previous next

FIL 10

1  t To, tun da yake Shari'a ishara ce kawai ta kyawawan abubuwan da suke a gaba, ba ainihin siffarsu ba, ashe, har abada ba za ta iya kammala waɗanda suke kusatar Allah ta wurin waɗannan hadayu ba, waɗanda ake yi a kai a kai kowace shekara. 2 In haka ne kuwa, ashe, ba sai a daina yin hadayar ba? Da an taɓa tsarkake masu ibadar nan sarai, ai, da ba su ƙara damuwa da zunubai ba. 3 t Amma a game da irin waɗannan hadayu, akan tuna da zunubai a kowace shekara,

4 t domin ba mai yiwuwa ba ne jinin bijimai da na awaki ya ɗauke zunubi.

5  t Shi ya sa da Almasihu zai shigo duniya, sai ya ce,
“Hadaya da sadaka kam, ba ka so,
Amma kā tanadar mini jiki.

6 Ba ka farin ciki da hadayar ƙonewa, da kuma hadayar kawar da zunnbai.

7  t Sa'an nan na ce, ‘Ga ni, na zo in aikata nufinka, ya Allah,’
Kamar yadda yake a rubuce a game da ni a Littafi.”
8  t Sa'ad da ɗazu ya ce, “Ba ka son hadaya, da sadaka, da hadayar ƙonewa, da hadayar kawar da zunubai, ba ka kuwa jin daɗinsu,” wato, irin waɗanda ake miƙawa ta hanyar Shari'a, 9 t sai kuma ya ƙara da cewa, “Ga ni, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon ne, don yă kafa na biyun.

10 t Ta nufin nan ne aka tsarkake mu, ta wurin miƙa jikin Yesu Almasihu hadaya sau ɗaya tak, ba ƙari.
11  t Har wa yau kuma, kowane firist yakan tsaya a kan hidimarsa kowace rana, yana miƙa hadaya iri ɗaya a kai a kai, waɗanda har abada ba za su iya ɗauke zunubai ba. 12 Amma shi Almasihu da ya miƙa hadaya guda ta har abada domin kawar da zunubai, sai ya zauna a dama ga Allah, 13 t tun daga lokacin nan yana jira, sai an sa ya take maƙiyansa. 14 t Gama ta hadaya guda kawai ya kammala waɗanda aka tsarkake har abada.

15 t Ruhu Mai Tsarki ma yana yi mana shaida haka, domin bayan ya ce,

16  t “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su,
Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji,
Zan sa shari'una a birnin zuciyarsu,
In kuma rubuta su a allon zuciyarsu,”

17  t sai kuma ya ƙara cewa,
“Ba kuma zan ƙara tunawa da zunubansu da laifofinsu ba.”

18 To, a inda aka sami gafarar waɗannan, ba sauran wata hadaya domin kawar da zunubi.

Mu Matsa Kusa, Mu Dage


19  t Saboda haka, ya 'yan'uwa, tun da muke da amincewar shiga Wuri Mafi Tsarki, ta wurin jinin Yesu, 20 t ta wurin sabuwar hanya, rayayyiya wadda ya buɗe mana ta labulen nan, wato jikinsa, 21 t da yake kuma muna da Firist mai girma, mai mulkin jama'ar Allah, 22 t sai mu matsa kusa, da zuciya ɗaya, da cikakkiyar bangaskiya tabbatacciya, da zukatunmu tsarkakakku daga mugun lamiri, jikinmu kuma wankakke da tsattsarkan ruwa. 23 t Sai mu tsaya da ƙarfi a kan bayyana yarda ga begen nan namu, domin shi mai yin alkawarin nan amintacce ne, 24 mu kuma riƙa kula da juna, ta yarda za mu ta da juna a tsimi mu mu yi ƙauna da aika nagari.

25 t Kada mu bar yin taronmu, yadda waɗansu suke yi, sai dai mu ƙarfafa wa juna zuciya, tun ba ma da kuka ga ranar nan tana kusatowa ba.
26  t In kuwa mun ci gaba da yin zunubi da gangan, bayan mun yi na'am da sanin gaskiya, to, ba fa sauran wata hadaya domin kawar da zunubai, 27 t sai dai matsananciyar fargabar hukunci, da kuma wuta mai tsananin zafi, wadda za ta cinye maƙiyan Allah. 28 t Kowa ya yar da Shari'ar Musa, akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidu biyu ko uku. 29 t To mutumin da ya raina Ɗan Allah, ya kuma tozarta jinin nan na tabbatar alkawari, wanda aka tsarkake shi da shi, har ya wulakanta Ruhun alheri, wane irin hukunci mafi tsanani kuke tsammani ya cancanta fiye da wancan? 30 t Domin mun san shi, shi wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce, ni zan sāka.” Da kuma, “Ubangiji zai yi wa jama'arsa hukunci.”

