But the scriptures shut up all things under sin, that the promise by faith in Jesus Christ might be given to them that believe.23 But before faith came, we were kept in ward under the law, shut up unto the faith which should afterwards be revealed.24 So that the law is become our tutor to bring us unto Christ, that we might be justified by faith.25 But now faith that is come, we are no longer under a tutor.26 For ye are all sons of God, through faith, in Christ Jesus.27 For as many of you as were baptized into Christ did put on Christ.28 There can be neither Jew nor Greek, there can be neither bond nor free, there can be no male and female; for ye all are one man in Christ Jesus.29 And if ye are Christ’s, then are ye Abraham’s seed, heirs according to promise.