previous next

GAL 6

Ku Ɗauki Wahalar Juna

1  t Ya ku 'yan'uwa, in an kama mutum yana a cikin yin laifi, ku da kuke na ruhu, sai ku komo da shi a kan hanya da tawali'u, kowa yana kula da kansa kada shi ma ya burmu. 2 t Ku ɗauki wahalar juna, ta haka za ku cika shari'ar Almasihu. 3 t Kowa ya zaci shi wani abu ne, alhali kuwa shi ba kome ba ne, ya ruɗi kansa ke nan. 4 Kowa yă auna aikinsa ya gani, sa'an nan ne zai iya gadara da maƙaminsa shi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba.

5 Lalle kowa yă ji da kayansa.

6  t Duk wanda aka koya wa Maganar, yă ci moriyar abubuwansa na alheri tare da mai koyarwa.
7  t Kada fa a yaudare ku, ai, ba a iya zambatar Allah. Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba. 8 t Wanda ya yi shuka a kwaɗayin son zuciyarsa, ta wurin son zuciya zai girbi ruɓa. Wanda ya yi shuka a Ruhu, ta wurin Ruhu zai girbi rai madawwami. 9 t Kada mu yi sanyi da yin aiki nagari, don za mu yi girbi a kan kari, in ba mu karai ba.

10 t To, saboda haka, in hali ya yi, sai mu kyautata wa kowa, tun ba ma waɗanda suke jama'ar masu ba da gaskiya ba.

Kashedi da kuma Gaisuwa


11  t Ku dubi irin rubutu gwada-gwada da nake muku da hannuna! 12 t To, mutanen nan masu son nuna bijinta cikin jiki, su ne masu son tilasta muku yin kaciya, don gudun shan wuya saboda gicciyen Almasihu. 13 t Ai, ko waɗanda aka yi wa kaciya ma ba sa kiyaye Shari'a. Sonsu ne a yi muku kaciya, don su yi fāriya da ku a kan an yi muku kaciya. 14 t Amma ni ko kusa ba zan yi fariya ba, sai dai a game da gicciyen Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta albarkacin mutuwarsa a kan gicciye ne na yar da sha'anin duniya, duniya kuma ta yar da sha'anina. 15 t Kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba, sai dai sabuwar halitta ita ce wani abu.

16 Salama da jinƙai su tabbata ga duk masu bin ka'idar nan, wato Isra'ilar gaske ta Allah.

17  t Daga nan gaba kada kowa ya ƙara damuna, domin a jikina ina da tabbai masu nuna ni bawan Ubangiji Yesu ne.
18  t Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku, 'yan'uwa. Amin.

Galatians 6

1 Brethren, even if a man be overtaken in any trespass, ye who are spiritual, restore such a one in a spirit of gentleness; looking to thyself, lest thou also be tempted.2 Bear ye one another’s burdens, and so fulfil the law of Christ.3 For if a man thinketh himself to be something when he is nothing, he deceiveth himself.4 But let each man prove his own work, and then shall he have his glorying in regard of himself alone, and not of his neighbor.5 For each man shall bear his own burden.6 But let him that is taught in the word communicate unto him that teacheth in all good things.7 Be not deceived; God is not mocked: for whatsoever a man soweth, that shall he also reap.8 For he that soweth unto his own flesh shall of the flesh reap corruption; but he that soweth unto the Spirit shall of the Spirit reap eternal life.9 And let us not be weary in well-doing: for in due season we shall reap, if we faint not.10 So then, as we have opportunity, let us work that which is good toward all men, and especially toward them that are of the household of the faith.11 See with how large letters I write unto you with mine own hand.12 As many as desire to make a fair show in the flesh, they compel you to be circumcised; only that they may not be persecuted for the cross of Christ.13 For not even they who receive circumcision do themselves keep the law; but they desire to have you circumcised, that they may glory in your flesh.14 But far be it from me to glory, save in the cross of our Lord Jesus Christ, through which the world hath been crucified unto me, and I unto the world.15 For neither is circumcision anything, nor uncircumcision, but a new creature.16 And as many as shall walk by this rule, peace be upon them, and mercy, and upon the Israel of God.17 Henceforth, let no man trouble me; for I bear branded on my body the marks of Jesus.18 The grace of our Lord Jesus Christ be with your spirit, brethren. Amen.