31 t Abu ne fa mai matuƙar bantsoro a fāɗa a cikin hukuncin Allah Rayayye.
32  t Amma dai ku tuna, a shekarun baya, bayan da aka haskaka zukatanku, kun jure tsananin fama da shan wuya, 33 t wata rana ana zaginku, ana ta wahalshe ku, ana wulakanta ku a gaban jama'a, wata rana kuma kuna mai da kanku ɗaya da waɗanda aka yi wa haka, 34 t domin kun ji tausayin ɗaurarru, kun kuma yarda da daɗin rai da wason da aka yi muku, tun da yake kun sakankance kuna da mallaka mafi kyau, mai tabbata kuwa. 35 Saboda haka, kada ku yar da amincewar nan taku, domin tana da sakamako mai yawa.

36 t Gama yin jimiri ya kama ku, domin bayan da kun aikata nufin Allah, ku sami abin da aka yi muku alkawari.

37  t “Sauran lokaci kaɗan,
Mai zuwan nan zai zo, ba kuwa zai yi jinkiri ba.

38  t Amma adalina, ta wurin bangaskiya zai rayu.
Amma in ya ja da baya, ba zan yi farin ciki da shi ba.”
39 Amma mu ba a cikin waɗanda suke ja da baya su hallaka muke ba, mu a cikin masu bangaskiya muke, mai kai mu ga ceton rayukanmu.

Hebrews 10

1 For the law having a shadow of the good things to come, not the very image of the things, can never with the same sacrifices year by year, which they offer continually, make perfect them that draw nigh.2 Else would they not have ceased to be offered? because the worshippers, having been once cleansed, would have had no more consciousness of sins.3 But in those sacrifices there is a remembrance made of sins year by year.4 For it is impossible that the blood of bulls and goats should take away sins.5 Wherefore when he cometh into the world, he saith, Sacrifice and offering thou wouldest not, But a body didst thou prepare for me;

6 In whole burnt offerings and sacrifices for sin thou hadst no pleasure:

7 Then said I, Lo, I am come (In the roll of the book it is written of me) To do thy will, O God.

8 Saying above, Sacrifices and offerings and whole burnt offerings and sacrifices for sin thou wouldest not, neither hadst pleasure therein (the which are offered according to the law),9 then hath he said, Lo, I am come to do thy will. He taketh away the first, that he may establish the second.10 By which will we have been sanctified through the offering of the body of Jesus Christ once for all.11 And every priest indeed standeth day by day ministering and offering oftentimes the same sacrifices, the which can never take away sins:12 but he, when he had offered one sacrifice for sins for ever, sat down on the right hand of God;13 henceforth expecting till his enemies be made the footstool of his feet.14 For by one offering he hath perfected for ever them that are sanctified.15 And the Holy Spirit also beareth witness to us; for after he hath said,

16 This is the covenant that I will make with them After those days, saith the Lord: I will put my laws on their heart, And upon their mind also will I write them; then saith he,

17 And their sins and their iniquities will I remember no more.

18 Now where remission of these is, there is no more offering for sin.19 Having therefore, brethren, boldness to enter into the holy place by the blood of Jesus,20 by the way which he dedicated for us, a new and living way, through the veil, that is to say, his flesh;21 and having a great priest over the house of God;22 let us draw near with a true heart in fulness of faith, having our hearts sprinkled from an evil conscience: and having our body washed with pure water,23 let us hold fast the confession of our hope that it waver not; for he is faithful that promised:24 and let us consider one another to provoke unto love and good works;25 not forsaking our own assembling together, as the custom of some is, but exhorting one another; and so much the more, as ye see the day drawing nigh.26 For if we sin wilfully after that we have received the knowledge of the truth, there remaineth no more a sacrifice for sins,27 but a certain fearful expectation of judgment, and a fierceness of fire which shall devour the adversaries.28 A man that hath set at nought Moses law dieth without compassion on the word of two or three witnesses:29 of how much sorer punishment, think ye, shall he be judged worthy, who hath trodden under foot the Son of God, and hath counted the blood of the covenant wherewith he was sanctified an unholy thing, and hath done despite unto the Spirit of grace?30 For we know him that said, Vengeance belongeth unto me, I will recompense. And again, The Lord shall judge his people.31 It is a fearful thing to fall into the hands of the living God.32 But call to remembrance the former days, in which, after ye were enlightened, ye endured a great conflict of sufferings;33 partly, being made a gazingstock both by reproaches and afflictions; and partly, becoming partakers with them that were so used.34 For ye both had compassion on them that were in bonds, and took joyfully the spoiling of you possessions, knowing that ye have for yourselves a better possession and an abiding one.35 Cast not away therefore your boldness, which hath great recompense of reward.36 For ye have need of patience, that, having done the will of God, ye may receive the promise.

37 For yet a very little while, He that cometh shall come, and shall not tarry.

38 But my righteous one shall live by faith: And if he shrink back, my soul hath no pleasure in him.

39 But we are not of them that shrink back unto perdition; but of them that have faith unto the saving of the soul.