previous next

GAL 5

Ku Dāge a Cikin 'Yanci

1  t Almasihu ya 'yanta mu, 'yantawar gaske. Don haka sai ku dāge, kada ku sāke sarƙafewa a cikin ƙangin bauta.
2  t To, ni Bulus, ina gaya muku, in kuna yarda a yi muku kaciya, Almasihu ba zai amfane ku kome ba ke nan. 3 t Ina sāke tabbatar wa duk wanda ya yarda a yi masa kaciya, cewa wajibi ne ya bi dukkan Shari'a. 4 t Ku da kuke neman kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, kun katse daga Almasihu ke nan, kun noƙe daga alherin Allah. 5 t Gama mu, ta wurin ikon Ruhu, muke ɗokin cikar begen nan namu na samun adalcin Allah saboda bangaskiya.

6 t In muna a cikin Almasihu Yesu, kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba. Bangaskiya mai aikata ƙauna ita ce wani abu.
7  t Dā, ai, kuna ci gaba sosai. Wane ne ya hana ku bin gaskiya? 8 t Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne. 9 t Ai, ɗan yisti kaɗan, yake game dukkan curin gurasa. 10 t Na dai amince da ku a cikin Ubangiji, ba za ku bi wani ra'ayi dabam da nawa ba. Wannan da yake ta da hankalinku kuwa zai sha hukunci, ko shi wane ne. 11 t Amma 'yan'uwa, in da har yanzu wa'azin yin kaciya nake yi, to, don me har yanzu ake tsananta mini? In da haka ne, ashe, an kawar da hamayyar da gicciyen Almasihu yake sawa ke nan!

12 t Da ma a ce masu ta da hankalinku ɗin nan su mai da kansu babanni!
13  t Ya ku 'yan'uwa, don 'yanci musamman aka kira ku, amma kada ku mai da 'yancin nan naku hujjar biye wa halin mutuntaka, sai dai ku bauta wa juna da ƙauna. 14 t Don duk Shari'a an ƙunshe ta ne a kalma guda, wato, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

15 Amma in kuna cin naman juna, ku mai da hankali fa, hanyar hallaka juna ke nan.

Albarkar Ruhu da Halin Mutuntaka


16  t Maganata ita ce, ku yi zaman Ruhu, ba kuwa za ku biye wa halin mutuntaka ba. 17 t Don halin mutuntaka gāba yake yi da Ruhu, Ruhu kuma yana gāba da halin mutuntaka. Waɗannan biyu gāba suke yi da juna, har ba kwa iya yin abin da kuke so.

18 t In Ruhu ne yake bi da ku, ashe, Shari'a ba ta da iko da ku, ke nan.
19  t Aikin halin mutuntaka a fili yake, wato, fasikanci, da aikin lalata, da fajirci, 20 da bautar gumaka, da sihiri, da gāba, da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da tsaguwa, da hamayya,

21 t da hassada, da buguwa, da shashanci, da kuma sauran irinsu. Ina faɗakar da ku kamar yadda na faɗakar da ku a dā, cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, ba za su sami gādo a Mulkin Allah ba.
22  t Albarkar Ruhu kuwa ita ce ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci, 23 t da tawali'u da kuma kamunkai. Masu yin irin waɗannan abubuwa, ba dama shari'a ta kama su.

24 t Waɗanda kuwa suke su na Almasihu Yesu ne, sun gicciye halin mutuntaka da mugayen sha'awace-sha'awace iri iri.
25 In dai rayuwar tamu ta Ruhu ce, to, sai mu tafiyar da al'amuranmu ta wurin ikon Ruhu. 26 t Kada mu zama masu homa, muna tsokanar juna, muna yi wa juna hassada.

Galatians 5

1 For freedom did Christ set us free: stand fast therefore, and be not entangled again in a yoke of bondage.2 Behold, I Paul say unto you, that, if ye receive circumcision, Christ will profit you nothing.3 Yea, I testify again to every man that receiveth circumcision, that he is a debtor to do the whole law.4 Ye are severed from Christ, ye would be justified by the law; ye are fallen away from grace.5 For we through the Spirit by faith wait for the hope of righteousness.6 For in Christ Jesus neither circumcision availeth anything, nor uncircumcision; but faith working through love.7 Ye were running well; who hindered you that ye should not obey the truth?8 This persuasion came not of him that calleth you.9 A little leaven leaveneth the whole lump.10 I have confidence to you-ward in the Lord, that ye will be none otherwise minded: but he that troubleth you shall bear his judgment, whosoever he be.11 But I, brethren, if I still preach circumcision, why am I still persecuted? then hath the stumbling-block of the cross been done away.12 I would that they that unsettle you would even go beyond circumcision.13 For ye, brethren, were called for freedom; only use not your freedom for an occasion to the flesh, but through love be servants one to another.14 For the whole law is fulfilled in one word, even in this: Thou shalt love thy neighbor as thyself.15 But if ye bite and devour one another, take heed that ye be not consumed one of another.16 But I say, walk by the Spirit, and ye shall not fulfil the lust of the flesh.17 For the flesh lusteth against the Spirit, and the Spirit against the flesh; for these are contrary the one to the other; that ye may not do the things that ye would.18 But if ye are led by the Spirit, ye are not under the law.19 Now the works of the flesh are manifest, which are these: fornication, uncleanness, lasciviousness,20 idolatry, sorcery, enmities, strife, jealousies, wraths, factions, divisions, parties,21 envyings, drunkenness, revellings, and such like; of which I forewarn you, even as I did forewarn you, that they who practise such things shall not inherit the kingdom of God.22 But the fruit of the Spirit is love, joy, peace, longsuffering, kindness, goodness, faithfulness,23 meekness, self-control; against such there is no law.24 And they that are of Christ Jesus have crucified the flesh with the passions and the lusts thereof.25 If we live by the Spirit, by the Spirit let us also walk.26 Let us not become vainglorious, provoking one another, envying one another.